THE PSALMS IN HAUSA


Zabura ta 1

Albarka ga wanda bai shiga * shawarar miyagu ba,

    bai tsaya a taron masu zunubi ba, * bai kuma zauna a gun masu yin ba’a ba.

Sai dai yana jin da]in karanta shari’ar Yahweh, * yana ta nazarinta dare da rana.


    Yana kama da itacen * da ke a gefen }orama,

    yakan ba da ‘ya’ya a kan kari, * ganyayensa ba sa yin yaushi, * yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

Miyagu ba haka suke ba, * su kamar yayi suke * wanda iska take kwashewa.

    Mai sama kuwa ba zai tallafa ba * miyagu a wurin hukunci * ko kuwa masu zunubi wurin adilai.

Sai dai Yahweh yana lura da taron adalai, * amma taron miyagu zai hallaka.

Zabura ta 2

Don me al’ummai suke tayarwa, * suna }irga maya}ansu?

    Don me sarakunan duniya suke yin tawaye, * masu mulkinsu suna gama kai

         na gâba da Yahweh, * da shafaffen sarkinsa?

    Suna cewa “Bari mu kwance igiyarsu, * mu fice daga }ar}ashinsu.”

         Shi wanda ke zaune a sama yana dariya, * yana mai da su abin dariya.

         Sannan yana korar manyansu da hushinsa, * da hasalarsa kuma yana razana su.

              Ni ma an na]a ni sarkinsa * a bisa Sihiyona, dutsensa tsattarka.

                   Bari in yi shelar umurnin * Ubangiji Yahweh, * ya ce da ni:

              “Kai ]ana ne, * a yau ne na haife ka.

         Ka ro}e ni, zan ba ka * al’ummai ka gada, * har bangon duniya za ka mallaka.

         Za ka yi kiwonsu da sandan }arfe, * ka farfashe su kamar tukunyar magini.”

    Yanzu, ku sarakuna, ku yi hankali, * ku garga]u, ku mahukunta!

         Ku bauta wa Yahweh da tsoro, * ku yi rawar jiki, ku da aka }addarawa zuwa kabari,

    don kada ya yi hushi, taronku kuwa ya hallaka, * gama yakan yi hushi da sauri.

Albarka ga duk * masu neman mafaka a wurinsa.

Zabura ta 3

Yahweh, magabtana sun }aru }warai! * Da yawa ne masu tasam mani!

    Barkatai ne su ke hararrata, suna cewa: * “Ai ba wani taimakon da Allah zai yi masa.”

    Amma kai, Yahweh, maigidana ne iyakar raina, * Ma]aukakina ne kuma, mai tallafata.

         In na kai kukana gaban Yahweh, * yakan amsa mani daga tsattsarkan dutsensa.

              In na kwanta in yi barci, * nakan farka, domin Yahweh yana kiyaye ni.

         Ya {a}}arfa, bana jin tsoron kiban magabtana, * da ke kewaye ta kowane gefe, ya Mai Sama.

    Ka yin}uro mana, Yahweh, * ka ku~utad da ni, ya Allahna!

    Kai da kanka * ka bugi bakin magabtana, * ka kakkarya ha}oran miyagu.

Ya Yahweh, kai mai nasara ne! * Albarkarka ga jama’arka.

Zabura ta 4

Da na yi kira, ka amsa mani, * ya Allah mai nasarata.

Daga matsatsi ka bu]e mani hanya, * ka ji tausayina, ka saurari addu’ata.

    Ya ku ’yan adan, yaushe ne * za ku dena zagin Ma]aukaki?

        kun bauta ma abubuwan banza, * kuna shawara da allolin }arya?

    Amma dai ku san cewa * Yahweh zai yi abubuwan mamaki don bawansa, * Yahweh zai saurara sa’ad da na kira shi.

        Ku ji tsoro, kada ku ]au zunubi, * ku binciki zukatanku, * ku kwanta, ku yi kuka.

        Ku yanka dabbobin da suka hallata hadaya, * ku kuma dogara ga Yahweh.

    Mutane da yawa suke cewa, * “Wa zai kawo mana ruwan sama?”

        Amma hasken fuskarka, * ya guje mana, Yahweh.

    Sai dai ka sanya farinciki a cikin zuciyata, * yanzu sai hatsinsu da abinshan inabinsu su }aru.

Da kwanciyar rai a gaban fuskarsa * zan kwanta in yi barci,

domin kai ka]ai ne, Yahweh, * kake zaunad da ni a cikin aminci.

Zabura ta 5

Ka kasa kunne ga kalmomina, Yahweh, * ka ji maganata.

    Ka saurari sautin kukana, * ya Sarkina, Allahna, * domin gare ka nake addu’a.

    Da sassafe ka ji muryata, * da sassafe nake yin }ara, * in kuma yi dakonka.

         Allolin banza ne ke jin da]in mugunta, * mugun mutun ma ba zai zo gunka ba.

         Masu fariya * kada su tsaya a gaban idanunka.

              Na }i dukkan masu mummunan aiki, * sai ka hallaka ma}aryata.

              Mai gunki da mai tsafi, * duk Yahweh yana }insu.

                   Amma ni, da yalwar }aunarka, * zan shiga gidanka.

                       Zan yi sujada zuwa ga tsattsarkan Haikalinka * tare da masu tsoronka.

                   Ka yi mani jagora zuwa aljanna, * nesa daga magabtana; * ka sa hanyarka ta yi mani saukin bi.

              Ba abin da za a gaskanta daga bakinsu, * cikinsu kududdufi ne da ba zai cika ba.

              Ma}ogwaronsu na ha]iya kamar bu]a]]en kabari, * suna kisa da halshensu.

         Ka hallaka su, ya Allah, * bari shirye-shiryensu su tadiye su.

         Saboda ]umbun laifuffukansu * ka jefad da su * domin sun yi maka tawaye.

    Duk wa]anda suka fake gare ka su yi farinciki, * kullun su yi ta raira wa}ar murna.

    Kakan kiyaye masu }aunar sunanka,* domin su yi matu}ar murna da kai.

Gama kana yi wa mai gaskiya albarka, * Yahweh, * kamar garkuwa, soyayyarka ke kewaye shi.

Zabura ta 6

Yahweh, kada ka tsawata mani da hushinka, * kada kuma ka hore ni da zafin ranka.

    Ka ji tausayina, Yahweh, * domin na bushe.

    Ka warkad da ni, Yahweh, * domin }asusuwana sun rafke.

         Raina ya wahala }warai, * amma kai, Yahweh, yaushe za ka dube ni?

         Ka dawo, Yahweh, ka ku~utad da raina, * ka cece ni yadda ya dace da }aunarka.

              Gama ba mai tunawa da kai a Mulkin Mutuwa. * Can a Lahira ma wa zai yi yabonka?

              Na gaji da kuka, * kowane dare sai na ji}a gadona, * ina cika tabarmana da hawaye.

         Idanuna sun dishe da ba}inciki, * zuciyata ta karaya saboda ba}inciki.

    Ku rabu da ni, masu mugun aiki, * domin Yahweh ya ji sautin kukana.

    Yahweh yâ ji ro}ona, * Yahweh ya kar~i addu’ata.

Su kunyata, su ]auki rawar jiki * dukan magabtana * su juya, su ji kunya a Mahallaka.

Zabura ta 7

Yahweh, Allahna, gare ka nake dogara, * ka cece ni daga dukan masu korata.

Ka ku~utad da ni, kada wannan ya kacancana ni * kamar zaki * yana }arya wuyana, ba kuma mai ceto.

    Yahweh, Allahna, in na yi cin mutunci, * in hannuna na da laifi,

    in na ci amanar abokina, * ko na dame shi da tsegumi,

         to, magabcina ya bi ni, ya kama ni, * ya tattake kayan cikina a }asa, * ya jefad da antata a ca~i.

         Ka tashi, Yahweh, da hushinka, * ka tsai da wulakancin magabtana.

         Ka falka, ya Allahna, * ka umurci

              Ka tattaro dukan kabilan kewaye da kai, * ka shugabance su, ya Ma] aukaki, * Yahweh, ka yi wa dukan mutane shari’a.

              Ka hukunta ni gwargwadon aikina na gaskiya * da kirkina, ya Ma]aukaki.

                   Ka rama ta’addancin ’yan ta’adda, * ka kuma kâre mai gaskiya.

                   Mai binciken zukata da hankula, * shi ne Allah mai gaskiya.

              Maigidana Allah Ma]akukaki ne, * yakan ceci masu zuciya tagari.

              Allah alkali ne mai gaskiya, * yana tsai da zalunci a kullun.

         Bari Mai Nasara ya sake * wasa takobinsa, * ya ]ana bakansa cikin shiri.

         Bari ya shirya makamansa masu kisa,* ya kunna kibansa masu wuta.

    Mugu yakan ]auki cuta, * yakan yi ciki da fitina, * yakan haifi ru]u.

    Ramin da ya ha}a ya tadiye shi, * ya fa]a ramin da ya tona.

    Muguntarsa ta koma kansa, * rikicinsa ya sauka }o}wan kansa.

Na gode wa Yahweh yadda ya kamata, * ina wa}ar yabon Yahweh Ma]aukaki.

Zabura ta 8

Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ]aukaka ne * a dukan duniya.

    Zan yi wa martabarka sujada, * wadda take bisa sama, * da bakin jarirai masu shan mama.

    Ka gina mafaka don gidanka, * bayan ka bebanta magabtanka * da ma}iyanka da masu ramuwa.

         Sa’ad da na dubi sammai, * aikin yatsunka,

         da wata da taurari * wa]anda ka halitta:

             Menene mutun, har da za ka tuna da shi, * ko ]an adan, har da za ka kula da shi?

         Duk da haka, ka yi shi ya gaza alloli ka]an, * da daraja da girma ka na]a shi.

         Ka mai da shi sarkin ayyukan hannuwanka, * ka sanya kome a }al}ashin sawayensa:

    tumaki tare da shanu, * har da namomin jeji,

    da tsuntsaye da kifayen teku, * masu yawo a hanyoyin ruwan tekuna.

Yahweh, Ubangijinmu, * sunanka mai ]aukaka ne * a dukan duniya.

Zabura ta 9-10

Zan yabe ka, Yahweh, da dukan zuciyata, * zan bayyana dukan ayyukanka masu banmamaki.

Zan yi murna, in yi farinciki da kai, * zan raira wa}ar da sunanka, Ma]aukaki.

    Sa’ad da magabtana suke ja da baya, * suna tuntu~e, su hallaka saboda hushinka.

    Ka yi na’am da hakkina da sha’anina, * ka zauna a kan gadon sarauta, ya Alkalin gaskiya.

         Ka tsawata wa al’ummai, ka hallaka miyagu, * ka shafe sunansu har abada abadin.

         Magabtana su isa }arshensu, * su zama kufai har abada.

         Ka tuge allolinsu masu tsare su, * a dena tunawa da su.

    Ga shi, tun fil’azal Yahweh ya yi mulki, * ya kafa kursiyinsa don yin shari’a.

    Shi ne yake mulkin duniya da gaskiya, * yana yi wa mutane shari’a da adalci.

         Yahweh mafaka ne ga wa]anda ake zalunta, * matsera kuma a lokacin }unci.

         Bari wa]anda suke son sunanka su amince da kai, * domin ba ka }yale masu nemanka, Yahweh.

              Ku yi wa}o}in yabon Yahweh, Sarkin Sihiyona, * ku gaya wa al’ummai aiyyukansa.

              Gama yakan lura da masu kuka, * yakan tuna da nishinsu, * baya mantawa da }arar masu shan wuya.

                  Ka ji tausayina, Yahweh, * ka ga wahalata.

                  Ka janye ni daga Ma}iyina, * da }ofofin Mutuwa,

                  don in bayyana yabonka sosai * daga }ofofin ’Ya Sihiyona,

                  in yi farinciki * da nasararka.

              Bari al’ummai su dulmuya cikin ramin da suka yi, * da tarkon da suka ]ana ya kama }afafunsu.

              Bari Yahweh ya sanu ta hukuncin da yake zartaswa, * amma bari a kama mugu ta aikin hannuwansa.

          Miyagu su koma Shawol, * su hallaka, su al’umman da suka manta da Allah.

          Gama ba kullun ne za a manta da mabukata ba, * sazuciyar zaluntattu ma ba za ta dannu ba har abada.

          Ka tashi, Yahweh, kada mutane su yi kirari, * a yi wa al’ummai shari’a a gabanka.

          Yahweh, ka danne bakinsu, * ka sa al’ummai su san su mutane ne kawai.

10           Yahweh, don me kake tsaye can nesa, * kana ~oyewa a lokacin wahala?

              Cikin mugu yana dafa wulakanci, * da aniya yake aikata dabarun da ya }u}}ulla.

              Mugu yana fahariya da marmarinsa, * mai }wacewa ma yana bauta wa kwa]ayinsa.

                   Mugu yakan rena Yahweh, cewa: * “Mai Sama ba zai aikata hushinsa ba.

                   Allah ba zai jirkita dabarunsa ba, * wadatata za ta jure har abada.”

                   Ma]aukaki, hukuntanka suna nesa da shi, * daga birnin zuciyarsa yana firjinsu da ba’a.

                   Yana cewa da kansa, “Ba zan yi tuntu~e ba, * ina da madauwamin farinciki ba wahala.

              Bakinsa cike yake da zagi, zamba da zalunci, * halshensa yana ri}on wulakanci da mugunta.

              Yakan yi kwanton ~auna a }auyuka, * a ma~oya yakan kashe marasa aibu, * idanunsa na hararar kâsasse.

          Yakan yi san]a kamar zaki a kogonnsa, * yakan yi san]a don ya kama gajiyayye, * yakan kama shi, ya tafi da shi.

          A tarkonsa zaluntacce ke fâ]uwa, * marasa katari kuma na fâ]awa raminsa.

          Yana cewa da kansa, “Allah ya mance, * ya rufe idonsa, * baya dubawa har abada.”

    Ka tashi, Yahweh Allah, ka ]aga hannunka, * kada ka manta da masu shan wahala.

    Har abada ne mugu zai rena Allah? * yana cewa da kansa, “Ba zai yi hisabi ba.”

         Ka dubi bakincikin da kanka, * ka dubi ~acin ran, * gama hannunka ne ke bayas da su.

         A gare ka gajiyayyen maraya ke dan}a kansa, * ka zama mataimakinsa mana!

    Ka karya dantsen mugu, * ka biya shi da muguntarsa. * Ba ka ganin }etarsa?

    Yahweh madauwamin sarki ne, * bari al’ummai su hallaka daga }asarsa.

Yahweh, ka saurari kukan matalauta, * ka mai da hankali, ka kasa kunne.

In ka kâre maraya da zaluntacce, * masu girman kai ba za su ri}a razana mutane daga duniya ba.

Zabura ta 11

Na sami mafaka wurin Yahweh. * Don me kuke san]ar raina? * kuna farautata kamar tsuntsu?

    Ga yadda miyagu suke jan baka, * suna ]ana kibansu,

    don su harbi * masu gaskiya a ~uye.

         Lokacin da ake ture harsashen, * me Mai-Gaskiya yake yi?

              Yahweh yana da mazauni a Haikalin, * kursiyin Yahweh a sama yake.

                   Idanunsa suna kallo, * suna binciken * duk ’yan adan.

              Yahweh mai gaskiya * yana auna miyagu.

         Duk wanda yake son zalunci * yana }in ransa.

    Bari Yahweh ya zubo wa miyagu * garwashin wuta da kibiritu.

    Bari iska mai }una * ta zama rabonsu.

Yahweh mai gaskiya ne * yana son ayyukan gaskiya. * Fuska da fuska zamu kalli Mai-Kirki.

Zabura ta 12

Ka yi taimako, Yahweh, * domin masu ibada sun }are.

Amintattun mutane sun kasa * a cikin ’yan adan.

    Kowa na zancen }arya, * da ma}wabcinsa.

    Da baki mai lahani * da zuciya biyu suke magana.

         Bari Yahweh ya yanka * duk baki mai lahani, * da duk halshe mai mur]a gaskiya,

         wa]anda suke fariya cewa, * “Halshenmu shi ne ikonmu.

         Makamanmu le~unanmu ne, * wa zai mallake mu?”

         “Saboda ajiyar zucin gajiyayyu * da nishin masu bukata,

         yanzu zan tashi,” * in ji Yahweh.

         “Zan ba da taimako * ga wanda ya ke bukatarsa.”

    Alkawalan Yahweh * alkawalai ne masu gaskiya,

    azurfa ne da aka tace a matoya, * aka tsabtace ta daga laka sau bakwai.

Yahweh, kai kâ tsare mu, * kâ kiyaye mu tun fil’azal, ya Madauwami.

Ko’ina miyagu suna rangadi, * suna tona ramuka don ’yan adan.

Zabura ta 13

Har zuwa yaushe za ka mance da ni, Yahweh? Har abada? * Har zuwa yaushe za ka kau da fuskarka daga wajena?

Har zuwa yaushe zan yi shakka a raina, * ina ba}inciki a raina? * Har zuwa yaushe ma}iyina zai yi mani dariya?

    Ka dube ni, ka amsa mani, * Yahweh Allahna.

         Ka bu]e mani idona, * ka kau da barcin mutuwa daga wajena.

    Kada magabcina ya ce, * “Na rinjaye shi,” * kada ma}iyina ya yi farinciki saboda fa]uwata.

Amma ina dogara ga rahamarka, * bari zuciyata ta yi murna don ka cece ni.

Zan raira wa}a ga Yahweh, * gama Ma]aukaki ya kyautata mani.

Zabura ta 14

A tunanin wawayesuna cewa, * “Allah baya nan.”

Su ~atattu ne, suna aikata al’amuran }yama, * ba wani mai yin abu mai kyau.

    Daga sama Yahweh yana dubo * ’yan adan duka,

    don ya ga ko akwai masu fahimi, * masu neman Allah.

         Amma dukansu masu taurin kai ne, * sun }azanta gaba ]aya.

         Ba mai yin kyakkyawan aiki, * babu ko ]aya.

         Masu aikin mugunta ba su sani ba * cewa masu washe jama’arsa

         suna satar hatsin Yahweh, * da ba su yi noma ba?

    Ga yadda suka yi }ungiya, * amma Allah ne a cikin jama’ar adilai.

    Majalisar gajiyayyu ta kunyata miyagu, * gama Yahweh shi ne mafakarsu.

Daga Sihiyona sai ceton Isra’ila ya fito! * Sa’ad da Yahweh ya sake arzuta jama’arsa,

bari ’ya’yan Yakubu su yi farinciki, * ’ya’yan Isra’ila su yi murna.

Zabura ta 15

Yahweh, wa zai iya ba}unci a alfarwarka? * Wa zai iya zama a kan tsarttsarkan dutsenka?

    Sai wanda ke bin hanya mara aibu, * yana aikata gaskiya, * yana fa]ar kaskiya daga zuciyarsa,

         Wanda baya kus}ure da halshensa, * baya cutar makwabcinsa, * baya baza jita-jita a kan abokansa.

              Yakan rena mai laifi, * amma yakan shirya liyafa don masu tsoron Yahweh.

         Ya rantse ba zai yi mugunta ba, * ba kuma zai canza ba.

    Baya bayas da rance da ruwa, * baya ma kar~ar toshi daga mayunwata.

Wanda yake yin wa]annan abubuwa * ba zai gaza ba.

Zabura ta 16

Ka kiyaye ni, ya Allah, * gama a gunka nike neman mafaka.

Na ce: “Yahweh, kai ne Ubangijina, * kai ne Nagartata, * ba wanda ya fi ka a sama.

    Game da tsarkakan iskokin gargajiya, * jarruman da na ji da]insu dâ,

         baru naku]arsu ta }aru, * su da]e cikin tsanani.

    Hannuwana ba zasu zuba masu hadaya ba, * bakina ma ba zai ambaci sunayensu ba.

         Yahweh, kâ ba ni rabona na abin sha mai da]i, * kâ yi kuri’ar }asata.

         An auna mani kyakkyawar }asa, * Ma]aukaki ya za~i ganduna.

    Zan yabi Yahweh mai ba ni shawara, * da dare yana garga]ina a zuci.

         Na za~i Yahweh shugabana har abada, * daga hannun damansa ba zan girgiza ba.

    Don haka zuciyata ke farinciki, antata ma ke murna, * jikina na zaune a cikin aminci.

Gama ba za ka sa ni a Mahallaka ba, * ba za ka bar mai bauta maka ya ga Ramin ba.

Za ka nuna mani hanyar rai, * kana cika ni da farinciki a gabanka, * da murna a hannun damanka har abada.

Zabura ta 17

Yahweh, ka ji ro}ona don hakkina, * ka saurari kukana.

    Ka kasa kunne ga addu’ata, * ka hallakad da bakunan yau]ara.

    Bari adalcina ya yi haske a gabanka, * idanunka su dubi gaskiyata.

         Ka gwada zuciyata, * ka bincike ni da dare, * ka jarrabce ni da wuta:

         Ba za ka sami tsafi a wurina ba, * ban yi batanci game da aikin hannuwanka ba.

         Ga kalmomin bakinka * na ri}e amana.

         {afafuna sun bi ta hanya mai wuya * ba su ratse daga hanyoyinka ba.

    Ina kiranka, * ka amsa mani, ya Allah.

    Ka kasa kunne gare ni, * ka ji maganata.

         Ka yi karo da masu sa~onka, ya Maceci, * rufe bakunan magabtanka.

              Ka adana ni kamar }wayar ido, * ka ~oye ni a inuwar fukafukanka

         daga mugun da ke son yayyaga ni * daga magabtana da ke kewaye da ni.

    Sun na]i gara, * suna magana da izgilanci sosai.

    {afafuna suna kyarma, * da suka kewaye ni.

         Sun sa ido su fya]a ni * {asar Hallaka,

         kamar zaki mai ha]amar kisan abincinsa, * kamar kuyakuyan zaki masu ~uya a wurin fako.

         Ka tashi, Yahweh, ka tsai da hushinsu, * ka kâ da su, * ka cece ni daga miyagun da ke ya}inka.

         Ka kashe su da hannunka, Yahweh, * ka hallaka su daga duniya, * ka shafe su daga masu rai.

    Amma darajantattun mutanenka, * ka cika cikinsu da gara.

    ’Ya’yansu su sami duk abin da suke so, * su bar wadatarsu ga jikokinsu.

A ranar shari’a zan ga fuskarka. * a ranar tashin kiyama zan gamsu da zatinka.

Zabura ta 18

Ina }aunarka, Yahweh, }arfina. * Yahweh dutsena ne da matserata. * Allahna mafakata ne,

    Tuduna ne kuma wurin da ni ke gudu, * da garkuwata da makamin ceto, * hasumiyata mai cancantar yabo.

Na yi kira ga Yahweh, * ya cece ni daga magabtana.

    Ra}uman ruwan Mutuwa sun kewaye ni, * rafukan Hallaka sun gangara ta kaina.

    Igiyoyin Mahallaka sun ]aure ni, * tarkunan Mutuwa sun fuskance ni.

A shan wahalata na yi kuka ga Yahweh, * ga Allahna na yi kira don taimako.

Daga cikin Haikalinsa ya ji muryata, * kukana ya kai har kunnuwansa.

    {ar}ashin {asa ya yi tanga]i, * gindin duwatsu ma ya motsa, * ya yi makyarkyata da Yahweh ya fusata.

    Haya}i ya fito daga hancinsa, * wutar gobara daga bakinsa, * har da garwashin wuta daga wajensa.

         Ya bu]e sama, ya sauko, * girgijen hadari alfarwarsa ya ke.

         Ya hau Kerub, ya tashi sama, * ya yi tafiya da fikafikai bu]e.

              Tantinsa ya duhunta, * alfarwarsa da gajimaren ruwa.

              Saboda haskensa gizagizai sun dâre a gabansa, * duk da kan}ara da harsunan wuta.

                   Yahweh ya yi tsawa daga sama, * Mafi ]aukaka ya furta maganarsa.

                   Ya }era kibansa, ya warwatsa su, * ya yawaita wal}iyoyinsa, ya fatattake su.

              {al}ashin teku ya bayyana, * harsasan duniya sun tonu,

              saboda tsautawarka, Yahweh, * saboda rurin hancinka.

         Ya mi}o hannu daga sama ya ]auke ni, * ya tsamo ni daga zurfafan ruwaye.

         Ya ku~utar da ni daga }a}}arfan Magabcina, * daga Ma}iyina da ya fi ni }arfi.

    Ya bi da ni ranar mutuwata, * Yahweh ya zama sandata.

    Ya fisshe ni daga {asar Hallaka, * ya cece ni, domin ya ji da]ina.

         Yahweh ya biya ni saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba ya saka mani da alheri.

              Gama na kiyaye hanyoyin Yahweh, * ba ni da laifi, ya Allahna.

                   Gama dukan hukuncinsa na gabana, * ban kuwa yas da dokokinsa ba.

              Kullun ina da sahihanci a gare shi, * na yi la’akari kada in yi masa laifi.

         Don haka ya saka mani saboda gaskiyata, * don hannuwana ba su yi aibu ba a gaban idanunsa.

              Ga mai aminci kai mai aminci ne, * ga mai sahihanci kai mai sahihanci ne.

              Ga mai gaskiya kai mai gaskiya ne, * amma ga mai wayo kai ne mafi wayo.

                   Ai, kai ne Mai iko duka, * kana ceton gajiyayyu, * amma kakan tan}waso masu alfarma.

                        Kana yi mani haske, * fitilata Yahweh ne, * Allahna yana haskaka dufuna.

                   Ta wurinka ina da gwanintar sere, * da ikon Allahna na iya tsallace duk wani shinge.

              Sarautar Allah kammalalliya ce, * ana tabbatad da umurninsa.

              Shi shugaba ne * na duk masu dogara gare shi.

         Gama wanene Allah in ba Yahweh ba? * Wanene kuma dutse in ban da Allahnmu?

              Shi Allah ne da ke yi mani ]amara da }ar}o, * da kuma Mai Bayarwa wanda sarautarsa take cikakka.

              Ya mai da }afafuna kamar na barewa, * ya sa in tsaya a kan tudunsa.

         Ya hori hannuwana don ya}i, * ya saukar mani da baka mai banmamaki.

    Kâ ba ni garkuwarka ta nasara, * da hannunka na dama kâ ri}e ni, * da ho~~asanka na zama mai girma.

    Kâ ba ni dogayen }afafuna masu sauri, * idanun }afata ma ba su goce ba.

         Na bi magabtana har na kama su, * ban juya baya ba sai da aka gama da su.

         Na kâ da su, ba su iya tashi ba, * sun fâ]i a }afafuna.

         Kâ yi mani ]amara da }arfi don ya}i, * kâ kâ da masu ya}i da ni a }ar}ashina.

         Kâ ba ni wuyan magabtana, * na hallaka ma}iyana.

    Sun yi kuka, amma Macecin baya nan, * sun kira Yahweh Ma]aukaki, * amma bai amsa masu ba.

    Na marmashe su sun zama kamar }urar titi, * kamar ta~on kwararo na tattake su.

Kâ ku~utad da ni daga kiban mutane, * kâ tsare ni daga dafin sauran al’ummai.

Ba}uwar al’umma za ta zama baiwata, * da sun ji ni, nan da nan sai su yi mani biyayya, * ba}i sai sun sunkuya don tsoro.

Ba}i sukan yi rawar jiki, * zukatansu sukan karaya.

    Ran Yahweh ya da]e! * Dutsena a yabe shi! * [aukaka ga Allah mai ba ni nasara!

    Shi Allah ne wanda ya ba ni nasara, * ya sarayar da al’ummai gare ni.

    Ya ku~utad da ni daga Magabcina, * ya ]aukaka ni a kan masu yin ya}i da ni, * ya cece ni daga masu cin mutuncina.

Ya Ma]aukakin Zati, zan yabe ka a cikin al-ummai, * Yahweh, in kuma yi wa}ar yabon sunanka.

Ya mai da sarkinsa sananne don cin nasara da ya yi, * ya nuna }auna ga shafaffen sarkinsa, * ga Dauda da irinsa har abada.

Zabura ta 19

Sammai suna shaida ]aukakar Allah, * aikin hannuwansa ma, sararin sama ke bayyana shi.

    Kowace rana tana furta magana ga rana ta biye, * kowane dare yana sanad da dare na biye.

    Ba wata magana, ba wasu kalmomi, * ba a jin muryarsu.

    A duniya duka kiransu ke bazuwa, * maganarsu kuwa har zuwa bangon duniya.

         Ya kafa wa rana alfarwa, * kamar ango tana ta}ama daga ma~oyarta.

         Tana murna kamar maya}i, * don ta ruga a kan hanyarta.

         Takan fara daga farkon sama, * ta koma gare shi, * ba ta kuskuren ]akinta.

              Shari’ar Yahweh kammalalliya ce, * tana sanyaya zuciyata.

              Shari’ar Yahweh tabbatacciya ce, * tana sa hikima a tunanina.

                   Ka’idodin Yahweh madaidaita ne, * suna faranta zuciyata.

                   Umurnin Yahweh mai haske ne, * yana haskaka idanuna.

                   Dokar Yahweh mai tsabta ce, * tana jurewa har abada.

                   Hukuntan Yahweh gaskiya ne, * dukansu daidai ne.

              Su aka fi so a kan zinariya, * komi yawanta.

              Sun fi zuma za}i, * i, fiye da sa}a cike da ruwan zuma.

         Suna haskaka ni bawanka, * wajen kiyaye su da lada mai girma.

         Wa zai iya gano kurakurai? * Ka hana ni bau]ewa.

    Ka kuma kare ni daga allolin }arya, * kada su mallake ni.

    A sa’an nan ne zan zama kamili, * in kuma ku~uta daga babban zunubi.

Sai bakina ya furta abin da ya gamshe ka, * zuciyata ma ta bi nufinka, * Yahweh, Dutsena da Mai Fansata!

Zabura ta 20

Yahweh ya ba ka nasara a ranar wahala! * Sunan Allah na Yakubu ya zama garunka.

    Ya aiko maka da taimako daga Haikalinsa, * ya kawo maka gudunmuwa daga Sihiyona.

         Ya tuna da dukan baye-bayenka, * ya yi na’am da hadayunka na }onawa.

    Ya biya bukatar zuciyarka, * ya cika dukan shirye-shiryenka.

         Sannan za mu yi sowa ta farinciki saboda ka ci nasara, * da sunan Allahnmu kuma za mu ka]a tutoci. * Bari Yahweh ya cika dukan ro}e-ro}enka!

              Yanzu dai na sani * Yahweh yakan ba shafaffen sarkinsa nasara.

         Yakan ba shi nasara daga tsattsarkar samaniyarsa, * a mafakarsa yakan ba da nasara da hannunsa na dama.

    Wa]ansu suna da karusai, * wa]ansu suna da dawaki,

         amma mu da sunan Yahweh * Allahnmu ne muke da }arfi.

    Suna sunkuyawa, suna fa]i, * amma mu, muna tashi tsaye kyam.

Yahweh yâ ba sarkin nasara, * yâ ba shi nasara da muka ro}a.

Zabura ta 21

Yahweh, da nasararka sarki yake murna, * da agajinka yake farinciki.

    Kâ biya masa burin zuciyarsa, * ba ka }yale ro}on da ya yi ba.

    Kâ zo gare shi da albarka mai kyau, * kâ sanya kambin zinariya a kansa.

         Ya ro}e ka madauwamin rai, ka kuma ba shi, * kwanaki ba iyaka, har abada abadin.

         Martabarsa babba ce don nasarar da ka ba shi, * kâ sa ya yi suna da kwarjini.

              Albarkarka tana a kansa har abada, * za ka faranta masa rai da ganin fuskarka.

              Sarkin yana dogara ga Yahweh, * ba kuma zai kawu daga }aunar Madaukaki ba.

              Hannunka na hagu ya kama dukan magabtanka, * hannunka na dama ya kama ma}iyanka.

              Yahweh, kâ sa su a cikin tanderu mai wuta * a lokacin hushinka.

         Da hushinsa yâ cinye su da wuta, * ya ha]iye su.

         Kâ hallaka ’ya’yansu daga duniya, * da zuriyarsu daga cikin ’yan adan.

    Gama sun shirya tayarwa game da kai, * sun }ulla mugunyar dabara, * amma ba su iya yinta ba.

    Kâ sa su durkusa, * inda kake ]ana masu bakanka.

Yahweh, ka yi bikin nasararka! * Za mu raira wa}a ta yabon ikonka.

Zabura ta 22

Ya Allahna, ya Allahna, * don me ka yashe ni?

kana korar ro}ona, * da sautin kururuwata.

    Ya Allahna, ina kira da rana, * amma ba ka amsa ba,

         da dare kuma, * ban sami ta’aziya ba.

    Amma kana zaune a kan tsattsarkan gado, * [aukakar Isra’ila.

Gare ka ne kakanninmu suka dogara, * sun dogara, kai ma ka ku~utad da su.

Gare ka ne suka yi kira, sun kuwa ku~uta, * gare ka ne suka yi kira, ba su kuwa kunyata ba.

    Amma ni tsutsa ne, ba mutun ba, * mafi renanne wurin mutane, * abin ba’a ga kowa.

         Duk wa]anda ke ganina suna maishe ni abin dariya, * suna tsaki, suna ka]a kai, suna cewa:

              “Ya bi Yahweh, bari ya ku~utad da shi; * sai ya cece shi in ya so shi.”

              Amma kai ne ka fito da ni daga mahaifa, * ka kwantad da raina a maman mahaifiyata.

         Kai ne ka ciyad da ni daga haifuwata, * tun ina cikin uwata kai Allahna ne.

    Kada ka yi nesa da ni, * gama masu tsananta sun yi kusa, * ba ma wani mataimaki.

         Bajimai masu yawa suna kewaye ni, * }arfafan bajimai daga Bashan suna sa ni tsaka.

         Suna bu]e mani bakinsu, * kamar zakoki masu kâwa masu hauka.

              An zub da ni kamar ruwa, * }asusuwana duka sun guggulle.

              Zuciyata ta narke kamar danko * tana ]igowa daga }irjina.

                   {arfina ya bushe kamar sakaina, * halshena ya li}e wa mu}amu}aina, *

                   an tura ni cikin ca~in Mutuwa.

                       Gama karnuka sun kewaye ni, * }ungiyar miyagu ta sa ni a tsaka,

                       sun cinye naman hannuwana da }afafuna. * Na iya }irga dukan }asusuwana.

                   Ga yadda suke kallona, suke zura mani ido, *

                   suna rarraba tufafina a junansu, * rigata kuwa suna }uri’a a kanta.

              Amma kai, Yahweh, kada ka yi nisa, * ya Rundunata, ka gaggauta ka taimake ni!

              Ka ceci wűyana daga takobi, * da fuskata daga ruwan gatari.

         Ka ku~utad da ni daga bakin zaki, * ka sa in rinjayi }ahonin ~akwane,

         don in yi shelar sunanka ga ’yan’uwana, * in yabe ka a tsakiyar jama’a.

    Masu tsoron Yahweh, ku yaba masa, * ku jikokin Yakubu, ku girmama shi, * ku tsorace shi, dukan jikokin Isra’ila.

         Gama bai rena ba, * ko }in wa}ar gajiyayye.

              Bai kuma kau da fuskarsa daga gareshi ba, * amma da ya yi kuka, yâ ji shi.

              Zan raira yabonka sau ]ari * wurin babbar jama’a * zan biya alkwaran da na rantse, ya Shugaba.

         Masu tsoronsa za su ci abinci, * matalauta za su }oshi.

    Masu neman Yahweh za su yaba masa, * zukatanku su da]e har abada!

Dukan iyakokin duniya za su tuna, * su komo wa Yahweh.

Dukan kabilan al’ummai ma * za su yi maka sujada.

    Gama Yahweh sarki ne, * mai mulki kuma na al’ummai.

         Lalle, dukan masu yin barci a Lahira * za su yi masa sujada.

    Duk wa]anda suka sauka a Ca~in * za su dur}usa masa, * gama Mai nasara yakan mayar da rai.

Bari jikokina su bauta masa, * su ba da labarinsa har abada.

Su soma ba da shaidar nagartarsa * ga mutanen da za a haifa, cewa ya yi abin.

Zabura ta 23

Yahweh makiyayina ne, * ba zan yi rashi ba, * zai sa ni in kwanta wurin ]anyar ciyawa.

Zai bi da ni wurin ruwan de ke kwance, * don ya farfa]o mani da rai.

Zai bishe ni wuri mai yawan ciyawa, * kamar yadda ya dace da sunansa.

    Ko da yake ina tafiya * ta tsakar duhu ba}i} }irin,

    ba zan ji tsoron hatsari ba, * domin kana tare da ni.

         Sandarka da kerenka * ba shakka za su yi mani jagora.

    Kakan shirya mani abinci * a gaban magabtana.

    Kakan shafa mani mai a ka, * }o}ona ya cika har yana zuba.

Ashe, alheri da rahama za su raka ni * duk kwanakin raina.

Zan kuma zauna a gidan Yahweh * kwanaki marasa iyaka.

Zabura ta 24

{asa da duk wadatarta na Yahweh ne, * da duniya da mazaunanta.

Gama ya gina ta a bisa tekunan da ke }ar}ashin }asa, * ya kafa harsashinta bisa igiyar tekuna.

    Wa zai hau kan dutsen Yahweh? * Wa zai tsaya a tsattsarkan wurinsa?

    Sai wanda hannunsa da zuciyarsa ba su da aibu, * wanda bai juya nufinsa ga gunki ba, * ko kuma ya rantse a kan allahn }arya.

         Shi ne zai kar~i albarka daga wurin Yahweh, * da nagarta daga Allahnsa maceci.

         Ku nemi Sarkin zamanai, * ku bi Wanda ya zauna tare da Isiyaku.

    Ku ]aga kanku, ya ku }ofofi, * ku ]agu, ku }ofofin Madauwami, * Sarkin ]aukaka na zuwa.

    Wanene Sarkin ]aukaka? * Yahweh ne mai }arfi mai iko, * Yahweh mai iko a ya}i.

Ku ]aga kanku, ya ku }ofofi, * ku ]agu, ku }ofofin Madauwami, * Sarkin ]aukaka na zuwa.

Wanene Sarkin ]aukaka? * Yahweh ne mai runduna, * shi ne Sarkin ]aukaka.

Zabura ta 25

A gare ka, Yahweh, * ni ke sa raina.

    Ya Allahna, a gare ka ni ke dogara, * kada in kunyata, * kada magabtana su yi murna a kaina.

    Duk wanda ya kira ka ba zai kunyata ba, * sai matsegunta marasa aminci su kunyata.

         Ka nuna mani hanyoyinka, Yahweh, * ka koya mani tafarkunka.

         Ka sa in bi ka da aminci, ka ma koya mani, * domin kai ne Allah mai cetona, * gare ka ni ke kira duk yini.

              Ka tuna, Yahweh, da rahamarka da alherinka, * yadda tun fil’azal suke.

              Zunubaina da kurakuraina na }uruciyata, * kada ka tuna da su!

              Amma ka tuna da ni bisa ga alherinka, * bisa ga }aunarka, Yahweh.

                   Yahweh mai nagarta da gaskiya ne, * Ma]aukakin Zati, ya kan koya wa masu zunubi hanyarsa.

                   Yakan bi da matalauta ta adalcinsa, * yakan koya masu hanyarsa.

                   Dukan hanyoyin Yahweh alheri ne da aminci * ga wa]anda suke kiyaye ka’idodin yarjejeniyarsa.

                       Albarkacin sunanka, Yahweh, * ka gafarta zunubina, * ko da yake babba ne.

                   Wane mutun ne ke tsoron Yahweh? * Shi ne wdanda zai koya wa hanyar da zai za~a.

                   Ransa zai zauna lafiya, * jikokinsa ma za su gaji }asar.

                   Zumuncin Yahweh ya ]auru da masu tsoronsa, * yana sanar masu da yarjejeniyarsa.

              Idanunna kullun ga Yahweh ne, * domin zai kau da }afafuna daga tarko.

              Ka dube ni, ka ji tausayina, * domin ina ka]aici a cikin matsatsi.

         Damuwa ta matsa wa zuciyata, * ka fid da ni daga ~acin raina.

         Ka dubi wahalata da azabata, * ka kawas da dukan zunubaina.

    Ka dubi yawan magabtana, * masu ha’inci da su ke }ina.

    Ka kiyaye raina, ka ku~utad da ni, * kada in kunyata, domin na nemi kâriya a wurinka.

    Ka sa nagarta da aminci su kiyaye ni, * domin na kire ka.

Ya Allah, ka ceci ’ya’yan Isra’ila * daga dukan wahalarsu.

Zabura ta 26

Ka hukunta ni, Yahweh, * gama na ri}a bin gaskiya.

Na dogara ga Yahweh, * ban girgiza ba.

    Ka bincike ni, Yahweh, ka auna ni, * ka gwada zuciyata da tunanina.

         Lalle, a kullun }aunarka tana cikin hankalina, * ina kuma bin ka da aminci.

              Ban zauna da masu bautar gumaki ba, * ban shiga gidan masu jahilci ba.

                   Na tsargi taron masu aikata mugunta, * ban ta~a zama da miyagu ba.

                       Na wanke hannuwana ba tare da aibu ba, * don in zagaya bagadinka, Yahweh,

                       don in ]aga muryar yabonka, * in fa]i dukan ayyukanka masu banmamaki.

                   Yahweh, ina }aunar zama a gidanka, * inda ]aukakarka take.

              Kada ka runtume ni da masu zunubi, * ko ha]a raina da matsafa.

         A hannunsu na hagu akwai gumaka, * hannunsu na dama cike ya ke da cin hanci.

    Ni kam, zan ri}a yin halin kirki, * ka fanshe ni, ka yi mani rahama.

{afata ta tsaya daram da masu gaskiya, * a cikin taronsu ne nike dur}usa wa Yahweh.

Zabura ta 27

Yahweh ne haskena da cetona, * to, wa zan ji tsoro?

Yahweh ne mafakar raina, * to, wa zai sa in firgita?

    Sa’ad da miyagu suke ya}ina * don su ci namana,

    ma}iyana da magabtana * suna tuntu~e, suna fâ]uwa.

         Ko da rundunar soja ta kewaye ni, * zuciyata ba za ta razana ba.

         Ko da maya}a sun taso mani, * zan yi taho mu gama da su.

              Abu guda na ro}a sau ]ari, * shi ne, Yahweh, ni ke nema:

              In zauna a gidan Yahweh, * dukan kwanakin raina,

              in ga kyan Yahweh, * in tashi kowace safiya a cikin Haikalinsa.

                   Zai darajanta ni a Zaurensa, * bayan Mugunyar Rana.

                       Zai ~oye ni a innuwar tantinsa, * a kan dutse mai tsayi.

                       Yanzu an ]aga kaina * bisa magabtana da ke kewaye da ni.

                   Zan yanka hadayun murna a tantinsa, * zan yi ki]a da wa}a ga Yahweh.

              Ka ji muryata, Yahweh, lokacin da na yi kira, * ka ji tausayina, ka amsa mani.

              “Zo mana,” in ji zuciyata, “ka nemi fuskarsa!” * Fuskarka zan nema, Yahweh.

              Kada ka juya mani baya, * kada ka watsar da bawanka cikin hushi, * ka zama mataimakina.

         Kada ka }i ni, * kada kuwa ka yashe ni, * ya Allah mai cetona.

         In ubana da uwata sun yashe ni, * Yahweh zai ri}e ni.

    Yahweh, ka nuna mani hanyarka, * ka yi mani jagora a hanyarka mara gargada * saboda magabtana.

    Kada ka bari magabtana su ha]iye ni, * don akwai shaidar zur a kaina, * suna magana da magudi.

Na amince da Mai Nasara, * don in ga kyan Yahweh * a }asar rai madauwami.

Ka jira Yahweh, ka }arfafa, * bari zuciyarka ta ]aure * ka jira Yahweh.

Zabura ta 28

A gare ka, Yahweh, nike kira, * Dutsena, * kada ka }i amsa mani.

In ba ka amsa mani ba, * zan yi kama da wa]anda suka gangara Ramin.

    Ka ji ro}ona don jin}ai, * da nike kira gare ka,

    da nike ]aga hannuwana * wajen tsarkakken dandalinka.

         Kada ka ha]a ni da miyagu, * ko masu aikata mugunta.

         wa]anda ke maganar salama da ma}wabtansu, * amma zukatansu cike suke da ha’inci.

              Ka yi masu abin da suka yi, * da sakayya gwargwadon ayyukan da suka yi.

              Ka biya su bisa ga aikin hannuwansu, * ka ba su abin da ya cancance su.

         Gama ba su kula * da abin da Yahweh ya yi ba, * ko kuwa aikin hannuwansa.

         Shi ma zai rushe su, * ba kuwa zai sake gina su ba.

    Yabo ga Yahweh! * domin ya ji ro}ona na jin}ai.

    Yahweh ne garkuwata mai }arfi, * zuciyata ta amince da shi.

Na koma }uruciyata, * zuciyata tana murna, * da wa}ata zan yabe shi.

Yahweh makara da mafakarmu, * shi Macecin shafaffen sarkinsa ne.

Ka ba jama’arka nasara, * ka yi wa gâdonka albarka, * ka kiwace su, ka tallafa masu har abada.


Zabura ta 29

Ku biya wa Yahweh, ku alloli, * ku biya shi ]aukaka da yabo, * ku biya Yahweh abin da ya dace da sunansa.

Ku rusuna a gaban Yahweh. * Mai-Tsarkin ya bayyana.

    Ana jin muryar Yahweh a bisa tekuna, * Allah Ma]aukaki yana tsawa, * Yahweh yana }ara bisa teku.

    Muryar Yahweh }arfi ce, * muryar Yahweh ]aukaka ce.

         Muryar Yahweh na tsaga itatuwan al-ul, * Yahweh na tsaga itatuwan al’ul na Labanon.

              Muryar Yahweh tana tatsatsi * da harsunan wuta.

              Yana sa Labanan tsalle kamar ]an mara}i, * da Sirion kamar ]an sa.

         Muryar Yahweh tana girgiza }asar jeji, * tana girgiza }asar jejin Kadesh.

    Muryar Yahweh tana sa bareyi haifuwa, * tana zabge ganyen daji duka,

    a cikin Haikalinsa kuma * Ma]aukakin yana bayyana.

Tun ruwan tsufana Yahweh ya zauna gadon mulkinsa, * tun fil’azal Yahweh sarki ne.

Yahweh yakan ba jama’arsa nasara. * Yahweh yana sa masu albarka da salama.

Zabura ta 30

Ina girmama ka, Yahweh, * gama ka ta da ni, * ba ka kuma bar magabtana su yi mani dariya ba.

    Yahweh Allahna, * na yi kuka gare ka, * ka ma warkad da ni.

    Yahweh ya tsamo ni daga Shawol, * bayan gangarawata a Rami ka mayar mani da rai.

         Ku yi wa}a ga Yahweh, ku masu bautarsa, * ku yabi sunansa mai tsarki.

         Gama mutuwa tana cikin hushinsa, * amma rai madauwami yana wurin alherinsa.

         Da duhu ya yi ana kwanciya da kuka, * amma da Asuba ana tashi da sowa ta murna.

              A wautance sai na ce, * “Har abada ba zan yi tuntu~e ba.”

                   Yahweh, alherinka ya }arfafa ni * fiye da manyan tsaunuka.

              Amma da ka kau da fuskarka, * sai na jijjiga }warai.

         Ina kira gare ka, Yahweh, * Ubangijina, ina neman jin}ai.

         Wane amfani za a samu daga hawayena? * ko gargarawata Ramin?

         Ca~i zai ta~a yabonka? * ko zai yi shelar amincinka?

    Yahweh, kasa kunne, ka ji tausayina, * Yahweh, ka zama mai taimakona.

    Ka mai da makokina rawa, * ka kwance tsummokina, ka yi mani ]amara da murna.

    Bari zuciyata ta yi wa}ar yabonka, * kada in sake yin bakinciki.

Yahweh Allahna, * zan gode maka har abada.

Zabura ta 31

A gare ka, Yahweh, na zo neman tsari, * kada in kunyata, ya Madauwami, * a cikin amincinka ka fanshe ni.

    Ka kasa kunne gare ni, * ka cecei ni da hanzari.

    Ya Dutsen mafaka, ka zama nawa, * ya Barikin Tsira, ka cece ni.

         Gama kai ne dutsena wurin tsira, * albarkacin sunanka za ka yi mani jagora, ka nuna mani hanya.

         Za ka ’yanta ni daga tarkon * da suka ]ana mani, * domin kai ne mafakata.

              A cikin hannunka nike dan}a ruhuna, * ka fanshe ni, Yahweh Allah.

         A gaskiya na }i * jinin masu bautar gumakan banza.

         Na dogara ga Yahweh, * zan yi farinciki da murna saboda alherinka.

    Lokacin da ka ga wahalata, * kâ lura da ni gâba da Magabci.

    Ba ka }ulle ni a hannun Magabci ba, * ba ka ma sa }afafuna cikin Mugun Daji ba.

         Yahweh, ka ji tausayina, * gama ina cikin shan wahala.

         Idona ya lalace da ba}inciki, * har da ma}ogwarona da cikina.

              I, rayuwata ta gaji saboda makoki, * shekaruna kuma saboda nishi.

              {arfina ya gaza cikin wahala, * }asusuwana sun tabke, * ana kuma cin kayan cikina.

                   Na zama abin ba’a har ma ga ma}wabtana, * na zama bala’i mai ban tsoro ga abokaina; * wa]anda suka gan ni a hanya suna guduna.

                   Na yan}wane, ba hankali kamar matacce, * na zama kamar fasasshen tulu.

                       Gama ina jin ra]e-ra]e masu yawa, * ta ko’ina razana ta kewaye ni,

                       lokacin da suka taru suna shawara a kaina, * suna }ulla ma}ircin kashe ni.

                   Amma a gare ka na dogara, * Yahweh, * ina cewa, kai ne Allahna.

                   Matakan rayuwata suna a hannunka, * ka cece ni daga hannun magabtana * da na masu matsa mani lamba.

              Ka sa fuskarka ta haskaka bawanka, * ka cece ni ta alherinka.

              Yahweh, kada in kunyata, * lokacin da nike kiranka.

         Bari miyagu su kunyata, * a jefad da su Shawol.

         Ka yi wa le~unan ma}aryata takunkumi, * wa]anda ke maganar fariya da gaba ga]i * ga Mai Gaskiya Mai Zamanu.

    Abubuwan alherai barkatai ne * ka shirya wa wa]anda suke jin tsoronka,

    abubuwan da ka tanada wa masu dogara gare ka, * a gaban mutane.

         Kâ ~oye su a ma~oyar zatinka * daga }arairayin mutane.

         Kâ kare su a zaurenka * daga tankiyar harsuna.

              Alhamdu ga Yahweh! * Gama ya nuna mani }auna mai bammamaki * daga }a}}arfan birninsa.

         Dâ fargabata tana sa in zaci: * “An raba ni a gabanka.”

         Amma kâ ji ro}ona na jin}ai * lokacin da na yi kira gare ka.

    Ku }aunaci Yahweh, dukanku masu bauta masa, * gama Yahweh yana kiyaye amintattunsa.

    Amma yana sakayya mai zafi * ga masu aikata izgili.

Ku }arfafa zukatanku, * dukanku masu sa zuciya ga Yahweh.

Zabura ta 32

Albarka ga wanda aka yafe wa laifinsa, * wanda aka gafarta zunubinsa.

Albarka ga wanda Yahweh bai sa wa laifi ba, * wanda ba zamba a ransa.

    Amma ni kamar fasassar tukunya nine, * }asusuwana sun rafke * saboda nishina wuni zubut.

    Ya Ma]aukaki, dare da rana * hannunka yana yi mani nauyi.

    Na ka]u, ya Shaddai, * kamar farin bazara.

         Na sanad da zunubina gare ka, * ban kuma ~oye laifina ba.

         Na ce, “Ma]aukaki, zan fa]i * laifofina, Yahweh.” * Kâ gafarta kurena da zunubina.

              Don haka ya kamata kowane mai bauta maka * ya yi addu’a zuwa gunka.

         Lokacin da runduna ta kusato, * ko babbar ambaliyar ruwa ta malalo, * ba za su kai gare shi ba.

         Kai ne mafakata, * ka kiyaye ni daga masu afka mani, * ya Matsarata, ka cece ni, ka kewaye ni.

    Zan karantad da kai in koya maka * hanyar da za ka bi. * A kullun idona baya rufu gare ka.

    Kada ka zama kamar doki * ko alfadari mara hankali.

    Da ragama da linzami ne * za a iya sarrafa shi, * sannan ka kusance shi.

Azabun miyagu da yawa suke, * amma duk wanda ya dogara ga Yahweh, * da }auna zai rungume shi.

Ku yi farinciki da murna ga Yahweh, ku adilai, * ku yi sowar farinciki, dukanku masu zucya ta kirki.

Zabura ta 33

Ku yi farinciki ga Yahweh, ku masu gaskiya, * ku yabi Ma]aukaki, ku adalai.

    Ku yabi Yahweh da molo, ku ka]a masa garaya mai tsarkiya goma.

    Ku raira masa sabuwar wa}a, * ku yi ki]i da gwaninta da muryoyi masu da]i.

         Gama maganar Yahweh daidai ta ke, * dukan ayyukansa kuma abin dogara ne.

         Yana }aunar abin da ke na adalci da adalci, * da alheri Yahweh ya cika duniya.

              Da umurnin Yahweh aka yi sammai. * Ta kalmar da ya fa]i * aka yi rundunar taurari.

              Yana tara tekuna a cikin tulu, * yana sa zurfafan tekuna a cikin rumbu.

              Ku ji tsoron Yahweh, ku dukan duniya, * girmama shi ku dukan mazaunan duniya.

                   Ya yi magana, ta zauna, * ya yi umurni, abubuwan sun kasance.

                   Yahweh yana sukulkuce shirin al’ummai, * yana mai da tsare-tsaren jama’a banza.

                   Amma shirin Yahweh ya tabbata tun fil’azal, * manufofinsa ma na dukan zamanai ne.

                       Mai murna ce al’ummar * da Yahweh Allahnta ya albarkace ta,

                       jama’ar da ya za~a * ta zama abin gadonsa.

                   Yahweh yana kallo daga sama, * yana ganin dukan ’yan’adan.

                   Daga inda ya zauna a kan kursiyinsa yana kallon * dukan mazaunan duniya.

                   Mahallicin yana binciken zukatansu, * Mai-Gani yana kallon dukan ayyukansu.

              Sarki baya nasara * da }arfin maya}a.

              Haka ma jarumi baya ku~uta * saboda }arfinsa.

              Dokinsa baya da amfani don cin nasara, * haka ma }arfin rundunar ya}insa don kwana lafiya.

         Yahweh yana kare masu tsoronsa, * wa]anda ke dogara ga alherinsa.

         Yana cetonsu daga mutuwa, * daga yunwarta yake kare rayukansu.

    Ga Yahweh muke sa zuciya, * Shi ne mai tsare mu da garkuwarmu.

    Muna murna saboda shi, * mun amince da sunansa mai tsarki.

Yahweh, ka sa tausayinka ya kasance tare da mu, * tun da a gare ka muke sa zuciya.

Zabura ta 34

Zan albarkaci Yahweh kulluni, * a kowane lokaci yabonsa yana bakina.

A wurin Yahweh ruhuna zai sami ]aukaka, * bari gajiyayyu su ji, su yi murna.

    Ku taya ni girmama Yahweh, * mu ]aukaka sunansa tare.

    Na yi kira ga Yahweh, ya kuwa amsa mani, * daga dukan fargabana ya ku~utad da ni.

         Sun dube shi, fuskokinsu sun yi haske, * ba za su kunyata ba har abada.

         Gajiyayyen nan ya yi kira, * Yahweh ya ji shi, * daga dukan ~acin ransa ya cece shi.

    Mala’ikan Yahweh yana sintiri * kewaye da masu tsoronsa, * domin ya cece su.

    Ku ]an]ana, ku tsotsa sosai, * gama Yahweh yana da za}i, * mai albarka ne mutumin da ya amince da shi.

         Ku ji tsoron Yahweh, ku tsarkakansa, * gama masu jin tsoronsa ba za su rasa kome ba.

         Mawadata za su yi talauci, su yi yunwa, * amma masu neman Yahweh, ba za su rasa albarka ba.

              Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni, * zan koya maku tsoron Yahweh.

              Akwai wani mutun da ke son tsawon rai? * da lokaci don ya da]e yana cin albarka?

         To, ka tsare halshenka daga mugunta, * le~enka kuma maganganun }arya.

         {i mugunta, ka aikata alheri, * nemi salama, ka bi ta.

    Idanun Yahweh suna kallon masu gaskiya, * kunnuwansa kuma suna sauraren kukansu.

    Hushin Yahweh kan masu aikata mugunta ya ke, * domin ya shafe tunawa da su a duniya.

         Lokacin da masu gaskiya suke yin kuka, Yahweh yana jinsu, * don ya cece su daga dukan }acin ransu.

         Yahweh na kusa da wa]anda suka karai, * wa]anda suka fid da zuciya ma yana cetonsu.

    Gwaje-gwajen masu gaskiya yawa gare su, * amma daga dukansu Yahweh yana cetonsu.

    Yana lura da dukan }asusuwansa, * ko ]ayansu ba zai karye ba.

{eta zata kashe mugu, * ma}iyan masu gaskiya ma za su hallaka.

Yahweh yana fansar rayukan bayinsa, * masu amince wa shi ma ba za su hallaka ba.

Zabura ta 35

Yahweh, ka yi fa]a da masu fa]a da ni, * ka yi ya}i da masu ya}i da ni.

    Ka ]auki garkuwarka da warwaji, * ka wo mani gudummuwar ya}i.

    Ka zaro mashinka da gatari, * don ka yi arangama da masu jan-daga da ni.

    Ka gaya wa ruhuna cewa, * “ni ne nasararka.”

         Masu neman raina, * bari su kunyata da }as}anci.

         Masu yi mani ma}arkashiya * su juya da kunya.

              Su zama kamar }ai}ayi a gaban iska, * mala’ikan Yahweh yana tasa }eyarsu.

              Bari }addararsu ta zama Duhu da Hallaka, * mala’ikan Yahweh yana tangaza }eyarsu.

         Gama a ~oye sun gina mani rami, * sun ]ana tarko suna ha}on raina.

         Bari Ramin ya ba su mamaki, * tarkonsu ya kama su, * su kuma fâ]a cikin ramin da suka gina.

    Amma ruhuna zai yi murna da Yahweh, * ya ji da]i cikin nasararsa.

    Dukan }asusuwana za su ce, * “Yahweh, wa ke kama da kai?

    Kâ ku~utad da gajiyye daga hannun wanda ya fi shi }arfi, * shi da mabukaci daga hannun mai zaluntarsu.

         Mashaidan }arya sun tayar mani, * wa]anda ban sani ba sun yi mani tambayoyi.

         Sun saka mani alheri da mugunta, * suna ba}anta ruhuna.

         Amma ni, lokacin da suka busa sarewa, * na sa tsumma.

              Na hori kaina ta wurin azumi, * addu’ata ta li}e a }irjina, * sai ka ce abokina ko kuma ]an’uwa.

              Ina tafiya kamar mai makokin mahaifiyarsa, * na dukufa da ~akinciki.

         Da na yi tuntu~e, sai su fashe da dariya, * ’yan dambe sun kewaye ni.

         Wa]anda ban sani ba suna ta yayyage ni, * ba su kuma dena yi mani }araiyayi ba.

         Masu ba’a kewaye da ni * suna ta murgu]a mani baki.

    Ya Ubangiji, don me ka tsaya kana kallo kawai? * Ka ceci raina daga ramukansu * fuskata kuma daga kuyakuyan zakoki.

    Zan gode maka a cikin babban taro, * a cikin babban biki ma zan yabe ka.

         Kada magabtana masu ha’inci su yi murna a kaina, * ko ma magabtana masu limshe idanu.

         Gama ba sa yin maganar salama, * amma suna afka wa marasa galibu na }asar.

              Sun shirya makirci, * duk sun wage bakunansu a kaina.

              Suna cewa, “Aha, Aha! * mun gan shi.”

                   Duba, Yahweh, kada ka yi shuru, * ya Ubangiji, kada ka yi nesa da ni.

                   Hanzarta ka zaburo don kâre ni, * ya Ubangijina da Allahna, ka taya ni fama.

              Yahweh, ka kâre ni a cikin adalcinka, * ya Allah, kada ka bari su yi mani dariya,

              ko su yi fahariya a cikin zukatansu, * su ce, “Haba, bakinmu ya kama shi,” * ko su ce, “Mun gama da shi.

         Duk masu murna da rashin katarina, * bari su kunyata, su sha }as}anci.

         Duk masu shuka }arya a kaina, * bari a lullu~e su da kunya da }as}anci.

    Amma duk masu son yin nasarata, * ka sa su yi sowa ta murna.

    Su dinga cewa: * “Yahweh akbar!” * mai son zaman lafiyar bawansa.

Sannan ne halshena zai yi shelar adalcinka * in kuma yi yabonka dukan yini.

Zabura ta 36

Zunubi yana hura birnin zuciyar mugu, * baya ma fahimtar ma’anar tsoron Allah.

    Amma Allahnsa zai hallaka shi da harara, * tun da yake ya ga sa~onsa.

    Maganarsa cike take da miyagun }arairayi, * }etarsa tana hana shi tunani ko yin abin kirki.

Yana }aga mugunta a kan gadonsa, * kamin ya fita aikatata, * baya ma jin kunyar aikata kowane mugun abu.

    Yahweh, }aunarka daga sama take, * amincinka ya kai har cikin gajimarai.

    Nagartarka ta milla sama kamar manyan duwatsu, * }addararka tana da zurfi kamar teku.

         Yahweh, kakan adana mutane da dabbobi, * alherinka akwai girma!

    Alloli da mutane suna samun mafaka * a innuwar fukafukanka.

    Suna biki da abinci mai kyau na gidanka, * kana shayar da su kuma daga kogin alherinka.

Kai ne tushen rai, * a cikin aljannarka za mu ga haske.

    Ci gaba da }aunatar wa]anda suka san ka, * yi alheri ga masu zukatai nagari.

    Kada }afar mai girman kai ta cim mani, * kada dantsen mugu ya yâ da ni }asa.

Dubi yadda masu aikata mugunta ke fa]i, * sun fâ]i }asa warwas, ba su iya tashi.

Zabura ta 37

Kada ranka ya ~aci saboda miyagu, * kada kuma ka ji haushin masu aikata sharri.

Domin sauran ka]an za su bushe kamar ciyawa, * kamar ]anyen ganye za su shu]e.

    Ka dogara ga Yahweh, ka aikata nagarta, * ka zauna a }asar, ka ci wadatarta.

    Ka gamsu da Yahweh * zai kuwa biya maka bukatar zuciyarka.

         Ka dan}a dabararka ga Yahweh, * ka dogara gare shi, zai kuwa cika ta.

         Zai sa adalcinka ya haskaka kamar rana, * hakkinka kuma kamar tsakar rana.

         Ka jira Yahweh, * ka sa zuciya gare shi.

         Kada ranka ya ~aci kan mutumin da ya arzuta, * yana nasara kan miyagun shirye-shiryensa.

    Dena hushi, ka ya da harzu}a, * kada ka cika damuwa, lahani kawai take jawowa.

    Domin za a sassare miyagu, * amma tabbaci hakika masu kira da sunanYahweh za su gaji }asar.

Sauran ka]an miyagu za su shu]e, * in ka duba gidajensu, ba sa nan.

Amma gajiyayyu za su gaji }asar, * za su kuma ji da]in albarka mai yawa.

    Mugu yakan yi wa mai kirki ma}ar}ashiya, * har yana cizon ha}ora a kansa.

    Ubangiji yana yi masa dariya, * domin ya ga ajalinsa yana gabatowa.

         Miyagu suna zaro takobinsu, * suna ]ana baka

         su ka da gajiyayyu da matalauta, * don su karkashe masu aikata gaskiya.

         Takobinsu zai sassoki zukatansu, * bakanninsu kuma za su kakkarye.

              Gara talaucin mai adalci * da wadatar mugu.

              Domin wadatar miyagu zata rushe, * amma Yahweh zai tallafi masu gaskiya.

         Yahweh yana lura da wadatar masu gaskiya, * gadonsu zai wanzu har abada.

         Ba za su bushe a lokacin fari ba, * amma za su }oshi a kwanakin yunwa.

    Amma miyagu za su yan}wane, * magabtan Yahweh za su hallaka

    kamar daji mai }onewa, * fiye da haya}i za su shu]e.

    Mugu yakan ci bashi, ya }i biya, * amma mai adalci yana bayaswa hannu sake.

    Wa]anda ya sa wa albarka za su gaji }asar, * amma wa]anda ya la’anta sassare su za a yi.

         Yahweh ne yake kare matakan mutun, * yana kuma tabbatad da tafiyarsa.

         In ya kai hari ba za a yi takara da shi ba, * domin Yahweh yana ]aga hannunsa.

              Dâ ni yaro ne, amma na tsufa, * tun da nike ban ta~a ganin inda aka ya da mai gaskiya ba, * ko kuma a ga ’ya’yansa na barar abinci.

              A kullun yakan ba da rance hannu sake, * ’ya’yansu kuma albarka ce ke biye da su.

         Rabu da mugunta, ka aikata alheri, * don ka wanzu har abada.

         Domin Yahweh yana }aunar masu gaskiya, * baya kuma ya da masu bauta masa.

    Za a hallaka miyagu, * ’ya’yansu ma za a sassare su.

    Amma masu gaskiya za su gaji }asar, * su zauna cikinta har abada.

Bakin mai gaskiya yana maganar hikima, * halshensa ma na fa]ar abin da ke daidai.

Shari’ar Allah na cikin zuciyarsa, * }afafunsa kuma ba za su yi tuntu~e ba.

    Da mugu ya makirci mai gaskiya, * yana neman kashe shi,

    Yahweh ba zai sa shi a hannunsa ba, * ba ma zai bari a same shi da laifi ba in an tuhunce shi.

         Ka jira Yahweh, * ka kiyaye hanyarsa,

         domin zai ]aga ka don ka mallaki }asar. * Za ka ga ran da za a sassare miyagu.

         Na ta~a ganin mugu da wadata, * ya yi tsawo kamar }a}}arfan itacen al’ul.

         Amma ya shu]e, ba a }ara ganinsa ba, * na nem shi, amma ba a iya samunsa.

    Ka bi mala’ikan Kirki, ka dubi mala’ikan Gaskiya, * gama akwai albarka ga mutumin kirki.

    Amma za a hallaka mutanen banza kwatakwata, * ba ma wata albarka da miyagu za su samu.

Daga wurin Yaweh ceton adalai yake, * shi ne mafakarsu a lokacin hari.

Yahweh ne zai ku~utad da su, ya cece su, * zai fanso su daga hannun miyagu,

ya ba su kariya, * domin sun nemi mafaka a gunsa.

Zabura ta 38

Yahweh, kada ka tsananta mani loton hushinka, * kada ma ka hore ni da zafin hushinka.

    Gama kibanka sun shisshige ni, * dantsenka kuma ya afko mani.

         Ba lafiya a naman jikina, * saboda haushinka.

         Ba }arfi a }asusuwana, * saboda zunubina.

    Domin sharrin }etata ya dawo kaina, * kamar kaya mai nauyi ya dan}are ni.

         Miyakuna suna zama gyambuna, suna ]oyi, * don wawancina.

              Duk na yan}wane, ina kwance, * ina ba}inciki wuni zubut.

              Domin jijiyoyina suna fama da zazza~i, * ba lafiya a naman jikina.

         Na gaji, na tafke, * ina kururuwa da nishi a zuciyata.

              Ya Ubangiji, duka ajiyar zuciyata tana gabanka, * kururuwata ba ta barin gabanka.

                   Zuciyata tana harbawa, * ba ni da }arfi.

                       Har ma ganin idanuna, * ya dushe.

                       Aminaina da abokan tafiya * sun kauce daga damuwata, * dangina sun yi nesa da ni.

                   Masu neman raina sun kafa mani tarko, * masu son ganin fa]uwata suna bina.

              Bala’i da lalacewa * suke yi mani fata dukan yini.

         Amma na yi kama da bebe da baya ji, * kamar kurma da baya magana.

              Na zama kamar beben da baya ji, * wanda babu wata tsawatawa daga bakinsa.

              Amma gare ka, Yahweh, kai ne nike jira, * Ubangijina da Allahna, ka amsa mani da nike cewa:

         “Kada su yi murna a kaina, * kada su zage ni in na yi sassarfa.

    Gama muguntata ta tsaya a kaina, * bakincikina yana gabana kullun.

         I, ina rungume laifina a gabana, * ina firgita saboda zunubina.

         Ma}iyana masu }arfi ne, * magabtana masu ha’inci suna da yawan gaske.

    Masu rama mugunta da alheri * suna zagina, lokacin da nike nema masu alheri.

Yahweh, kada ka yashe ni, * ya Allahna, kada ka yi nesa da ni.

Ka gaggauta taimakona, * ya Ubangiji, ka cece ni!

Zabura ta 39

Na ce, “Zan yi hankali da abin da nike yi, * kada in kuskure da halshena.

Zan yi wa bakina linzami, * sa’ad da mugu ke yin surutu a gabana.”

Na yi shuru tsit, * na }i yin magana, * damuwata ta taso.

    Zuciyata tana yi mani }una, * in na yi tunani a kai, sai ka ce an cinna mani wuta.

Sai na yi magana, na ce, * “Yahweh, ka sanar da ni }arshena,

in san ko kwana nawa suka rage mani, * bari in san ajizancina.”

Ga shi, ka mai da rayuwata ’yar guntuwa, * shekaruna a gabanka kamar babu ne.

    Kash! Kowa kamar haya}i ne, * kowane mutun siffa ne kawai.

         Kash! Mutun kamar iska yake zagayawa. * Kash! Yana fusata a banza.

         Yana jibge dukiya, * bai kuwa san mai cinta ba.

              Amma yanzu, ya Ubangiji, me zan ro}a, * Begena yana gare ka.

              Daga dukan taurin kaina ka cece ni, * kada ka mai da ni gurbin wawa.

         Na zama bebe, ban bu]e bakina ba, * ya Ubangiji, yi wani abu!

         Ka kawar mani da bugunka, * domin kulkin hannunka zai hallaka ni.

    Da tsawatawar laifin mutun kake horonsa, * kakan ci jikinsa kamar asu. * Kash! Kowane mutun kamar iska ne.

Yahweh, ka ji addu’ata. * Ya Allah, ka saurari ro}ona.

Kada ka zama bebe ga kwallana, * domin ni ba}o ne a gidanka, * mai ziyara kamar dukan kakannina.

Ka kau da fuskarka daga wajena don raina ya ji da]i, * kafin in }aura, in dena wanzuwa.

Zabura ta 40

Na yi ta kiran Yahweh, * ya kuwa karkato gare ni, ya amsa kukana.

    Ya tsamo ni daga Ramin Hallaka, * daga Lema Mai Ca~i.

         Ya ]ora }afafuna a kan dutse, * na taka tudun-na-tsira.

    Ya sanya sabuwar wa}a a bakina, * wa}ar yabon Allahnmu.

Da yawa za su gani, su ji tsoro, * su ma dogara ga Yahweh.

    Albarka ta tabbata ga mutumin * da ya dogara ga Yahweh,

    bai juya ga gumaka ba, * ko ga siffofin }arya.

         Yahweh, kâ yi manyan ayyuka, * ya Allahna, kâ aikata al’ajibai masu bammamaki.

              Kana tunaninmu kullun, * ba wani kamarka.

         Da na so in fa]e su duka, * sun fi gaban }idaya.

              Ba ruwanka da hadaya ko baiko, * shi ya sa ka shirya kunnena ya ji.

              {onannen baiko da na gafarar zunubi * ba ka bukata.

                   Sannan na yi alkawali na ce, * “Ga shi, ina zuwa.

                   A cikin shafofin Littafi ne * aka rubuta wajibaina.

                   Ina jin da]in aikata nufinka * ya Allahna, shari’arka tana cikin birnin zuciyata.”

              Na bayyana albishir mai da]i na cetonka * ga babban taron jama’a.

              I, ban kulle le~unana ba, * kai ma ka sani, Yahweh.

         Ban rufe alherinka * a birnin zuciyata ka]ai ba.

              Na bayyana amincinka * da aikinka mai ceto.

         Ban ~oye }aunarka * da amincinka ga babban taron ba.

    Yahweh, kai ba ka hana }aunarka * zuwa gare ni ba.

    Alherinka da amincinka * suna kiyaye ni a kullun.

Amma wahaloli sun kewaye ni, * har ba su }idayuwa.

{ai}an zunubaina ya komo mani, * har bana iya tsira.

    Sun fi gashin kaina yawa, * zuciyata kuma ta karai.

    Gaggauta, Yahweh, ka cece ni, * Yahweh ka yi hanzari ka taimake ni.

         Bari dukan masu neman raina * su kunyata, su sha }as}anci.

         Duk masu neman kisa * su koma da kunya da }as}anci.

         Duk masu ce da ni, “Yauwa, yauwa!” * bari su karai don tseguminsu.

    Bari dukan masu nemanka * su yi murna da farinciki a wurinka.

    Bari dukan masu son cetonka * su yi ta cewa: “Yahweh akbar!”

Ko da nike gajiyayye da mabukaci, * Ubangiji zai tuna da ni.

Kai ne mataimakina, macecina, * ya Allahna, kada ka yi jinkiri.

Zabura ta 41

Albarka ga mai magana da azanci, * a lokacin hatsari Yahweh ya cece shi.

    Yahweh ya kiyaye shi, ya tsawanta rayuwarsa, * ya yi masa albarka a duniya, * kada ya ba da shi ga magabtansa.

    Yahweh ya tallabe shi a kan gadon jiyyarsa, * ka yi masa rangwame, * ka kau da ciwonsa.

         Na ce, “Yahweh, ka ji tausayina, * ka warkad da ni, * ko da yake na yi maka laifi.

              Magabtana suna zagina, suna cewa, * “Yaushe ne zai mutu, a manta da sunansa?”

              In waninsu ya zo ya gaishe ni, * yana }aga }arya a zuciyarsa.

              Yana tattara wa kansa }eta, * ya fita waje, yana tsegumguma.

                   Duk ma}iyana, ya Ma]aukaki, * suna ra]a da junansu a kaina, * suna shirya mani ma}ar}ashiya, cewa:

                   “Zuba masa wani abu mai dafi, * domin wanda yake kwance kada ya sake tashi.”

              Har ma abokina * wanda na amince da shi,

              wanda muke ci a kushi ]aya, * yana }ulla }arairayi a kaina.

         Amma kai, Yahweh, ka ji tausayina, * ka tashe ni, * domin in saka masu.

    Sannan ne zan san kana sona, * in dai Magabcina bai yi rinjaye a kaina ba.

    Saboda cikar kirkina ka sure ni, * ka aje ni a gabanka har abada.

Albarka ga Yahweh, Allah na Isra’ila, * tun fil’azal har abada abadin.

Amin. Amin.

Zabura ta 42

Kamar yadda kishimi ke kururuwa don ruwan rafi, * haka raina ke kururuwa gare ka, Allah.

Raina yana jin }ishi, * Allah, ya rayayyen Allah.

Yaushe ne zan soma sha * a gaban fuskar Allah?

    Hawayena sun zama abincina * dare da rana,

    a kullun kuma ana tambayata, * “Ina Allahnka?”

Wa]annan abubuwa nike tunawa, * zan zubar da ruhuna gare shi

in na }etare dokin }ofa, * in na kwanta rub da ciki * kusa da gidan Allah,

inda ake yin sowar ta yabon Allah, * tare da taron alhazan {udus.

    Me ya sa kake ~aci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

    Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna

         Zuciyata ta karaya, * Ma]aukakin Zati, ina tunawa da kai

              daga Magangaran Lahira duk da tarunanta, * daga gindin dutsenta.

              A can ruwa mai zurfi ke kiran ruwa mai zurfi, * yana amsa wa tsawarka.

         Dukan ra}uman ruwanka masu husata * suna ta]iye ni.

              Dâ Yahweh yakan aiko mani da alherinsa da rana, * da ru’yarsa kuma da dare.

         Ina yin addu’a ga Allahna rayayye, * ina cewa, “ya Allah, Dutsena,

              me ya sa ka mance da ni? * Me ya sa nike sha takaici

              saboda matsawar Magabci, * saboda Makashin cikin }asusuwana?”

         Ma}iyana suna bakanta mani, * a kullun suna cewa da ni, * “Ina Allahnka?”

    Me ya sa kake ~aci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

    Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna

(Zabura ta 43)

Ka kâre ni, ya Allah, * ka tsaya wa hakkina.

Ka fanshe ni daga hannun marasa bin Allah, * daga hannun mayaudara, marasa gaskiya.

    Tun da kai ne Allah Mafakata, * me ya sa ka yâ da ni?

    Dom me nike shan takaici * saboda matsawar Magabci?

         Ka aiko da haskenka da gaskiyarka, * i, bari su yi mani jagora.

         Bari su kai ni zuwa dutsenka mai tsarki * wurin zamanka.

    Bari in tafi wurin bagaden Allah, * gun Allah, mai faranta mani rai.

    Bari in yabe ka da garaya, * ya Allah, Allahna.

Me ya sa kake ~aci, ya raina? * Me ya sa kake nishi a gabana?

Jira Allah, * domin zan ci gaba da yabonsa, * Macecina, Ikona da Allahna.

Zabura ta 44

                   Ya Allah, mun ji da kunnuwanmu,* kakanninmu sun gaya mana

                   ayyukan da ka yi a zamaninsu, * a zamanin dâ hannunka ya aikata al’ajibai.

                   Kâ kori sauran al’ummai, * amma kâ dasa taka.

                   Kâ warwatsa sauran kabilu, * amma kâ sa taka ta yi toho.

Ba da kaifin takobinsa suka ci }asar ba, * ba da }arfin dantsensu suka yi nasara ba,

amma ta hannun damanka da dantsenka ne * da hasken fuskarka, * tun da yake ka }aunace su.

    Kai ne Sarkina, Allahna, * Shugabana, Macecin Yakubu.

    Ta wurinka mun fatattaki abokan gabanmu, * ta sunanka muka tattaka masu nemanmu da ya}i.

Domin ban dogara ga bakana ba, * takobina kuma bai sa in ci nasara ba.

Amma ka sa mun yi nasara kan abokan gabanmu, * ka kuma kunyata ma}iyanmu.

    Da Allah ne muke yin ta}ama kullun, * sunanka ne kuma za mu yaba har abada.

         Amma ka yi watsi da mu, ka }as}antad da mu, * ba ka kuma }ara taya sojojimu ba.

         Ka sa abokan gabanmu su ga }eyarmu, * ma}iyanmu kuma sun }wace kayanmu.

              Ka bashe mu kamar bisashen da za a yanyanka, * ka warwatsa mu a cikin al’ummai.

              Ka sayar da mutanenka arha, * ba su yi tsada ba.

         Ka mai da mu abin zagi ga ma}wabtanmu, * abin reni da ba’a ga wa]anda ke kewaye da mu.

         Ka mai da mu abin zun]e ga al’ummai, * abin ka]a kai ga mutane.

              Wulakancina yana gabana kullun, * kullun ina sane da kunyata,

              saboda muryar mai zagin nan da mai sa~on nan, * saboda magabci da mai neman ramuwa.

         Kowane wulakanci ya zo mana, * amma ba mu mance da kai ba, * ko yin rashin biyayya da yarjejeniyarka.

         Zuciyarmu ba ta juya baya ba, * }afafunmu kuma ba su goce daga hanyarka ba,

              ko da yake ka wahalshe mu da ciwon gindi, * ka ma rufe mu da duhu ba}i} }irin.

         In da mun mance da sunan Allahnmu, * ko mun mi}a hannu ga wani allah,

         ashe Allah ba zai tona wannan ba? * tun da yake ya san lungu-lungu na zuciya.

    Duk da haka, saboda kai ne ake kashe mu yini zubut, * ana }irga mu kamar tumakin da za a yanka.

Ka farka! Dom me kake barci, ya Ubangiji, * ka tashi, kada ka yi hushi, ya Jarumi.

    Me ya sa ka kau da fuskarka, * ka mance da }uncinmu da danniyar da ake yi mana?

    Domin wűyanmu ya bunkuya cikin tur~aya, * cikinmu ya nane }asa.

Ka tashi, ka agaje mu, * ka fanshe mu saboda }aunarka.

Zabura ta 45

Zuciyata ta wallafa wa}a mai da]i, * zan raira aikina, ya Sarki, * halshena alkalamin }wararren marubici ne.

    Kai ne mafi kyau a cikin dukan ’yan’adan, * da]]a]ar magana na fitowa daga le~unanka.

    Allah, Ma]aukakin Zati, * ya albarkace ka tun fil’azal.

         Ka ]ora takobinka a kan cinyarka, * ka rinjaya da darajarka, * ka ci nasara da sarautarka.

         Ka rinjaya a harinka saboda gaskiya, * ka ma kâre matalauta.

              Al’ajiban hannunka na dama da kibanka masu tsini * su za su sa ka yi suna.

              Al’ummai za su fâ]i a gabanka, * magabtan Sarki su kwanta sumammu.

                   Allah Madauwami ya tabbatar da sarautarka, * sandar sarautarka sanda ce ta gaskiya.

                       {aunaci gaskiya, ka }i mugunta, * Madauwamin Zati ya shafe ka, * Allah, Allahnka.

                   Mayafanka ne man farinciki, * duk tufafinka su ne mur da aloyes da tafasa.

              Ai, akwai gidajen hauren giwa barkatai, * don faranta maka zuciya.

              ’Ya’yan sarakuna mata na cikin matan fâdarka, * sarauniya na tsaye a hannun damanka da kayan zinarya ta Ofir.

         Saurara, ke ]iya, ki gani, * ki kasa kunne: * Manta da mutanenki * da gidan mahaifinki.

         Domin Sarki yana marmarin kyanki, * i, shi ne ubangijinki, * ki yi masa sujada.

         Riga daga garin Taya tana a cikin kyautayinki, * manyan ba}i ma suna bi]ar alherinki.

    Dukan tufafinta iri na sarauta ne, * a ciki an yi masu dajiya da zinariya, * gwanayen ma]inka ne suka yi kayanta.

    Bari a kai Gimbiya wurin Sarki, * daga baya kawayenta su bi.

    Ku zo, bari a raka ta da murna da farinciki, * a shigar da ita fâdar Sarki.

Gurbin kakanninka ’ya’yanka za su maye, * za ka maishe su sarakunan dukan duniya.

Zan yi shelar sunanka a dukan zamanai, * dukan jama’a za su yabe ka, ya Ma]aukaki Madauwamin Zati.

Zabura ta 46

Allah ne ma~oyarmu da mafakarmu, * Mai Duka, mun same shi Macecinmu daga ya}i.

    Ma]aukakin Zati, ba za mu ji tsoron * mu}amu}an {al}ashin {asa ba.

         Ko fa]awar duwatsu * a tsakiyar teku,

             ko da ruwayen teku na kumfa, * duwatsu na fâ]uwa cikinsu, * igiyoyin ruwa suna gilme-gilme.

             Allah yana kawo wa birninsa farinciki, * Ma]aukaki yana tsarkake mazauninsa.

         Da yake Allah na cikinsa, * ba zai girgiza ba.

     Zai taimake shi * tun da asuba.

Al’ummai sun raunana, * sarautu sun jijjigu.

Ya yi furci, * duniya ta narke.

Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.

    Ku zo, ku ga ayyukan Yahweh, * wanda ya sa wa duniya albarka.

         Yakan tsaid da ya}i * har bangon duniya.

         Ya kan karya baka, yana lalata mashi, * yana }one karusai da wal}iya.

    Ku kwantar da hankalinku, ku sansance ni ne Allah, * ina bisa al’ummai, * na ma mallaki duniya.

Yahweh mai runduna yana tare da mu, * mafakarmu shi ne Allahn Yakubu.

Zabura ta 47

Dukanku }afarfan ruhuna, ku yi tafi, * ku alloki, ku yi sowa ta murna.

    Yahweh Ma]aukaki mai ban tsoro ne, * babban sarki ne bisa dukan duniya.

    Ya bi mana da mutane, * ya sa al’ummai a }al}ashen }afafunmu.

    Ya za~i mulkinmu don kansa, * }asar Yakubu abar ta}ama da yake }auna.

         Allah ya hau da sowa, * Yahweh da muryar kakaki.

         Ku raira yabbai, ku alloki, ku raira yabbai, * ku raira yabbai ga Sarkinmu, ku raira yabbai.

    Gama shi ne Sarkin dukan duniya, * ku alloli, ku raira yabo da gwaninta.

    Allah ne ke mulkin al’ummai, * yana zaune kan tsattsarkan kursiyinsa, * ku sarakunan jama’a, ku tattaru.

Allahn Ibrahim Mai Iko ne, * Allah shi ne Mai duniya, * shi ne kuma mafi dacewa da ]aukaka.

Zabura ta 48

Yahweh mai girma ne, * ya cancanci matu}ar yabo.

A birnin Allahnmu * akwai tsattsarkan dutsensa.

    {ololuwa mai kyan gani, * da ke faranta wa dukan duniya rai,

    Dutsen Sihiyona ne babban birnin duniya, * birnin Sarki mai girma.

    Karagarsa Allah ne * da gwadajjiyar mafaka.

         Gama sarakunan sun taru, * sun kai hari tare.

         Da suka ga garin sun yi mamaki, * suka firgita, suka ranta a noman kare.

              Tsoro ya kama su * i, azaba kamar ta mace mai na}uda,

              kamar yadda iskar gabas * kan kakkarya jiragen ruwan Tarshishi.

                   Kamar yadd muka ji, * haka muka gani

                       a birnin Yahweh mai runduna, * a birnin Allahnmu.

                   Allah zai tabbatad da shi * har abada abadin.

              Mun tuna da }aunarka, ya Allah, *a tsakkiyar Haikalinka.

              Kamar sammanka, ya Allah, * haka yabonka ke kaiwa har bangon duniya.

         Hannun damanka cike yake da alheri, * bari dutsen Sihiyona ya yi murna,

         }auyukan Yahuda kuma su yi farinciki, * saboda ayyukanka na tsare su.

    Ku zaga Sihiyona, ku kewaye ta, * ku }irga hasumiyoyinta.

    Ku dubi ganuwarta, * ku binciki ginin tsaronta,

donin ku gaya wa tsara mai zuwa, * cewa “Birnin nan na Allah ne.”

Madauwamin Allahnmu * shi zai bishe mu har abada.

Zabura ta 49

Ku ji wannan, ku dukan jama’a. * Ku saurara, ku dukan mazauna duniya,

}as}antattu da ]aukakakku, * mawadata da matalauta duka.

Bakina zai yi zancen hikima, * zuciyata za ta furta fahinta.

Zan kasa kunnena ga misali, * zan ra]a kacinci-kacincina da ki]in molo.

    Don me zan ji tsoron miyagun kwanaki, * ko }etar ma}aryata kewaye da ni,

    wa]anda ke dogara ga dukiyarsu, * suke fahariya da ]umbin wadatarsu?

         Kai! Mutun baya iya ceton kansa, * ko ya biya wa Allah fansarsa.

         Gidan Can {asa zai zama fansar ransa, * zai tafi har abada,

              ko da yake dâ ya iya rayuwa da murna har abada, * da ma bai ga Ramin ba.

         In Allah ya fuskanci masu hikima, za su mutu. * In ya harari wawaye,

         nan da nan za su hallaka, * su bar wa wasu dukiyarsu.

    Loton da suke a madauwamin gidansu, * mazauninsu na har abada,

    magadansu a duniya * suna ambaton sunayensu.

A Gidan {asa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka shu]e.

    Wannan ce }adarar mawadata, * da }arshen masu mugun kwa]ayi.

    Tamkar bisashe za a jefa su a Shawol, * Mutuwa ce za ta zama mai kiwonsu.

         Za su gangara cikin ma}ogwaronta kamar ]an mara}i, * Shawol za ta ha]iye ga~o~insu, * Mai Cinyewa zai gama da su.

         Amma Allah zai fanshe ni, * ba shakka zai kwato ni daga hannun Shawol.

    Kada ka yi }yashin mai arziki, * lokacin da wadatar gidansa ke ha~~aka.

    Domin lokacin da ya mutu ba zai tafi da kome ba, * dukiyarsa ba za ta bi shi ba, * ko da ya bauta wa sha’awarsa lokacin da yake da rai.

    Duk da ana yabonka in ka arzuta, * za ka shiga taron kakanninka, * wa]anda ba za su }ara ganin haske ba.

A Gidan {asa mutun zai yi barci sosai, * zai yi kama da dabbobin da suka shu]e.

Zabura ta 50

Allahn alloli shi ne Yahweh, * ya yi magana, ya kirayi duniya, * daga fitowar rana zuwa fa]uwarta.

Daga Sihiyona, cikamakin kyau, * Allah ya hasko.

    Allahnmu yana zuwa, * ba zai yi shuru ba.

    Wuta mai cinyewa na tafe a gabansa, * kewaye da shi kuma da hadari mai tsawa.

    Ya kirayi sama da }asa * wajen shari’ar jama’arsa.

Ku tattaro masa masu yi masa bauta, * masu jarjejeniya da shi a gaban hadaya.

Bari sammai su yi shelar hakkinsa, * domin shi ne Allah mai gaskiya.

    “Ku saurara, jama’ata, zan yi magana, * Isra’ila kam, zan yi magana mai gâba da ke. * Ni ne Allah, Allahnki.

    Ban tsauta maki saboda hadayunki ba, * ko hadayun }onawarki da ke gabana kullun.

    Ban bi]i bajimin sa daga gidajenku ba, * ko awaki daga garkunanku,

         tun da yake dukan namomin daji nawa ne, * da dabbobin da ke bisa duwatsu.

         Na ma san dukan tsuntsayen da ke kan duwatsu, * duk mai yawon karkara ma a gabana yake.

         Da na ji yunwa, da ba zan gaya maku ba, * domin duniya tawa ce da dukan abin da ke cikinta.

         Ina cin naman bajimai, * ko in sha jinin awaki?

    Mi}a wa Allah hadayarka ta godiya, * ka cika wa’adodinku ga Ma]aukaki.

    Sannan ka kira ni a lokacin wahala, * zan cece ka, in kira ka biki.”

    Amma game da mugu Allah ya ce: * “Ta yaya za ka furta dokokina, * ka ambaci yarjejeniyata da bakinka?

    Tun da yake ba ka son a koya maka, * kana kuma yin watsi da kalmomina.

         Lokacin da ka ga ~arawo, kana yin gasa da shi, * kana kuma cudanya da mazinata.

         Da bakinka kake furta mugunta, * da halshenka kake sa}a yaudara.

         Ka zauna kana yin gulma da }anenka, * kana ya]a aibu ga ]an mahaifiyarka.

    Duk ka yi wa]annan abubuwa, * to, ni zan yi shuru ne?

    Kâ shirya makirce-makirce, * ni ma kamarka ne?

    Zan tuhume ku, in gabatad da }ara * a gaban idanunka.

Ku yi tunani kan wannan, ku da ke mance wa Allah, * kada in cafke ku, ba mai }wacewa.

Duk wanda ya mi}a hadayar yabo, * zan gayyace shi biki.

Wanda ya tsaya a kan hanyata, * zan shanyad da shi sosai da ceton Allah.”

Zabura ta 51

Ka ji tausayina, ya Allah, * saboda }aunarka.

Saboda yawan rahamarka, * ka shafe tawayena.

Zubo ruwa, ka wanke ni daga muguntata, * ka tsarkake ni daga zunubaina.

    Sharrin }eta da ke tuhumata na san shi, * zunubina gabana yake kullun.

    Kai ka]ai ne na yi wa laifi, * na yi zunubin nan a idanunka.

         To, ka yi daidai a shari’ar da ka yanke, * hukuncin da kakan yi ba shi da aibu.

    I, da laifi aka ]auki cikina, * ni mai zunubi ne tun haifuwata.

    I, ka fi son gaskiya * fiye da sanin boka da wayon wulli, * ka koya mani hikima.

         Ka raba ni da zunubi, * zan kuma tsarkaka fiye da ruwan }al}ashin dutse, * ka wanke ni, zan fi auduga fari.

         Bari in ji farinciki da murna, * bari }asusuwan da aka rumurmutse su farfa]o.

              Ka kau da fuskarka daga zunubaina, * ka shafe dukan }etata.

                   Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, * ka sa mani sabon ruhu na biyayya.

              Kada ka kore ni daga gabanka, * ko ka }wace mani Ruhunka Mai Tsarki.

         Ka mayar mani da farinciki na cetonka, * ka }arfafa ni da ruhun biyayya,

         domin in koya wa masu tawaye hanyoyinka, * masu zunubi kuma za su juyo gare ka.

    Ka cece ni daga }wallan mutuwa, * ya Allah, Allahna.

    Sannan ne, Macecina, * halshena zai raira yabon alherinka da }arfi.

         Ya Ubangiji, ka bu]e le~unana, * halshena kuma zai furta yabonka.

    Da ka so hadaya, * da na mi}a, * da ka yi marmarin hadaya ta }onawa, da na bayas.

    Hadaya mafi kyau, ita ce ruhu na }as}anci, * }as}antaciyyar zuciya, ya Allah, ba za ka yas ba.

Ka sabunta kyan Sihiyona da alherinka, * ka sake ginin ganuwar Urushalima.

Sannan ne za ka kar~i hadayun da ke daidai, * }onannun hadayu, * har ’yan mar}a za su hau bagadinka.

Zabura ta 52

Don me kake alfari da }eta, kai gawurtaccen mutun? * Mai bautar Allah, me ya sa ka ke tunanin fitina kullun?

    Halshenka kamar kakkaifar aska yake, * ya kai gwanin yaudara.

    Ka fi son mugunta da nagarta, * da }arya maimakon fa]in gaskiya.

    Kana }aunar dukan batutuwa * da halshenka mai yaudara ke yi.

         Allah ya hana ka haifuwa har abada, * ya rushe ka da tsawa!

         Ya koro ka daga alfarwarka, * ya janye rayukan ’ya’yanka daga duniya.

              Masu gaskiya za su duba da tsoro, * amma daga baya za su yi masa dariya, su ce:

         “Ga mutumin nan * da bai mai da Allah mafakarsa ba,

         amma ya dogara ga yawan wadatarsa, * ya dogara ga mugun abunsa.

    Ni dai, kamar itacen zaitun ne, * da ke girma a cikin gidan Allah,

    na dogara ga }auna * ta Madauwamin Allah.

Ina yabonka, ya Madauwami, * domin ka aikata.

Zan yabi sunanka * mai da]i gun masu bauta maka.

Zabura ta 53

Wawa yana tunani a zuciyarsa, * cewa, “Allah baya nan.”

Masu ha’inci ne, suna yin miyagun abubuwa, * babu wani mai aikata alheri.

    Daga sama Allah yana dubo * dukan ’yan’adan,

    ya gani ko akwai masu hikima, * da ke neman Allah.

         Amma dukansu sun bau]e, * duk miyagu ne.

         Babu mai yin kirki a cikinsu, * ko mutun ]aya.

         Masu aikata aibu ba su sani ba, * in sun washe jama’arsa,

         suna cin hatsin Allah, * wanda ba su yi girbi ba?

    Ga yadda suka yi }ungiya ta sojinsu, * amma hari bai da]e ba,

    domin Allah ya yi kaca-kaca * da }asusuwan masu kai maku hari.

    Kun karai * sai da Allah ya tara gawarwakinsu.

Daga Sihiyona wa zai kawo wa Isra’ila ceto? * Lokacin da Allah ya sake arzuta jama’arsa,

bari ’ya’yan Yakubu su yi farinciki, * ’ya’yan Isra’ila su yi murna.

Zabura ta 54

Ya Allah, ka cece ni da sunanka, * ta ikonka kuma ka kâre ni.

    Ya Allah, ka ji addu’ata, * ka kasa kunne ga kalmomin bakina,

         domin ba}i sun tasam mani, * ’yan iska suna neman raina, * ba su san Allah shugabana ba ne.

              Dubi yadda Allah ya zama mataimakina, * Ubangiji Matallafin raina.

         Ya saka wa masu ~ata mani suna da muguntarsu, * da amincinsa ya hallaka su.

    Saboda darajarka zan yi maka hadaya, * Yahweh, zan yabi sunanka mafificin kyau.

Gama ya tserad da ni daga dukan ma}iyana, * idanuna sun ga yadda ya yi nasara da magabtana.

Zabura ta 55

Ya Allah, ka ji addu’ata, * kada ka zama kurma ga ro}ona.

Ka karkato gare ni, ka amsa mani, * ka sauko inda ni ke }ara.

    Na gigice da muryar abokin gaba, * da hararar miyagu,

    domin suna tila mani zage, * suna ci mani fuska.

         Zuciyata tana ra]a]i a cikina, * razanar mutuwa tana girgiza ni.

         Tsoro da fargaba sun afka mani, * sai makyarkyata nike yi.

              Sai na ce, “Wa zai ba ni fukafukai kamar na kuruciya, * don in tashi fir in huta.

              Da sai in tafi nesa, * in sauka a kungarmin daji.

              Zan hanzarta zuwa mafakata, * daga iska mai }arfi da hadari.”

                   Ya Ubangiji, ka hallaka halshensu mai rinto, * domin na ga tashin hankali da hargitsi a cikin birnin.

                   Dare da rana suna kewaye da shi. * A kan garunsa akwai }eta da fitina.

                   Daga tsakkiyarsa ayyukan mugunta suna fitowa, * daga tsakkiyarsa ba su dena zuwa ba, * daga dandalinsa zalunci da zam~a suna watsuwa.

                       Ba magabci ba ne * wanda ya yi mani cin fuskar da nike jurewa.

                       Ba ma}iyi ba ne ya ~ata mani suna, * balle in ~uya daga gare shi.

                            Amma kai ne, aminina, * abokina da na amince da shi.

                            Mun saba yin shirin zaune tare * a cikin Gidan Allah, * inda muke cudanya da taron jama’a.

                       Bari mutuwa ta afko masu, * bari su gangara Shawol da ransu,

                       domin magana mai dafi na fitowa * daga ma}ogwaronsu da }irjinsu.

                   Amma na yi kira ga Allah, * Yahweh kuwa ya cece ni.

                   Da yamma, da safe, da rana tsaka * ina kai }ara da nishi.

              Mafanshi kuwa ya ji muryata, * yana biyan ku]in raina.

              Ya matso kusa da ni * lokacin da masu yawa suke gâba da ni.

              Allah ya ji ni, * Mai Zamanu ya ba ni amsa, * domin ba canzawa a gare shi.

         Duk da haka, basu da tsoron Allah. * Wancan mutun ya sa hannu kan amininsa, * ya sa~a yarjejeniyarsa.

         Maganarsa ta fi kitse taushi, * amma zuciyarsa tana cike da }iyayya.

         Kalmominsa sun fi mai sul~i, * amma a gaskiya sun fi takobi kaifi.

    Yahweh Ma]aukaki ne Mai Arzutaka, * Mai Ba ka wanda ke tallafa maka.

    Har abada ba zai bar * mai gaskiya ya yi tuntu~e ba.

Amma kai, ya Allah, za ka kai su, * Rami mai Ca~i.

Kada masu gumaki da tsafi * su rayu rabin kwanakinsu. * Amma ni, na dogara gare ka.

Zabura ta 56

Ka ji tausayina, ya Allah, * gama mutane suna musguna mani!

Wuni zubut * suna tozarta ni da mu}amu}ansu.

Masu yankena suna wahalda ni wuni zubut, * mutane barkatai ne ke ya}i da ni.

    Ya Ma]aukaki, in na firgita, * ina dogara gare ka.

Da Allah nike ta}amai, kai mai yanke! * Na dogara ga Allah.

Bana jin tsoro. * Me mutun zai iya yi mani?

    Wuni zubut masu yankena suna harzuka ni, * suna mugun shiri a kaina kullun.

    Suna shawara da juna da mugun nufi a asirce, * dubi yadda masu kushena ke kallo, * kamar tarkon }afa suke neman raina.

        Ka cece mu daga }etarsu, * cikin hushinka ka tsawata wa al’ummai, ya Allah!

        Ka rubuta makokina kai da kanka, * ka lissafta hawayena a kan takardarka, * da gajiyata a ckikin kundinka.

    Da magabtana sun juya, * sun yi dabur-dabur da na yi kira,

    sannan nike sani, * lalle Allah yana goyon bayana.

Da Allah ne nike ta}ama, kai mai yanke! * Da Yahweh nike ta}ama, kai mai yanke!

Na dogara ga Allah. * Bana jin tsoro. * Menene mutun zai iya yi mani?

    Hakika, ya Allah Ma]aukaki, * zan biya wa’adodina * tare da yabbanka.

Sai ka cece ni daga Mutuwa, * ka hana }afafuna zuwa cikin Kora,

domin in yi tafiya a gaban Allah * a cikin aljannar rayuwa.

Zabura ta 57

Ka tausaya mani, ya Allah, ka tausaya mani, * domin a gare ka nike fakewa.

A innuwar fukafukanka nike fakewa, * har bala’in nan ya wuce.

    Ina kira ga Allah Ma]aukaki, * ga Allah, Sarkin Sakayya.

    Zai aiko daga sama a cece ni, * daga cin mutuncin masu tozarta ni.

    Allah zai aiko * da alherinsa da amincinsa.

        Ina kwance a tsakkiyar zakoki, * ga shi, suna marmarin naman ’yan’adan.

        Ha}oransu masu ne da kibau, * harsunansu takubba ne masu shegen kaifi.

            Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ]aukakarka ta rufe dukan duniya.

        Sun ha}a wa }afafuna tarko, * da igiya don su zarge wuyana.

        Sun gina rami don in fâda ciki da kâ, * da ma su yi kundumbala a ciki.

    Na shirya zuciyata, ya Allah, * na shirya zuciyata, * zan yi wa}a in yabe ka.

    Ki farka, zuciyata! * Ku farka, molona da garayata! * Sai in farkad da asuba!

Zan gode maka a cikin jama’a, ya Ubangiji, * zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Mai Duka.

Domin alherinka ya kere sammai, * amincinka kuma ya zarce sararin sama.

Girmanka ya wuce sammai, ya Allah, * ]aukakarka ta rufe dukan duniya.

Zabura ta 58

Ya ku mashawarta, ku alkalai, ku zartad da hukuncin adalci, * ku yi mulkin ’yan’adan da gaskiya.

Amma ba haka ba, kuna aikata }eta a zukatanku, * da zalunci kuke yanke shari’a ta son ranku.

    Miyagu abin }yama ne tun daga ]aukar cikinsu, * tun daga haifuwa ma}aryata ke bau]ewa.

    Dafinsu kamar na maciji ne, * suna yin kama da kububuwa mai tosasshen kunne,

    wadda ba ta jin muryar gardawa, * ko ta gwanayen tsibbu.

        Ya Allah, ka zub da ha}oransu daga bakunansu, * Yahweh, ka kakkarya fi}o}in kuyakuyan zakoki.

        Bari su zube, kamar ruwa mai gudu, * su ]ana kibansu ba tare da }arfin harbi ba.

    Kamar wanda ciwon }anjamau ya takure, bari ya }aura * kamar ~arin mace, kada su ga hasken rana.

    Kafin su yi la’akari da hadarinka, * bari zafin haushinka ya watsad da su.

Mai adalci zai yi murna in ya ga nasararsa, * zai wanke }afafunsa daga jinin miyagu.

Mutane za su ce, “Zama mai adalci abin kirki ne. * Hakika akwai Allah mai shara’anta duniya!”

Zabura ta 59

Ka cece ni daga abokan gabata, ya Allah, * a game da masu tasar mani ka zama ganuwata!

Ka cece ni daga masu aikata mugunta, * daga masu gumaka ka fanshe ni.

    Dubi yadda suke fakon raina, * masu iko suna yi mani ma}ar}ashiya.

    Ba don laifina ba, * ba don zunubina ba, Yahweh,

    ba don kurena ba, * sun sha mani da-ga.

Tashi, ka bi ni, * ka gani da kanka,

Yahweh, Allah mai runduna, * Allah na Isra’ila.

Farka domin ka hori dukan al’ummai, * kada ka ji tausayin miyagun masu ha’inci.

    Sukan dakata sai maraice, * kâna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.

    Duba daga bakunansu da le~unansu suna aman takubba. * Suna cewa, “Wanene zai saurare mu?”

        Amma, Yahweh, za ka yi masu dariya, * kana mai da dukan al’ummai abin wasa.

            Allahna mafakata ne, * hakika ina samun kariya.

            Allah, shi ne ganuwata, * hakika Allah ne katangata.

            Allah zai riga ni zuwa, * zai sa in yi wa magabtana dariya.

                 Ya Allah, ka kashe su, * kada mutanena su razana.

                 Ka runtume su daga mafakarka, * ka yâ da su }asa, * ya Ubangiji Shugabanmu.

            Bari a kama su ta zunubin bakinsu * da gulmar le~unansu.

            Saboda izgilancinsu, zage-zage da }arairayinsu, * bari a shafe su.

            Ka hallaka su da hushinka, * ka hallaka, ka shafe su,

        domin su sani Allah ne * yake mulki daga }asar Yakubu * har zuwa bangon duniya.

    Sukan dakata sai maraice, * kâna su yi haushi kamar karnuka, * suna zaga birnin.

    Da haushi sukan nemi rabonsu, * in ba su }oshi ba, sai su ci gaba.

Zan yi wa}ar ikonka, * kowace safiya zan yabi }arfinka,

    domin kâ zama ganuwata, * da katangata lokacin hari.

    Allah mafakata ne, * hakika yana tsare ni.

Allah shi ne ganuwata, * Allah ne katangata.

Zabura ta 60

Ya Allah, ka ji hushi da mu, ka guje mu. * Kâ yi haushi, ka juya mana baya.

    Kâ girgiza }asar, ta kuwa rugurguje.* Raunanniya daga targa]enta, * ta gigice sosai.

        Kâ sa jama’arka su shanye }o}on, * kâ sa mun sha abinshan inabi da ya bugar da mu.

            Ka ba masu tsoronka tuta, * inda za su iya gâba da masu baka.

            Domin ka ku~utad da }aunatattunka, * da hannun damanka sa mu yi rinjaye, mu ci nasara.

                 Allah ya yi magana daga tsattsarkan gidansa, ya ce: * “Ku ji, zan raba Shekem, * in auna kwarin Sukkot.

                 Gileyad nawa ne, har da Manassa, * Ifraimu hulata ne, * Yahuda kuma sandata ce ta sarauta.

                 Mowab bangajin wankina ne, * a kan Edom zan taka da takalmina, * a kan Filistiya zan yi ihun nasara.

            Wa zai kai ni Birnin Dutse? * Wa zai ba ni gadon Edom?

        Amma kai, ya Allah, za ka yi hushi da mu? * ba za ka }ara fita da sojojinmu ba?

    Ka ba mu ’yanci daga abokan gaba, * tun da yake taimakon mutane banza ne.

Da ikon Allah za mu yi nasara, * shi kansa ne zai tattake magabtanmu.

Zabura ta 61

Ya Allah, ka ji kukana, * ka saurari addu’ata.

    Daga bakin {al}ashin {asa * na yi kiranka, * lokacin da zuciyata ta karaya.

    Ka jawo ni daga bakin Ramin * zuwa Dogon Dutse.

    I, zama mafakata, * hasumiyar tsaro daga Magabcina.

        Bari in zauna a madauwamiyar alfarwarka, * in sami tsira a innuwar fukafukanka.

    Ya Allah, ka ji wa’adonina, * ka biya begen mai tsoron sunanka.

    Ka }ara shekaru ga shekarun sarki, * shekarunsa su zama tsararraki barkatai.

    Bari ya zauna kan kursiyinsa a gaban Allah har abada, * ka sa alheri da aminci su kiyaye shi.

Sannan zan yi wa}ar sunanka har abada, * ina cika wa’adodina kowace rana.

Zabura ta 62

Allah mai alloli, * shi ka]ai ne mafakata. * Ya raina, daga gare shi ne cetona zai zo.

Shi ka]ai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan fâda a Tarun ba.

    Don me za ku dinga maganar banza, * kuna ta yin tsegumi a kan mutun?

    Dukanku kama da bango mai son fâ]i, * ko dangar da ta kishingi]a.

        Yau]ara ce kawai suka runguma, * suna jin da]in }arairayi.

        I, da baka suna sa albarka, * amma a zuci suna yi maka la’ana.

            Allah ka]ai ne mafakata,* ya raina, daga gareshi ne nike samun bege.

                Shi ka]ai ne dutsen nasarata, * mafakata, ba zan yi tuntu~e ba.

                Allah Ma]aukaki ne nasarata, * Mai [aukaka shi ne mafakata, * Allah shi ne masterata.

            Ku dogara gare shi, Mai Iko ne kullun, * ku bu]e zukatanku gare shi, * domin Allah ne matseranmu.

        Talakawa kamkar haya}i suke, * manyan mutane kuma kamar tururi.

        A kan sikelai ba su yi nauyin ganyaye ba, * dukansu biyu kuma ba su kai nauyin iska ba.

    Kada ku cika rungumar zulunci, * kada ku mai da dukiya gunkinku.

    In Allah ya yi magana, * ku saurara.

Abu ]aya ne Allah ya fa]i, * biyu ka]ai ne na ji:

“Iko na Allah ne, * a gare ka kuma, ya Ubangiji, }auna take.

Domin kana saka wa kowane mutun * gwargwadon aikinsa.

Zabura ta 63

Ya Allah, Allahna, * kai ne nike marmari.

    Raina yana jin }ishinka, * jikina na begenka,

        fiye da yadda busasshiyar }asa * ke marmarin ruwa.

            A tsattsarkan mabautarka bari in zuba ido gare ka, * ina kallon ikonka da ]aukakarka.

        Domin }aunarka tana da da]i * fiye da rayuwata da le~unana da ke yabonka.

    A madauwamiyar rayuwata ka sa in yabe ka, * a samaniyarka kuma in ]aga hannuwana zuwa gare ka.

        A can zan yi biki, in }oshi * da madara da man shanu.

        Le~unana za su yi sowa ta murna, * bakina kuma zai raira yabonka.

    A kan gadona ina tunawa da kai, * dukan dare ina tunaninka.

        Ka zama Mataimakina! * Bari in ~uya a cikin innuwar fukafukanka.

            Bari in manne maka, * hannunka na dama kuwa ya ]aga ni.

        Amma masu neman kisana, * bari su tafi can }urewar {al}ashin {asa.

    Bari su gamu da kaifin takobinsa, * duk su zama kalacin kyarketai.

Sarki zai yi murna da Allah. * Duk wanda ya rantse da shi zai gama lafiya, * amma za a toshe bakin ma}aryata.

Zabura ta 64

Ka ji muryata, ya Allah, da nike ro}o.

Ka kiyaye raina daga taron ma}iya, * ka ~oye ni daga miyagun mashawarta, * daga rukunin ’yan iska,

    masu wasa halshensu kamar takobi, * suna bârâ da maganarsu mai dafi kamar kibiya,

    don su yi wa mara laifi kwanton ~auna, * su hallaka shi kwatsam, ba tsoron Allah.

        Suna shirya masa magani mai dafi, * suna kakkafa masa tarkuna,

            suna cewa: “Wanene ke ganinmu? * Wa zai binciki daidaitaccen sharrinmu?”

            Amma Mai Bincike zai binciki * can cikin cikin mutun * har cikin birnin zuciya.

        [aukaka ga Allah Mai Kibau! * Ka ninka raunukansu!

    Ma]aukaki zai sa matsegunta su yi tuntu~e, * dukan masu girman kai za su }as}anta.

    Kowane mutun zai ji tsoro, * ya bayyana aikin Allah, * ya ri}a tunanin aikinsa.

Bari mai adalci ya yi murna da Yahweh, * ya nemi tsira a gunsa! * Bari dukan masu zuciyar kirki su more!

Zabura ta 65

Yabo gare ka a mafakarka ta samaniya, * da can Sihiyona, ya Allah.

    A gun ka za a cika wa’adodi, * domin ka kan ji addu’o’i.

        A gare ka duk bil’adama * zai kai miyagun ayyukansa.

            Ayyukanmu na tawaye sun yi yawa, * ka gafarta mana!

            Mai albarka ne wanda ka za~a zuwa kusa da kai, * don ya zauna a majalisarka.

        Bari mu gamsu da kyan gidanka, * da tsarkin Haikalinka.

    Lokacin shari’a ka nuna mana al’ajibanka, * ya Allahnmu mai nasara!

        Kâ shimfi]a dukan kusurwoyin duniya, * da na nesan teku.

            Kâ kakkafa duwatsu da ikonka, * sun yi ]amara da }arfinka.

            Kâ kwantada da haukan teku, * da haukan ra}uman ruwansa, * da kuma tarzomar mutane.

        Mazaunan bangon duniya sun ji tsoro * saboda al’ajibanka.

    Ka sa gamzaki da tauraron dare * su yi sowar murna.

    Ka ziyarci }asa, * ka sa ta tsalle don murna, * ka sa ta yi albarku da ruwan samanka.

        Ka cika magudadar sama da ruwa, * ka wadaci }asa da hatsi, * gama kâ kafa ta don wannan.

            Ka malalo ruwa a kwarin gona, * ka ji}a kunyoyinta.

            Ka tausasa ta da ruwa mai yawa, * ka albarkaci hatsinta!

        Ka albarkaci tuddai da ruwan samanka, * makiyayunka sun ba da mai.

    Dajin Allah ya tsatso da mai, * ka lullu~i tuddai da murna.

    Ka sa kwaruruwa su cika da dabbobi * }asar kwari kuwa alkama.

Bari su ta da murya, * su yi sowar farinciki.

Zabura ta 66

Yi sowar farinciki ga Allah, ke duniya duka, * yi wa}ar ]aukaka sunansa, * yi shelar ]aukaka yabonsa.

A ce, “Ya Allah, * mai ban tsoro ne kai ta ayyukanka!

    Saboda girman ikonka, * magabtanka suna sunkuyawa don tsoro a gabanka.

    Dukan duniya tana bauta maka, * tana yi maka wa}a, wa}ar sunanka.

        Ku zo, ku ga ayyukan Allah, * mai firgita ’yan’adan ta ayyukansa.

            Ya mai da teku busasshiyar }asa, * suka taka }asar kogin suka haye. * Ku zo, mu yi farinciki a cikinsa!

        Yana sarauta daga madauwamiyar mafakarsa, * idanunsa na kallon al’ummai, * don kada ’yan tawaye su tayar masa.

    Ku yabi Allahnmu, ya ku mutane, * da murya mai }arfi ku yabe shi!

    Wanda ya lissafa mu a cikin rayayyu, * bai ma sa }afafuna cikin Lema ba.

        Amma kâ gwada mu, ya Allah, * kâ jarraba mu kamar yadda ake tace azurfa.

        Kâ kai mu cikin hamada, * kâ sa marurai a gindinmu.

        Kâ sa ciwo ya hau kanmu, * mun ratsa wuta da ruwa, * bayan ka fishe mu daga wurin wadata.

    Zan shiga gidanka da }onannun hadayuna, * in cika wa’adodina,

    wa]anda na fa]a da le~unana, * bakina ya furta a lokacin wahala.

    Zan mi}a maka dabbobi masu ki~a don a }ona, * da }amshin raguna da aka }ona. * Zan shirya bajimai duk da awaki.

        Ku zo, ku ji, dukanku masu tsoron Allah, * zan gaya maku abin da ya yi mani.

        Da bakina na yi kuka gare shi, * muryaoyin wa}a kuma suna kan halshena.

    Da na tabbata mugunta a zuciyata, * da Ubangiji bai ji ni ba.

    Amma Allah ya ji ni, * ya saurari muryar addu’ata.

Albarka ga Allah! * domin bai }i addu’ata ba, * zan sake fa]in alherinsa har sau ]ari.

Zabura ta 67

Allah ya ji tausayinmu, ya yi mana albarka, * ya zo mana da hasken fuskarsa.

In an san sarautarka a duniya, * da nasararka a cikin dukan al’ummai,

    mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.

        Al’ummai za su yi farinciki da sowar murna, * domin kai ne sarki.

        Za ka kai al’ummai Sararin, * jama’a kuma cikin {asar.

    Mutane za su yabe ka, ya Allah, * mutane za su yabe ka, dukansu.

Bari }asa ta ba da amfaninta, * Allah, Allahnmu, ya yi mana albarka.

Allah ya yi mana albarka, * dukan }asashe su ji tsoronsa * har bangon duniya.

Zabura ta 68

In Allah ya tashi, * magabtansa sukan watsu, * ma}iyansa sukan guje shi.

Kamar yadda haya}i ke bin iska, su ~ace, * kamar yadda dan}o ke narkewa a gaban wuta.

A gaban Allah * miyagu sukan san inda dare ya yi masu.

    Amma masu gaskiya za su yi murna, * su sami tagomashi a gaban Allah, * za su yi wa}a mai farinciki.

        Ku yi wa}a, ku alloli, * ku raira yabo, ku sammansa, * ku share hanya ga Mai Hawan Giza-gizai.

    Ku ji yi murna da Yahweh, * ku yi murna a gabansa!

Allah daga tsattsarkan mazauninsa * shi ne uban marayu da mai kare gwauraye.

Allah wanda ya ba mai ka]aici gida, * shi ya ’yanto ’yan sar}a tare da wa}a

Amma masu taurin kai, * an binne su a Hamada.

    Ya Allah, sa’ad da ka fita * gaban mutanenka, * da ka }etare hamada,

    sai }asa ta raunana, * sammai kuma suka saukad da ruwa

        da ganin Allah, * Mai Sinina,

        da ganin Allah, * Allah na Isra’ila.

            Ya Allah, ka aiko da ruwan samanka mai yawa, * }asarka da sarautarka, ka tabbatad da su.

            Ka wadaci jama’arka da ke zaune a kai, * da ruwan samanka ka arzuta mazaunanta, ya Allah.

                 Allah ya aike da magana, * mai faranta rundunar taurari.

                 Sarakunan rundunarsu su sauko da ruwa, * wurin kiwon kasar ya sami rabonsa na albarka.

                 Bari su zube * a tsakar garken tumaki

            An dalaye fukafukan kuruciya da azurfa, * da gashinta kuma da zinariya.

            Sa’ad da Shaddai ya inuwantad da sarakuna, * dusar }an}ara ta sauka a kan Zalmona.

        Ya babban dutse, Dutsen Bashan, * ya dutse mai yawan tulluwa, Dutsen Bashan,

        don me kake kallo da hassada, * ya dutse mai yawan tulluwa,

        dutsen da Allah ya za~a don mazauninsa, * inda Yahweh zai zauna har abada.

    Karusan Allah dubu ishirin ne, * maharban Ubangiji dubbai ne, * wanda ya kafa Sinina mabautarsa.

    Kâ hau sama, * kâ jawo kamammu.

    Kâ kar~i kyautai daga hannuwansu, * amma Yahweh Allah ya binne masu taurin kai.

    Albarka ga Ubangiji yau da kullun, * Allah kansa, Macecinmu, ya cire mana nauyin kayanmu.

    Allah kansa shi ne Allah na cetona, * tun da Ubangiji Yahweh ya sa mu tsira daga mutuwa.

    I, Allah ya buge kan magabtansa, * ya farfashe kwakwalunsu, * sa’ad da ya fito daga sammansa.

        Allah ya ce, “Na taushe Macijin, * na kwantad da Teku Mai zurfi.”

        Haka, }afarka ta ragargaji ga~o~insu, * harsunan karnukanka kuma sun sami rabo gun magabtanka.

            Ku ga faratin Allah, * faratin Allahna, * Sarkina daga mabautarsa.

            Mawa}a suna kan gaba, * mabusa a baya, * a tsakiya ’yan mata suna ki]a.

                 A taruwar jama’a ku yabi Allah, * Yahweh kuwa a taron Isra’ila.

            Ga Biliyaminu }arami, yana yi masu jagora, * sarakunan Yahuda kuma a jeri biyu,

            sarakunan Zabaluna, * da sarakunan Naftali.

        Ya Allah, ka aiko mana da }arfinka, * }arfi, ya Allah, abin da ka gina domin mu.

        Haikalinka, ya Ma]aukaki, a {udus yake, * sarakuna za su kawo maka kyautai.

    Ka tsawata wa dabbar lema, * taron bajimai da maru}ansu.

    wa]anda ke tattaka mutane saboda sha’awar azurfa, * suna warwatsa mutane don marmarin ya}i,

Bari attajiran Masar su kawo shu]in zane, * Habasha ta rugo ta kawo kayanta ga Allah.

Ku sarakunan duniya, ku yi wa}a, * ku alloli, ku raira yabbai ga Ubangiji.

    Ku dubi Mai Hawa sammansa, * sammai na tun fil’azal.

    Ku saurara, yana aiko muryarsa, * murya mai girma!

Ku girmama Allah, * Ma]aukakin Isra’ila.

[aukakarsa da ikonsa * sun fi }arfin sama. * Allah mai bantsoro ne a tsattsarkan mabautarsa.

Hakika shi Allah ne na Isra’ila, * wanda ke ba da nasara da iko. * Ku mutane, ku yabi Allah!

Zabura ta 69

Ka cece ni, Allah, * domin ruwa ya kai wuyana.

    Na nutse cikin Ta~o mai zurfi, * inda ba damar tsayawa.

        Na shiga zuzzurfan ruwa, * inda igiyoyin ruwa suke cina.

    Na gaji da kuka, * ma}ogwarona ya bushe.

Idanuna sun fara dushewa, * sa’ad da nike dako, ya Allah.

    Magabtana masu makirci sun yi yawa, * fiye da gashin kaina.

    Fiye da gashin kaina * mayaudarana suka zarce da yawa.

    Abin da ban sata ba, * dole ne in mayas da shi?

        Ya Allah, ka san barancina, * laifofina ma ba a ~oye suke gare ka ba.

            Kada masu sa zuciya gare ka su sha kunya * saboda ni, ya Ubangiji Yahweh Mai Runduna.

                 Kada masu nemanka su kunyata * saboda ni, ya Allah na Isra’ila.

                 Saboda kai ne na sha zagi, * cin mutunci ya rufe fuskata.

            Na zama ba}o ga ’yan’uwana, * bare kuma ga ’ya’yan da muke uwa ]aya.

        Gama kishi domin gidanka ya cinye ni, * zage-zagen masu zaginka sun taru a kaina.

    Ina tunanin dukan ~acin raina a cikin azumina, * wulakanci kuma ya zama rabona.

    Na mai da tsummoki tufafina, * na zame masu abin dariya.

    Har ’yan bikin da mashaya * suna wallafa wa}o}in shegantaka a kaina.

        Amma ni kam, addu’ata gare ka take, Yahweh, * ya Allah, ka nuna mani alherinka yanzu.

        Da }aunarka mai girma * ka amsa mani * da amintaccen taimakonka.

            Ka cece ni daga Ca~in, * kada in nutse.

            Bari a ku~utad da ni daga Ma}iyi, * daga zurfafan ruwaye ma.

            Kada juyewar ruwan teku ta rufe ni, * ko zurfinsa ya ha]iye ni, * ko Ramin ya rufe bakinsa a kaina.

                 Ka amsa mani, Yahweh, * domin }aunarka mai girma ce.

                      Bisa ga yawan rahamarka, * ka juyo fuskarka gare ni.

                           Kada ka juya * wa bawanka baya.

                      Ka amsa mani da sauri, * don wahalar da ke damuna,

                 Ka kusato ni, ya Allah, ka cece ni, * ka fanshe ni daga Mazaunin Magabcina.

            Ka san wulakancin da ake yi mani, * kunyata da }as}ancina a gabanka suke.

            Wulakanci ya lalata kayan cikina, * ciwo ya dagargaji zuciyata.

        Na nemi mai jin tausayi, amma babu, * da mai sanyaya zuciya, amma ban sami wani ba.

        Sun sa dafi a abincina, * don }ishinruwana sun mi}a mani ruwan tsami.

    Bari teburin abincin da ke gabansu ya zama tarko gare su, * abokan tarayyarsu kuma su zaman masu taru.

    Idanunsu su dushe don kada su gani, * cinyansu kuma su yi ta rawa kullun.

    Ka jibga masu haushinka, * bari tsananin hushinka ya cim masu.

        A sansaninsu kada wani ya ragu, * a tantunansu kada wani ya zauna.

            Domin wanda ka buge sun tsananta masa, * azabar wanda ka raunata kuwa suna ta tsegumi a kai.

            Ka hukunta su da sharri bisa sharri, * kada su shiga aljannarka.

        Bari a share sunayensu daga littafin rai, * kada a sa a cikin adalai.

    Amma ni gajiyayye ne, cikin azaba, * taimakon Allah ya tallafe ni,

    don in yabi sunan Allah da wa}a, * in ]aukaka shi da godiya.

    Wannan zai da]a]a ran Yahweh fiye da takarkari, * ko fiye da bajimin sa mai }ahoni da kofatai.

Ku duba, ku gajiyayyu, * bari masu neman Allah su yi farinciki, * zukatansu su tofu!

    Domin Allah yana sauraren mabukata, * Yahweh baya ya da wa]anda ke nasa.

        Bari sama da }asa su yabe shi, * tekuna da dukan abin da ke motsi a cikinsu.

    Hakika, Allah zai ceci Sihiyona, * zai sake ginin garuruwan Yahuda, * wa]anda aka kora za su koma su zauna ciki.

Jikokin bayinsa za su gaji birnin, * za su zauna ciki, su mallake shi.

Zabura ta 70

Ya Allah, ka cece ni, * Yahweh, ka yi hanzari ka taimake ni!

    Bari masu neman raina * su kunyata, su ru]e.

        Bari masu sha’awar lalacewata * }as}anci ya zama nasu.

            {ai}ai ya koma wa masu tseguman banza, * wa]anda ke ce mani, “Ga shegen nan, ga shegen nan!”

            Bari dukan masu nemanka * su yi farinciki, su yi murna da kai!

        Bari dukan masu son cetonka * su ri}a cewa: “Allahu akbar!”

    Amma ni, da ke gajiyayye da mabukaci, * ya Allah, ka hanzarto zuwa gare ni.

Kai ne mataimakina da macecina, * Yahweh, kada ka yi jinkiri.

Zabura ta 71

Yahweh, a gare ka nike dogara, * kada in kunyata, ya Madauwami!

    Da amincinka ka ku~utad da ni, ka fanshe ni, * ka kasa kunne gare ni, ka cece ni.

        Dutsen Taimako, ka zama nawa! * Kâ alkawalta zuwa guna a kowane lokaci.

        Ka cece ni yanzu! * gama kai ne dutsena da mafakata.

    Ya Allah, ka ’yanta ni daga hannun mugu, * daga kagen azzalumi da ]an fashi.

        Gama kai ne begena, ya Ubangiji, * Yahweh, madogarata ne tun a cikin kuruciyata.

        Kai ne ka tallafa mani tun daga mahaifa, * daga cikin uwata kai ka lura da ni, * zan dinga yabonka.

            Na zama zakaran gwajin dafi ga mahar~a, * amma kai ne }a}}arfar mafakata.

        Bakina ya cika da yabonka, * da na al’ajibanka yini zubut.

        Kada ka watsad da ni da tsufana, * in }arfina ya gaza, kada ka yashe ni.

            Magabtana suna hararata, * masu neman raina suna }ulla shawara da juna,

            suna cewa: “Allah ya yashe shi, * mu fafare shi, mu kama shi, * domin babu mai ceto.”

                 Ya Allahna, kada ka yi nesa da ni, * ya Allahna, ka hanzarta taimakona.

            Bari matseguntana * su sha kunya tuli.

            Masu neman lalacewata * su kwashi muzanci da kunya.

                 Amma ni a kullun zan sa zuciya gare ka, * in dinga yabonka ba fashi.

                 Bakina zai lissafta ayyukanka masu aminci, * wuni zubut kuma dukan aikinka na ceto, * duk da ba zan iya lissafa su ba.

            Zan shiga babban gidanka, ya Ubangiji, * Yahweh, amincinka ka]ai zan yi shela.

                 Ya Allah, kâ hore ni tun daga }uruciyata, * har yanzu ma ina ba da labarin al’ajibanka.

                 Har cikin tsufana da furfura, * kada ka yashe ni, ya Allah,

            sai na ba jama’a labarin ikonka, * ga duk wanda zai shiga }aton gidanka.

            Ya Allah, amincinka ya kai har sama, * domin ka aikata manyan abubuwa. * ya Allah, wa ke kama da kai?

            Ko da yake ka nuna mani * wahalu masu yawa da husumai da cuta,

            za ka sake raya ni, * daga zurfafan {al}ashin {asa kuma * za ka sake ta da ni.

        Ka ji da]in babban baikona na shanu, * ka ma lullu~e ni da tausayinka.

    Da babbar murya zan yabe ka da garaya, * in yabi amincinka, ya Allah.

        Zan yabe ka da molo, * ya Mai Tsarkin nan na Isra’ila.

        Le~unana za su yi wa}a, * i, zan yabe ka, * duk da ruhuna da ka fanso.

    Da babbar murya halshena zai lissafta * ayyukanka masu aminci yini zubut.

Ka sa su sha kunya, * duk masu marmarin lalacewata, * ka sa su ru]e.

Zabura ta 72

Ya Allah, ka ba sarki hikimar yanke hukuncinka, * ]an sarki kuma ya san gaskiya,

    don ya hukunta mutanenka da gaskiya, * zaluntattu kuma da adalci.

        Bari duwasu su kawo wa mutanenka salama, * tuddai kuma adalci.

    Bari ya kare wa]anda aka zalunta * ya ceci ’ya’yan mabukata, * ya dami azzalumi.

Ka sa ya girmama ka muddin da]ewar rana, * har wanzuwar wata, * zuwa zamanin zamanu.

    Bari ya sauko kamar ruwan sama a kan ciyawa, * tamkar yayyafi a kan busasshiyar }asa.

    Bari adali ya bun}asa a zamaninsa, * salama kuma ta kasance muddun wata na wanzuwa.

        Bari ya yi mulki daga teku zuwa teku, * daga Kogin Yufiretis har zuwa }arshen duniya.

        Bari kabilun hamada su dur}usa masa, * har sai magabtansa sun ci tur~aya.

            Sarakunan Tarshishi da na tsibirai * su kakkawo masa haraji.

                 Sarakunan Shiba da na Saba * su ba shi kyautayi.

                      Dukan sarakuna su dur}usa a gabansa, * dukan al’ummai su bauta masa!

                      In ya ceci mabukacin da ke kuka, * da zaluntaccen da ba shi da mataimaki,

                 in ya ji tausayin matalauci mabukaci, * har ya ceci rayukan yasassu,

            in ya ceci rayukansu daga zalunci, * jininsu kuwa yana da daraja a gare shi,

        daga nan ransa ya da]e! * ya sami kyautar zinariya daga Shiba,

        a dinga yi masa add’ua ba fâshi, * ana ro}a masa albarku kullun.

    Bari mayafin alkama ya rufe }asar, * da haki mai yawa a kan tuddai.

    ’Ya’yansa su yi fure kamar icen Labanan, * suna yin toho kamar ciyawa.

Bari jikokinsa su ]ade har abada, * suna haifuwar ’ya’ya har ran da rana ta }are.

    Bari jikokinsa su sami albarka saboda shi, * dukan al’ummai su yi murna ta wurinsa.

    Albarka ga Allah Yahweh! * Allah na Isra’ila, * mai aikata al’ajibai shi ka]ai.

Albarka ga sunansa mai ]aukaka har abada! * Bari duniya duka ta cika da ]aukakarsa.

Amin, Amin.


Zabura ta 73

Ya Isra’ila, lalle Allah yana kyautata * wa masu tsattsarkar zuciya.

    Amma sawayena sun kusa yin tuntu~e, * }afafuna sun kusa gocewa,

    sa’ad da na ji }yashin masu fankama, * har na ga }wanjin dukiyar miyagu.

        Ba su da fa]i-tashi, * jikinsu yana da }arfi da sul~i.

        Ba su yin aikin bayi, * ba a tsananta masu kamar sauran ’yan’adan.

            Don haka alfarma ta zamam masu sar}ar wuya, * tufafin zalunci ya rufe su.

            Idanunsu na yin she}i fiye da madara, * miyagun dabarun zukatansu ba su da iyaka.

                 Suna zagi da magana “Mai Kawo Mugunta”, * “Azzalumi” ne suke kira Ma]aukaki.

                 Bakinsu yana la’anta sama, * halshensu bai }yale abubuwan {al}ashin {asa ba.

            Don haka sun }agara su }osad da kansu, * har suna shanye ruwayen teku.

            Suna cewa, “Ta yaya Allah zai sani? * ko Ma]aukaki yana da ilimi ne?”

        Haka miyagu suke, * ba su damu da Madauwami ba, * sai dukiyarsu kawai suke }arawa.

    Ashe, a banza nike kiyaye zuciyata da tsabta, * ina kuwa wanke hannuwana daga laifi,

    domin ana tsananta mani wuni zubut, * ana horona kowace safiya.

        Da na ce, “Haka zan yi magana,” * da na yi wa jama’ar ’ya’yanka ha’inci.

        Da na yi }o}arin gane wannan, * zaluncinsa kawai nike tunani,

        sai da na shiga tsattsarkan mabautar Allah, * kâna na gane }arshensu.

    Hakika za ka sa su }aura zuwa Gidan Hallaka, * kana sa su fâ]a Kufai.

    Nan da nan za su fâ]a Hallaka, * za a share su da Falgaba!

    Tamkar mafarkin an farka, ya Ubangiji, * za ka mance da su can Garin Aljanu.

        Amma in zuciyata ta ~aci, * hankalina ya gigice,

            sai in zama wawa mara fahinta, * dabba kurum a wurinka.

            Amma ni kullun ina wurinka, * ka ri}e hannuna na dama.

        Ka bi da ni zuwa mashawartarka, * ka ]auke ni da ]aukaka zuwa gunka.

    Me zan rasa a sama * tare da kai? * bana bukatar komi a duniya.

    Jikina da zuciyata sun gaza, ya Dutse, * amma zuciyata da jikina, ya Allah, za su dauwama har abada.

    Sai dai duk wanda ya nisance ka zai hallaka, * ka hallaka dukan masu yin zina ta guje maka.

Ni kam, kusantar Allah na sa ni murna, * na dogara ga Ubangiji Yahweh, * ina shelar dukan ayyukanka.

Zabura ta 74

Don me, ya Allah, kake ri}a yin hushi? * Don me hancinka kuma ke fid da haya}i a kan tumakin makiyayarka?

Ka tuna da garken da ka tanada tun dâ, * ka fanshi gâdonka da kulkinka, * Dutsen Sihiyona inda kake zaune.

Ka ]aga jama’arka daga da~en kufai, * magabci ya lalata komi daga tsattsarkan mabautarka.

    Magabtanka sun yi ruri a tsakar taron jama’arka, * sun kafa ]aruruwan alamu.

        Sun }one }ofar bisa, * suka sassare adon }ofofi da gatura.

            Sun sassaka dukan }yamare, * sun bubbuge su da digogi da gudumu.

        Sun sa wa tsattsarkan mabautarka wuta, * sun wulakanta mazaunin sunanka.

    A zukatansu sun ce, * “A }one dukan ’ya’yansu, * da dukan ]akunan taron Allah a }asar.”

        Ba wasu alamu daga wajenka dominmu, * ba sauran wani annabi yanzu, * ba mai bayyana wahayinka da muka samu.

            Ya Allah, har yaushe magabci zai sa~e ka? * ma}iyi kuma zai wulakanci sunanka, ya Jarumi?

            Me ya sa ka janye hannun hagunka? * kana dafe }irjinka da hannun dama?

        Ya Allah, ka hallaka sarakunan Gabas, * ka yi nasara a babban birnin duniya.

        Tuntuni ka farfashe Teku da ikonka, * ka kakkarya kawunan Tannin, dodon ruwa, * mai tasowa daga teku.

            Kai ne ka gwararra~e kawunan Lawiyatan, * ka mai da su abinci, * domin kabilun hamada su ci.

                 Kai ne ka saki ma~u~~ugu da ’yan rafuka, * ka ba da busasshiyar }asa daga tsaffin koguna.

            Kai ne mai rana da dare, * kai ne ma ka halicci rana da wata.

        Kai ne ka shata kusurwoyin duniya, * kai ne mai gumi mai ]ari.

    Ka tuna cin mutuncin magabci, * wanda ya sa~e ka, Yahweh, * da wawayen mutanen da suka sa~e ka.

        Kada ka ba mahaukatan dabbobi * mutanen da ka koyar wa.

            Ya Jarumi, kada ka }yale * rayukan gajiyayyunka.

        Ka dubi Haikalinka, * birnin ya cika da duhu, * karkara kuma da fitina.

    Kada dannannu su sha kunya, * amma bari matalauta da mabukata su yabi sunanka.

Ka tashi, ya Allah, ka tsare hakkinka! * Ka tuna yadda wawaye ke sa~onka wuni zubut.

Kada ka mance da rurin magabtanka, * da hargowar abokan gabarka da ke tasowa kullun.


Zabura ta 75

Mun gode maka, ya Allah, * mun gode maka, ya Makusaci! * sammanka suna bayyana al’ajibanka.

    I, zan kira taron jama’arka, * in kuma yi shari’ar adalci.

    Da duniya ke girgiza, * da dukan mazaunanta, * ni ne ke kafa ginshi}anta.

        Na ce, “Ku masu fankama, kada ku yi ta}ama, * ku miyagu, kada ku ]aga muryar }ahonku!

            Kada ku yi karo da Ma]aukaki, * kada ku yi magana gâba da Dutsen Fil’azal.

            Domin shi Mai Nasara ne daga Gabas da Yamma, * Shi Mai Nasara ne daga hamadar kudu har duwatsun arewa.

        Domin shi Allah sarki ne, * yana saukad da mutun, * ya tashe shi kuma.

    Domin akwai }o}o a hannun Yahweh, * da bangaji cike da abinshan inabi, * yakan ]ebo, yana zubawa.

    I, za su shanye tsakin, * dukan miyagun duniya za su sha mana!>Amma ni zan ]aukaka Madauwamin, * in yi wa}a ga Allah na Yakubu.

Zan kakkarya dukan }ahonin miyagu, * amma }ahonin Mai Adalcin za su ]aukaka.

Zabura ta 76

Allah ya bayyana a Yahuda, * a Isra’ila ma sunansa babba ne.

    Kogonsa a Salem yake, * ma~oyarsa a Sihiyona.

    Da wal}iyoyinsu ya kakkarya bakan, * da garkuwar da takobin da makaman ya}i.

        Ya Haske, kana da kwarjini, * sun yi aniyar kai hari a duwatsun Zaki,

        Amma maya}an sun yi barcinsu na }arshe, * ba a }ara samunsu ba, * sojojin sun hallaka duk da }arfinsu.

        Da rurinka, ya Allah na Yakubu, * karusar da dokin sun fâ]i sumammu.

            Kai ka]ai ne mai razanarwa, * wa zai iya tsayawa a haushinka, * ga hushinka na tuntuni?

        Daga samaniya zaka yanke hukunci, * }asa za ta gigice, ta yi tsit.

        Sa’ad da ka tashi yin shari’a, ya Allah, * don ka ceci gajiyayyun duniya,

        za su yabe ka domin tunzurarka da bil’adama, * wa]anda suka rage bayan haushinka za su kewaye ka.

    Ku yi wa’adodinku, ku cika * ga Yahweh Allahnku.

    Bari dukan na kewaye da shi * su kai baye-baye ga Mai Gani.

Ya san tunanin hakimai, * mai bantsoro ne ga sarakunan duniya.

Zabura ta 77

Ina kuka, ya Allahn alloli, * ina kuka sosai.

Ina kuka, ya Allahn alloli, * ka ji ni!

    Da nike ro}on Allahna, * ina neman Ubangijina,

    hannunsa yana fâda ni da dare, * baya denawa, * ransa ya }i juyaji.

        Nikan tuna da Allah da nishi, * ina magana, amma ruhuna ya karai.

        Idanuna sun saba da tsaro, * yawo nike yi, ba kwanciya ba.

            Ina tunanin zamanin dâ, * ina tuna shekarun da suka shu]e.

            Dukan dare ina ka]a molo, * ina magana a zuciyata, * ta yadda ruhuna zai warke.

                 Ubangiji zai yi hushi har abada? * Ba zai }ara jin tausayi ba?

                 Ya dena yin alheri har abada? * ba za a sake samun wahayi daga gunsa ba?

                      Ko kayan cikin Allah sun bushe? * Ko kuwa cikinsa ya ]ame don zafin hushi?

                      Ina jin, “Ciwonsa ke nan, * hannun dama na Ma]aukaki ya shanye.

                 Zan ba da labarin ayyukanka masu banmamaki, * i, zan fa]i al’ajibanka na tuntuni.

                 Zan lissafta dukan ayyukanka, * in yi maganar manyan ayyukanka.

            Ya Allah, kana mulkin dukan tsarkakan mala’iku. * Wane allah ne ya fi ka girma, ya Allah?

            Ka zo, ya Allah mai aikata al’ajibai, * ka nuna ikonka gun mutane.

            Da dantsenka mai }arfi * ka fanshi ’ya’yan Yakubu da na Yusufu.

        Da ruwaye suka gan ka, ya Allah, * da ruwaye suka gan ka, sun gigice, * har zurfafan teku sun razana.

        Gajimarai sun saki ruwa, * sararin sama ya amsa muryarka, * kibanka sun tafi ko’ina.

    Aradunka ta yi kururuwa a tulluwar sararin sama, * wal}iyoyinka sun haskaka duniya, * {al}ashin {asa kuwa ya razana, ya girgiza.

    Hanyarka bisa teku take, * kana jan zanenka bisa ruwayen da ke sama, * don haka ba a ganin digadiganka.

Ka yi jagoran mutanenka kamar tumaki, * ta hannuwan Musa da Haruna.

Zabura ta 78

    Mutanena, ku kasa kunne ga koyaswata, * ku karkata kunnuwanku ga maganad da zan fa]i.

    Zan bu]e bakina, in yi magana da misali, * zan bayyana kacinci-kacinci na zamanin dâ.

        Abin da muka ji muka sani, * da kakanninmu suka gaya mana,

        ba za mu ~oye wa ’ya’yanmu ba, * amma za mu sanar da tsara mai zuwa,

        nasarar Yahweh mai ]aukaka * da al’ajiban da ya aikata.

            Ya kafa ka’ida don Yakubu, * da doka don Isra’ila,

            da cewa abin da ya umurci kakanninmu * su sanad da ’ya’yansu,

        don tsara ta gaba ta sani, * da ’ya’yan da za a haifa su tashi, * su ba ’ya’yansu labarin,

        don su kafa begensu ga Allah, * kada kuma su manta da ayyukan Allah,

    su dinga kiyaye dokokinsa, * kada kuma su zama kamar kakanninsu,

    sangartacciyar tsara mai tawaye, * wadda ba ta yin abu da zuciya ]aya, * da ruhunsu bai amince da Allah ba.

’Ya’yan Ifraimawa ne maya}a masu baka, * maharbansa masu ha’inci, * masu juya baya a ranar ya}i.

Sun kasa kiyaye yarjejeniyarsu da Allah, * sun kuma }i bin shari’arsa.

Sun mance da ayyukansa, * da kuma al’ajiban da ya nuna masu.

    A idanun kakanninmu ya aikata al’ajibai, * a filin Zowan,a }asar Masar.

    Ya raba teku, ya ratsa ta ciki da su, * ya sa ruwayen sun tsaya kamar bango.

    Da rana ya bi da su da gajimare, * da duhu kuma da hasken wuta.

Ya faskara duwatsu a daji, * ya kuma ni’imantad da babbar hamada.

Ya fid da }oramu daga cikin dutse, * ya sa ruwa yana gudada kamar koguna.

    Duk da haka sun ci gaba da sa~onsa, * suna yi wa Ma]aukaki tawaye a hamada.

    Sun gwada Allah a zukatansu, * suna ro}on abinci don ma}ogwaronsu.

        Suka yi maganar sa~on Allah, suka ce: * “Ko Allah na iya shirya abinci a jeji?”

        Ko da yake ya bugi dutsen, * ruwa kuma ya yi ambaliya, * }oramu sun malalo,

        anya zai iya ba da abinci, * ko nama ga mutanensa?

            Lokacin da Yahweh ya ji su, * sai ya fusata,

            ya harzu}a da Yakubu, * hushinsa ya yi }una kan Isra’ila,

            don ba su gaskata da Allah ba, * balle dogara ga ceton da zai yi.

            Duk da haka, ya umurci sararin sama, * ya bu]e }ofofin sammai.

            Ya zubo masu manna don su ci, * ya ba su tsaba ta sama.

            [an’adan tukururu ya ci abincin mala’iku, * ya aiko masu da abinci a wadace.

        Ya sa iskar gabas ta buso daga sama, * ya ma saki iskar kudu daga mafakarsa.

        Ya zubo masu nama daga sama kamar }urâ, * tsuntsaye kuwa kamar yashin teku.

    Ya sa sun zuba a tsakkiyar sansaninsu, * da kewayen zangonsu.

    Ta haka suka ci, suka }oshi, * ya kawo masu iyakar abin da suka lashe.

        Ba su dena tsegunguma ba, * duk da yake ga abinci a bakinsu.

        Hushin Allah ya yi }una a kansu, * ya kashe }arfafansu, * ya yayyanke za~a~~un matasan Isra’ila.

            Duk da haka sai suka ci gaba da yin zunubi, * ba su gaskanta da al’ajibansa ba.

            Ya sa kwanakinsu saurin wucewa fiye da tururi, * shekarunsu kuma sun fi iska gudu.

                 Da ya ri}a kisansu, sai suka neme shi, * suka tuba, suka bi shi da aniya.

                 Sai suka tuna Allah ne Dutsensu, * Allah Ma]aukaki kuma Mai Cetonsu.

                 Amma sun yi masa da]in baki, * sun kuma yi masa }arya da halshensu.

                 Zuciyarsu ba ]aya ba ce game da shi, * domin ba su gaskanta da yarjejeniyarsa ba.

            Amma Mai Jin}an ya gafarta masu zunubansu, * bai hallaka su ba.

            Sau tari ya huce hushinsa, * bai ta da hasalarsa ba.

            Ya tuna su nama da jini ne kawai, * iska mai wucewa ba komowa.

        Sau nawa suka tayar masa a jeji, * suna ba}anta masa ciki a hamada.

    A kai a kai suka gwada Allah, * suna tsokanar Tsattsarkan Nan na Isra’ila.

    Ba su tuna da ikonsa ba, * loton da ya fanshe su daga abokin gaba,

        da ya aikata al’ajibai a Masar, * da abubuwan banmamaki a filin Zowan,

        inda ya mai da ruwan kogunansu jini, * ba su kuma iya shan ruwan koramunsu ba.

            Ya aika }udaje don su cinye su, * da kwa]i don su hallaka su.

            Ya ba farin]ango hatsinsu, * amfanin gonakinsu kuma ga }wari.

                  Ya kashe inabinsu da }an}ara, * da ]oroyinsu da sanyi mai sandararwa.

                 {an}ara ta hallaka shanunsu, * garkunansu gatarin aradu ya tarwatsa.

                      Ya aiko masu da zafin hushinsa, * haushi da hasala da ru]ewa,

                      da ke raka mala’iku masu hallakarwa, * wa]anda ke share masa hanya.

                           Bai ke~e su daga mutuwa ba, * amma ya ba da ransu ga annoba.

                           Ya kashe duk ]an fari a Masar, * amfanin farko na komi nasu a tantunan Hamu.

                           Sannan ya ja gaban mutanensa kamar tumaki, * yana bi da su ta cikin jeji.

                           Ya kare su ba falgabobi, * amma ruwan teku ya dulmuye magabtansu.

                      Ya kai su tudunsa mai tsarki, * dutsen nan da hannun damansa ya kafa.

                      Ya kori al’ummai a gabansu, * ya kâ da su a }asarsu mai tsaunuka, * ya sa kabilun Isra’ila sun gaje tantunansu.

                 Amma suka ci gaba da gwada Allah ta tawayensu, * ba su kiyaye dokokin Ma]aukaki ba.

                 Suka yi tawaye da rashin aminci kamar kakanninsu, * sun gaza aiki kamar lalataccen baka.

                 Suka tsokane shi da mabautansu kan tsaunukansu, * da gumakinsu kuma suka sa ya ji kishi.

            Allah ya ji su, ya husata, * Mai Iko ya }i Isra’ila.

            Ya bar mazauninsa da ke Shilo, * tantin da ya kafa a tsakkiyar mutane.

        Ya bar mafakarsa ga masu kwashe ganima, * akwatin yarjejeniyarsa kuma a hannun magabci.

        Ya ba da mutanensa ga kaifin takobi, * ya yi hushi da gadonsa.

    Wuta ta }one samarinsu, * ’yan matansu kuma ba a yi masu wa}ar amarci ba.

    Firistocinsu sun hallaka da kaifin takobi, * gwaurayensu kuma ba su yi wa}ar makoki ba.

Sannan Ubangiji ya farka kamar wanda ke barci, * sai ka ce jarumin da ke hutu bayan shan barasa.

Ya runtumi magabtansa daga bayansu, * ya rufe su da kunya ta har abada.

    Ya yi watsi da alfarwoyin Yusufu, * bai ma za~i kabilar Ifraimu ba.

    Amma ya za~i kabilar Yahuda, * da Dutsen Sihiyona da yake }auna.

    Ya gina tsattsarkan mabautarsa da tsawo kamar sammai, * ya tabbatad da ita kamar }asa da ya kafa tun fil’azal.

Ya za~i baransa Dauda, * wanda ya ]auko daga garken tumaki.

Daga kiwon tumaki ya kirawo shi, * don ya yi kiwon jama’ar Yakubu da ke tasa, * da Isra’ila abin gadonsa.

Ya lura da su da kyakkyawar zuciya, * da jagoranci mai kyau ya bi da su.

Zabura ta 79

Ya Allah, ba}i sun afka wa gâdonka, * sun }azanta Haikalinka, * sun mai da Urushalima kufai.

    Sun bar wa tsuntsaye * gawarwakin bayinka su ci,

        da naman masu bautarka * ga namomin daji.

    Sun zub da jininsu kamar ruwa * ba wani daga kewayen Urushalima * da zai binne su.

Mun zama abin zargi ga ma}wabtanmu, * abin ba’a da }yama ga wa]anda ke kewaye da mu.

    Yahweh, sai yaushe? * Za ka yi hushi har abada? * Har yaushe kishinka zai dinga }una kamar wuta?

    Ya Allah, ka kwararo hushinka, * a kan al’umman da ba su san ka ba, * da kan masarautun da ba su kiran sunanka.

    Domin sun cinye Yakubu, * sun kuma mai da }asarsa kufai.

        Ya Magatakarda, kada ka rubuto laifinmu,* ko muguntar da kakanninmu suka aikata.

        Bari jiye-jiyen kanka su tarbe mu, * domin mun }as}anta }warai.

    Ka taimake mu, ya Allahnmu mai nasara! * Don sunanka mai ]aukaka ka cece mu, * ka gafarta mana zunubanmu saboda sunanka,

    don kada al’ummai su ce, * “Ina Allahnsu?”

    Don mu ga sunanka ya sanu ga al’ummai, * ka rama jinin bayinka da aka zubas!

Bari ajiyar zucin ]aurarru * ta zo wurinka.

    Mi}o hannunka mai tsawo, * ka kare wa]anda aka tanaji kisansu.

        Ya Ubangiji, ka biya wa ma}wabtanmu ri~i bakwai * na zagin da suka yi maka.

    Mu mutanenka ne, tumakin makiyarka, * za mu gode maka har abada.

Daga tsara zuwa tsara kuma * za mu yi shelar yabonka.

Zabura ta 80

            Ya Makiyayin Isra’ila, ka kasa kunne, * ka shugabanci Yusufu kamar garke.

            Ya Mai Zama a kan Kerubobi, ka haskaka * a gaban Ifraimu da Biliyaminu da Manassa!

            Ka ta da }arfinka, * ka zo ka cece mu!

Ya Allah, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Yahweh Allah Mai Runduna, * yaya za ka yi hushi, * lokacin da jama’arka ke yin addu’a?

    Ka }osad da mu da kwalla, * ka shayad da mu da bangaji-bangajin hawaye.

    Ka mai da mu madari ga ma}wabtanmu, * ma}iyanmu ma suna yi mana dariya.

Ya Allah Mai Runduna, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Kâ fito da kuringar inabi daga Masar, * kâ kori sauran al’ummai, kâ dasa ta.

    Kâ tuge wa]anda suka gaje ta, * kâ sa ta kafa sauya, * ta kuma mamaye }asar.

        An lullu~e duwatsu da inuwarta, * ganyayenta sun rufe rimin Allah.

        Ka sa rassanta su bazu har Bahar Maliya, * ya]unanta kuma har Kogin Yufiretis.

    Me ya sa ka rushe shingenta, * don duk mai wucewa ya tsigi inabinta?

    Alhanzir-alhanzir na daji sun yi kiwo a cikinta, * zomaye da bareyi sun yi ta cinye ta.

Ya Allah Mai Runduna,, ka juyo wurinmu yanzu-yanzu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

    Ka lura da abin da hannun damanka ya dasa, * da kuma [an da ka }arfafa don kanka.

        Wa]anda suka banka mata wuta, * bari su hallaka ta tsautawar hushinka.

        [ora hannunka kan mutumin da ke hannunka na dama, * da kan [an’adan da ka }arfafa don kanka.

    Ba mu ta~a juya maka baya ba, * ka raya mu don mu kira sunanka.

Yahweh Allah Mai Runduna, ka juyo wurinmu, * bari fuskarka ta haskaka, * dom mu sami tsira.

Zabura ta 81

        Ku yi sowa ta farinciki ga Allahmu na Akwatin Yarjejeniya, * ku yi hayaniyar murna ga Allahn Yakubu.

        Ku raira wa}a, ku buga kuge da tambari, * da ki]in molo mai da]i da garaya.

            Ku busa }aho a amaryar wata, * da tsakkiyarsa, ran aikin hajinmu.

        Domin ka’ida ce, ya Isra’ila, * umurni ne kuma daga Allahn Yakubu.

        Ya sanya shi ga Yusufu kamar doka, * sa’ad da ya fito daga Masar.

Na ji maganar wanda ban san shi ba, * na sauke kaya daga kafa]arsa, * an hutad da hannuwansa daga ]aukar kwando.

    A cikin wahala ka yi kira, * na kuwa ku~utad da kai.

Na amsa maka daga ma~oyar aradu, * ko da yake kun fusata ni wurin ruwan Mariba.

    Ku ji, ku mutanena, zan maku bakar shaida, * Isra’ila, sai ku kasa kunne gare ni.

    Kada wani ba}on allah ya kasance a tsakaninku, * ba kuma za ku bauta wa shigaggen allah ba.

        Ni ne Yahweh, Allahnku, * da ya fito da ku daga }asar Masar, * na kuwa hangamemen bakinku.

    Amma mutanena ba su ji muryata ba, * Isra’ila kuma bai yarda da ni ba.

    Don haka na yi watsi da su kan taurin zuciyarsu, * sun bi nasu shawarwari.

Dâ ma mutanena sun saurare ni, * Isra’ila sun ya bi turbata!

    Da nan take zan kau da magabtansu, * in juya hannuna kan ma}iyansu.

    Duk ma}iyan Yahweh za su du}a a gabansa, * za su ]an]ana kudarsu har abada.

Sannan zai }osad da Isra’ila da alkamar tuddai, * zan kuwa }osad da ku da zuma na kan duwatsu.


Zabura ta 82

Allah yana yin jagorancin taron alloli, * yana zartas da hukuncinsu a tsakkiyarsu:

    “Me ya sa kuke kâre marasa gaskiya, * da son zuciya kan miyagu?

    Kâre gajiyayyu da marayu, * ba da gaskiya ga wanda aka cuta da matalauci.

    Ceci gajiyayyu da mabukata, * ka cece su daga hannun miyagu.”

    Ba sani ko fahinta, * suna ta yawo cikin duhu. * Ana girgiza dukan harsashun duniya.

    Na yi zaton, “Ku alloli ne, * dukanku ’ya’yan Ma]aukaki ne.

    Amma kamar mutane za ku mutu, * ku bau]e kamar kowane sarki.”

Tashi, ya Allah, ka hukunta duniya, * ka sarauci dukan al’ummai da kanka.

Zabura ta 83

Ya Allahna, wane allah ne ya yi kama da kai? * kada ka yi shiru, kada ma ka yi zugum, ya Allah.

    Dubi yadda magabtanka ke surutu, * ma}iyanka kuma suna ]aga kansu.

        Suna shirya wa mutanenka shawarwarin makirci, * a kan hajarka suke yin ma}ar}ashiya.

    Suna cewa: “Ku zo, mu shafe al’ummarsu, * kada a }ara jin sunan Isra’ila.”

        I, suna yin shawara da zuciya ]aya, * masu tasar maka suna }ulla yarjejeniya:

        Idumawa da Isma’ilawa, * Mowabawa da Hagarawa,

            Bibilosawa tare da Amalakawa, * Filistiyawa da mutanen Taya,

            jama’ar Assuriya ma ta gama kai da su, * inda ta zama garkuwar ya}in ’ya’yan Lutu.

            Ka yi da su kamar yadda ka yi da Midiyan * da Sisera, da Yabin a Kogin Kishon.

            Ka shafe su daga fuskar duniya, * sai sun zama taki.

        Ka mai da dattawansu kamar Oreb da Ziyib, * da dukan sarakunansu kamar Zeba da Zalmunna,

        wa]anda suka ce, “Bari mu }wato * wurare mafi kyau na }asarsu.

    Ya Allahna, ka mai da su kamar bunu, * kamar }ai}ai a gaban iska.

        Kamar wutar gobarar kurmi, * da harsunan wuta masu lashe gefen dutse,

            ka runtume su da hadarinka, * ka raka su da iskarka mai }arfi.

        Ka cika fuskarsu da kunya, * Yahweh, ka ]au fansar sunanka.

    Bari su kunyata, su muzanta * har abada * su hallaka da }as}anci.

Bari su san kai ne ke da suna “Yahweh”, * kai ka]ai ne Ma]aukaki bisa dukan duniya.

Zabura ta 84

Lalle, mazauninka mai da]i ne, * Yahweh Mai Runduna!

Yahweh, raina yana ]oki da marmarinka sosai, * ga begen farfajiyarka! * zuciyata da jikina suna sowa.

    Ya Allah, ya Allah Mai Rai, * har gwara ta sami gida.

        Tsattsewa kuma ta sami she}a, * inda za ta sa ’ya’yanta.

            Yahweh Mai Runduna, * Sarkina da Allahna!

        Albarka ga mazaunan gidanka, * kusa da bagadanka suna ri}a yabonka.

    Albarka ga wanda mafakarsa a wurinka ne, * zuciyarsa kuma tana yabonka.

        Allah ya }addara }oramu su malalo a kwarin, * ya mai da kwarin ma~u~~uga.

        Da tsautawa Mai Ba da Ruwa * ya yawaita shi da tabkuna!

            Suna tafiya daga }auye zuwa }auye, * don su ga Allah mai alloli a Sihiyona.

        Yahweh, Allah Mai Runduna, * ka ji addu’ata, * ka kasa kunne, ya Allah na Yakubu!

        Ka duba shugabanmu da alheri, ya Allah, * ka zuba ido a kan fuskar shafaffen sarkinka.

    Kwana ]aya a farfajiyarka * ya fi kwana dubu a Kabari kyau.

        Gara a jira a }ofar gidanka, ya Allahna, * da zama a Alfarwar Mugu.

        Lalle, Ranarmu da Shugabanmu, * Yahweh Allahnmu * ya kan ba da alheri da ]aukaka.

    Yahweh ba zai hana ruwansa ba * daga masu bin hanyar gaskiya.

Yahweh Mai Runduna, * albarka ga wanda ya dogara gare ka!

Zabura ta 85

Yahweh, ka kyautata wa }asarka, * ka mai da lafiyar Yakubu!

Ka kau da laifin mutanenka, * ka yafe dukan zunubansu!

Ka kau da duk haushinka, * ka huce zafin hushinka!

    Yahweh mai arzuta mu, ka komo mana, * ka sauke fusatar da ka yi da mu!

    Za ka yi hushi da mu ne har abada? * kana tsawaita hushinka har ga tsararraki masu zuwa?

        Kai ne Mai Nasara, * ka sake raya mu, * don mutanenka su yi murna da kai.

        Yahweh, ka nuna mana tausayinka, * ka ha]a mu da arzikin da ka kan bayas.

            Bari in fa]i abin da Allah ya ce: * “Hakika, Yahweh ya alkawalta zaman lafiya

        ga mutanen da ke bautar masa, * da masu sake sa zuciya a gunsa.

        Albarkarsa tana dab da masu tsoronsa, * i, ]aukakarsa tana zaune a }asarmu.

    Tausai da aminci za su gamu, * gaskiya da lafiya za su sumbaci juna.

    Aminci zai tsiro daga }asa, * gaskiya za ta karkato daga samaniya.

Da tsautawa Yahweh zai ba da ruwan sama, * }asarmu kuma za ta ba da amfaninta.

Gaskiya za ta yi tafiya gabansa, * kyan gani kuma zai bi sawayensa.

Zabura ta 86

Ka karkato kunnenka, Yahweh, ka amsa mani, * domin ni gajiyayye ne da mabukaci.

Ka kiyaye raina, * domin ni mai bautarka ne.

    Ka ceci bawanka * da ke dogara gare ka, ya Allah.

Ka ji tausayina, ya Ubangijina, * a gare ka nike yin kuka wuni zubut.

Ka faranta ran baranka, ya Ubangijina, * domin a gare ka nike ]aga raina.

    Tun da kai, Ubangijina, mai alheri da yafewa ne, * mai yalwar rahama ga duk masu ro}onka,

        ka kasa kunne, Yahweh ga addu’ata, * ka ji ro}ona na neman afuwa.

        Ran da ake tsananta mani na kira ka, * sai ka amsa mani!

    Babu kamarka a cikin alloli, * ya Ubangijina, * ba kuma ayyuka irin naka.

        Ya Ubangijina, in ka yi wani abu, * dukan al’ummai za su zo,

        su yi sujada a gabanka, * su ]aukaka sunanka.

    Hakika, kai mai girma ne, * Mai Yin Al’ajibai, * kai ka]ai, ya Allah.

        Ka nuna mani hanyarka, Yahweh, * don in bi ka kai ka]ai da aminci. * Koya wa zuciyata don in ji tsoron sunanka.

        Zan yi maka godiya, ya Ubangijina da Allahna * da dukan zuciyata * zan ]aukaka sunanka, ya Madauwami.

    Tun da }aunarka mai girma ce, ya Ma]aukaki, * za ka jawo ni daga }arshen Shawol.

Ya Allah, masu alfarma sun tasam mani, * kungiyar mafa]ata tana neman raina, * ba su kula kai ne Shugabana ba.

Amma kai, ya Ubangijina, Allah ne mai rahama mai jin}ai, * mara jinkirin hushi, mai yalwar jin}ai da gaskiya. * Ka juyo gare ni, ka ji tausayina.

    Ka ba bawanka nasararka, * ka sa ]anka mai aminci ya rinjaya.

Ka aikata mani alama, ya Managarci, * don ma}iyana su gani su kunyata.

Yahweh, kai kanka ka taimake ni, * ka sanyaya mani zuciya.

Zabura ta 87

        Ya birnin da ya kahu a kan tsarkakan duwatsu, * ya }ofofin Sihiyona, Yahweh yana son ku.

        Shi ne Gwanin ginin gidajen Yakubu masu ]aukaka * da ke magana a cikinka, ya birnin Allah:

“Zan rubuta Masar da Babila * a cikin wa]anda suka san ni,

    har da Filistiya da Taya da Habasha: * Wa]ansunsu a can aka haife su.

        Amma game da Sihiyona za a ce: * “Kowanensu an haife shi a can, * Ma]aukaki kuma zai tabbatad da ita.

    Yahweh zai rubuta a cikin kundin mutane, cewa: * “An haifi wannan a can.”

Dukan wa]anda suka sha wuya a cikinki * za su yi wa}a da rawa.

Zabura ta 88

Yahweh, Allahna Macicina, * da dare da rana ina kuka gare ka.

Bari addu’ata ta zo gabanka, * ka kasa kunne ga kukana.


Gama ruhuna cike ya ke da wahala, * raina kuma ya kai gab da Shawol.

An lissafta ni tare da masu zuwa Rami, * na zama mutun mara }arfî.

    A fadar Mutuwa tabarmana yake, * kamar yankakku, * gadona yana Kabari,

    inda ba ka tunawa da su, * tun da an yanke }aunarka daga gare su.

    Kâ jefa ni }uryar Rami, * a wurare masu duhu da zurfi.

    Hushinka ya yi }una a game da ni, * ka ma tsananta haushinka a kaina.

Ka sa abokaina yin nesa da ni, * don na zama abin }yama a gare su.

Ina kurkuku, bana iya gudu, * idanuna sun rage gani saboda wahala.

    Ina kiran gare ka kullun, Yahweh, * ina ]aga hannuwana gare ka.

        Kana aikata al’ajibai ga matattu? * Ko kuwa kurwoyinsu na tashi su yabe ka?

            Ana sanar da alherinka a Kabari? * ko kuwa amincinka a {asar Mutuwa?

        Ana sanar da mu’ujjizanka a Duhu? * ko kuma alherinka a {asar Mantuwa?

    Amma ina yin kira gare ka, Yahweh, * da asuba bari addu’ata ta zo gabanka.

Yahweh, don me kake ya da ni? * kana juya fuskarka daga gare ni?

    Da }unci da nishi ina mutuwa, * ina shan wahala daga tsananinka.

        Harzu}arka ta bangaje ni, * bankarka ta yi kaca-kaca da ni.

    Suna kewaye ni wuni zubut kamar tsufana, * suna kai mani hari a ka]aicina.

Kâ kai ma}wabcina mai }aunata nesa da ni, * duhu ka]ai ne abokina.

Zabura ta 89

        Yahweh, zan raira wa}ar }aunarka har abada, * zan yi shelar amincinka a kowane zamani.

        Da bakina ina furtawa: * “Ya Madauwami, }aunarka ce ta halicci sammai, * amma ka sa amincinka ya zarce su nesa.

        Na yi yarjejeniya da za~a~~ena, * na rantse wa barana Dauda:

        “Zan kafa zuriyarka har abada, * in inganta kursiyinka ga dukan zamanai.

A can sama ana yabon alkawalinka, Yahweh, * amincinka kuma a taron tsarkaka.

Domin wanene a sama ya iya kwatanci Yahweh? * Wa ya iya kwatancin Yahweh a cikin alloli?

    Allah ne mai bantsoro a mashawartar tsarkaka, * mai girma, mai banrazana ga dukan wa]anda ke kewaye da shi.

    Yahweh, Allah Mai Runduna, wa yake kamarka? * Yahweh mai iko, amintattunka suna kewaye da kai.

        Kai ne mai mulkin gadon bayan teku, * in ra}uman ruwansa na tashi, kai ne mai kwantad da su.

        Kâ rushe Rahab kamar gawa, * da hannunka mai }arfi ne kâ yi ]ai]ai da magabtanka.

            Kai ne mai sammai da }assai, * duniya da dukan abin da ke cikinta kai ne ka kafa su.

            Duwatsun Zafon da Amanus kai ne ka hallice su, * Dutsen Tabor da Dutsen Harmon suna wa}a a gabanka.

        Kana da hannu }a}}arfa, ya Maya}i, * hannun hagunka ya jarunta, * hannun damanka ya ci nasara.

        Gaskiya da adalci su ne harsashin kursiyinka, * }auna da aminci suna tsaye a gabanka.

    Masu albarka ne da ke sanin haskenka, * wa]anda ke tafiya da }yal}yalin fuskarka, Yahweh.

    Suna farinciki a gabanka wuni zubut, * suna murna da alherinka.

I, kai ne nasararmu mai ]aukaka, * agajinka yana sa mu ci nasara.

Hakika Yahweh ne Shugabanmu, * Tsattsarkan Nan na Isra’ila shi ne Sarkinmu.

    A zamanin dâ ka yi magana ta wahayi, * i, ka ce da mai bautarka:

    “Na mai da matashi sarki a maimakon maya}i, * na ]aukaka saurayi fiye da mai }arfi.

        Na sami barana Dauda, * da maina mai tsarki na shafe shi.

        Hannuna ne zai tabbatad da ikonsa, * kafadata za ta }arfafa shi.

            Ba magabcin da zai tsokane shi, * ]an mugunta ba zai rinjaye shi ba.

            Amma zan gwabji magabtansa a gabansa, * in kâ da ma}iyansa.

                 Amincina da }aunata suna tare da shi, * ta wurin sunana zai yi nasara.

                 Zan sa hannun hagunsa bisa teku, * hannun damansa kuma kan Yufiretis.

                      Shi zai kira ni, * ‘Kai ubana ne, Allahna, * kuma Dutsen cetona.’

                      Zan mai da shi ]an farina, * mafi ]aukaka a cikin sarakunan duniya.

                 Zan }aunace shi har abada, * yarjejeniyata da shi za ta tabbata.

                 Zan sa zuriyarsa a kan kursiyinsa, * gadon mulkinsa ma zai da]e kamar kwanakin sammai.

            In ’ya’yansa sun }eta shari’ata, * sun }i bin umurnaina,

            in sun sa~i ka’idodina, * ba su kuma kiyaye dokokina ba,

            zan hori tawayensu da sanda, * taurin kansu kuma da bulala.

        Amma ba zan ta~a janye }aunata daga gunsa ba, * ba ma zan }aryata amincina ba.

        Ba zan karya jarjejeniyata ba, * ko kuwa in canza maganata.

    Daga yanzu na rantse da tsarkina, * bana iya yi wa Dauda }arya.

    Layin mulkinsa zai jure har abada, * kursiyinsa ma kamar rana a gabana.

    Kamar wata jikokinsa za su rayu, * gadon sarautarsa ma zai tabbata fiye da sararin sama.”

Duk da haka cikin zafin hushi kâ jefad da shafaffen sarkinka, * ka harzu}a da shi.

Kâ jefad da jarjejeniyarka da baranka, * ka wulakanta kambinsa.

    Kâ huhhuda garunsa, * ka mai da wuraren tsaronsa kago.

    Duk masu wucewa suna cin ganimarsa, * ya zama abin }yama ga ma}wabtansa.

        Kâ ]aukaka hannun daman abokan gabarsa, * kâ ]aga hannuwan ma}iyansa.

        Da hushinka kâ juye bakin askarsa, * ba ka tabbatad da takobinsa ba.

            Ka sa ya dena tashe a cikin maya}ansa, * kâ kuma jefad da kursiyinsa }asa.

            Kâ gajarta kwanakin samartakarsa, * kâ hana mashi haifuwa cikin }uruciyarsa.

        Yahweh, har yaushe za ka juya baya? * ka bar hushinka, ya Mai Nasara, ya yi ta ci kamar wuta?

        Ka tuna da ~acin raina, * da ’yan kwanakin raina. * Saboda me kâ halicci dukan ’yan’adan?

    Wane rayayyen mutun ne ba zai ga mutuwa ba? * Wa zai }waci ransa daga hannun Shawol?

    Ina ayyukan tausayinka na dâ, * ya Ubangiji, * wa]anda ka alkawalta kan amincinka ga Dauda?

Ka tuna, ya Ubangiji, da cin mutuncin da aka yi wa bawanka, * yadda a }irjina nike ]aukar kiban al’ummai,

yadda magabtanka, Yahweh, ke wulakanta ni, * da zage-zage suke wulakanta shafaffen sarkinka.

Yabo ga Yahweh har abada! * Amin, summa Amin.

Zabura ta 90

Ya Ubangiji, agajinmu, ka zo! * ka zama namu daga zamani zuwa zamani.

Kafin halittar duwatsu, * ko }asa da duniya, * tun fil’azal har abada kana nan.

    Kada ka mai da mutun ga Ca~i, * kada ka ce, “Kai, ku ’yan’adan, ku dawo!.”

    Domin shekaru dubu a ganinka * suna wucewa kamar jiya, * kamar sa’ar tsaro ta dare.

        In ka tsige su da dare, * da sassafe suna kama da ciyawa da aka yanke.

        Ta tsira da safe, * an yanke ta da yamma, * takan yi yaushi ya bushe.

    Muna hallaka a cikin hushinka, * muna gajiya cikin haushinka.

    Kana ri}e da laifofinmu a gabanka, * zunubanmu tun na }uruciya suna a hasken fuskarka.

        Duk kwanakinmu sun shu]e * a cikin hushinka.

            Aiki ya zo }arshe, * shekarunmu kamar ajiyar zuciya suke.

            Tsawon ranmu shekaru saba’in ne, * in muna da }ar}o, shekaru tamanin.

        To, alfarma wauta ce mara kyau, * jin da]i na wucewa, mu ma za mu shu]e.

    Wa zai gane ta’adin hushinka, * ko masu tsoronka ma za su gamu da haushinka?

    Don haka ka koya mana mu }irga kwanakinmu, * don mu sami zuciyar hikima.

        Yahweh, ka dawo, * don me kake jinkiri? * ka ji juyayin bayinka.

        Da safe ka wadata mu da }aunarka, * don mu yi sowar farinciki a dukan kwanakinmu.

    Ka sa kwanakin farincikinmu su zarce na bakincikinmu, * da shekarun da muka ga bala’i.

    Ka bayyana aikinka ga bayinka, * da sarautarka kuma ga ’ya’yansu.

Bari alherin Ubangiji * Allahnmu ya sauko mana!

Ya taimaki aikin hannuwammu * don amfanimmu!

Ya taimaki aikin hannuwammu * don amfaninsa!

Zabura ta 91

Mai kursiyin }al}ashin kâriyar Ma]aukaki, * wanda ke kwana a inuwar Mafi Iko Shaddai,

ya ce: “Yahweh matserata da mafakata, * ya Allahna, na dogara gare ka.”

    Shi ka]ai ne zai tsirad da kai daga tarko, * ya kâre ka daga makamai masu guba.

    Da gashinsa zai rufe ka, * }al}ashin fukafukansa za ka fake, * kafadarsa za ta zama garkuwarka da wargajinka.

        Kada ka ji tsoron taron karnuka da dare, * ko kibiyar da ke walankeluwa da rana,

        ko bala’in da ke shawaji da dufu, * ko allobar da ke kai da kawo da tsakar rana.

    Ko da dubu sun fa]i a hagunka, * dubu goma kuma a damanka, * ba za su kusance ka ba.

    Idanunka za su ga ru~arsu, * za ka ga ribar miyagu.

    In ka mai da Yahweh matserarka, * Ma]aukaki mafakarka,

    ba wani mugun abin da zai same ka, * ba wani bala’in da zai tunkari alfarwarka.

        Gama zai aiko maka da mala’ikunsa, * don su kiyaye ka a dukan hare-haren ya}inka.

    Za su tallabe ka da hannuwansu, * don kada ka yi tuntu~e da dutse.

    Za ka taka zaki da kububuwa, * za ka bi ta kan marakin zaki da maciji.

In ya manne mani, zan cece shi, * in ]aukaka shi in yana shaidar sunana.

In ya kira ni, zan amsa masa, * in kasance da shi a lokacin wahala, * zan cece shi, in shirya masa liyafa.

Zan wadata shi da tsawon rai, * in sa ya sha ruwan cetona.

Zabura ta 92

Yahweh, ya kyautu a yi yabo * da wa}ar sunanka, ya Ma]aukaki,

a yi shelar }aunarka da safe, * da amincinka dukan dare,

da ki]in molo da kuntigi, * da muryar garaya.

    Domin ka sa ni murna, Yahweh, ta aikinka, * saboda abubuwan da ka yi ina wa}a ta murna.

    Ayyukanka manya ne, * Yahweh Mai Duka, * tunaninka suna da zurfi }warai.

        Da}i}i baya sanin haka, * wawa baya ganewa:

            lokacin da miyagu ke toho kamar ciyawa, * dukan masu }eta ma suna ci gaba,

                 yana hallaka su har abada. * amma kai, Yahweh, Mai Sama ne har abada.

                 Domin ga magabtanka, Yahweh, * ga magabtanka sun hallaka, * an fatattaki masu aikata mugunta.

            Amma kâ ]aga }ahona kamar }ahon ~auna, * an shafe ni da sabon mai.

        Idanuna sun harari matseguntana * da miyagu masu neman tasam mani.

    Kunnuwana sun ji: * “Masu gaskiya za su yi albarka kamar icen dabino, * su yi girma kamar icen al-ul na Labanan.

    An dasa su a gidan Yahweh, * za su yi yabanya a farfajiyar Allahnmu.

Suna cike da ruwa har tsufansu, * za su yi zamansu ]anyu masu duhuwa,

suna shelar gaskiyar Yahweh, * shi Dutsena wanda ba cuta gare shi.

Zabura ta 93

Yahweh yana mulki, * yana sâye da ]aukaka.

Yahweh na saye da alkyabba, * ya yi ]amara da nasara.

    Ya kafa duniya sosai, * ba za ta }ara girgiza ba.

    An kafa kursiyinka tun zamanin dâ, * tuntuni kake.

        Igiyoyin teku sun tayas, Yahweh, * igiyoyin teku sun tayas da aradunsu, * igiyoyin teku sun tayas da tsawar
ra}umansu.

    Amma Yahweh ya fi tsawar ruwa }arfi, * ya fi ra}uman ruwan teku iko, * ya fi sama iko.

Kafawar sarautarka ta tabbata tun dâ, * Yahweh, a cikin gidanka tsattsarka za su yabe ka, * har abada abadin.

Zabura ta 94

Ya Allah mai sakayya, Yahweh, * ya Allah mai sakayya, ka haskaka.

Ka tashi, ya alkalin duniya, * ka ba masu izgilanci hakkinsu.

    Har yaushe ne ’yan taurin kai, Yahweh, * har yaushe ne miyagu za su yi alfarma?

    Har yaushe za su yi ta maganar wulakanci, * dukan miyagu za su yi fahariya?

        Sun ragargaji mutanenka, Yahweh, * naka ne suke tsanatawa.

    Sun kashe gwauruwa da ba}o, * suna yi wa marayu kisan gilla.

    A zatonsu, “Yahweh baya gani, * Allah na Yakubu baya yin la’arki.

        Ku da}i}ai, ku koyi hikima! * Ku wawaye, yaushe za ku fahinta?

            Wanda ya dasa kunne, ba ya iya ji? * wanda ya sifanta ido, ba ya iya gani?

            Mai koya wa al’ummai, ba ya iya yin hukunci? * ko kuwa malamin ’yan adan na rasa ilimi ne?

        Yahweh ya san shirye-shiryen mutane, * duk banza ne.

        Yahweh, mai albarka ne wanda ka koyawa,* wanda ka sanar da shari’arka,

            kana ba shi hutu bayan miyagun kwanaki, * lokacin da ake gina rami don miyagu.

            Hakika Yahweh ba zai yas da jama’arsa ba, * ba zai }yale nasa ba.

        Amma Mai Kursiyin Adalci zai raya gaskiya, * da dukan masu kirki.

    Wa ya tsaya mani a game da miyagu? * a kan masu aikata mugunta wa ya goyi bayana?

    In da Yahweh bai zama mataimakina ba, * da tuni na da]e a Kukuku.

        Sa’ad da na ce, “{afata tana nutsewa,” * Yahweh, }aunarka ce ta tallabe ni.

        Sa’ad da damuwata ta yawaita, * ta’aziyyarka ce ta faranta mani rai.

    Anya, kursiyin zalunci zai iya yin tarayya da kai? * mai karya shari’a zai sami kariya a wurinka?

    Sun taru don su kashe mai gaskiya, * a asirce suke hukunta mara aibu.

Amma Yahweh ya zama garu gare ni, * Allahna kuma dutsena na fakewa.

Ya sa muguntarsu ta koma kansu, * saboda sharrinsu ya hallaka su, * Yahweh Allanmu ya hallaka su.

Zabura ta 95

Ku zo, mu yi wa}ar murna ga Yahweh, * mu gai da Dutsen da ya cece mu.

Mu zo gabansa da yabo, * mu gai da shi da wa}o}i.

    Gama Yahweh Allah ne mai girma, * babban Sarki bisa dukan alloli.

    A hannuwansa ne Ramukan {al}ashin {asa suke, * tulluwoyin duwatsu ma nasa ne.

    Ruwan teku nasa ne, tun da shi ya yi shi, * busasshiyar }asa shi ya sifanta ta da hannuwansa.

        Ku zo, mu sunkuya, mu yi sujada, * bari mu dur}usa a gaban Yahweh Mahaliccinmu.

        Gama shi ne Allahnmu, * mu ne mutanen makiyayarsa, * garken filin kiwonsa.

    Yau sai ku saurari Mai Bantsoro yana magana: * “Kada ku taurare zukatanku

    yadda ya faru a Mariba, * ko kamar ranan nan a Masaha cikin jeji,

    inda kakanninku suka jarabce ni, * suna tsokanata, ko da yake sun ga aikina.

Shekaru arba’in na jure da tsaran nan, * sai da na ce:

‘Su mutane ne masu yawo da zuciya, * ba su san hanyoyina ba.’

Daga nan a husace na yi rantsuwa, * ‘Ba za su shiga hutuna ba har abada.’”

Zabura ta 96

Ku yi wa Yahweh sabuwar wa}a, * ku yabi Yahweh, dukan mutanen duniya, * ku yi wa Yahweh wa}a, ku yabi sunansa!

Ku yi zancen nasararsa daga teku zuwa teku! * A tsakkiyar al’ummai ku ba da labarin ]aukakarsa, * da al’ajibansa a gaban dukan mutane!

    Domin Yahweh mai girma ne, mai cancantar yabo, * mai bantsoro ne fiye da dukan alloli, * amma allolin al’ummai tsummoki ne kawai.

    Yahweh ne ya yi sammai, * ]aukaka da kwarjini suna gabansa, * }arfi da kyau a gefensa.

             Ku yi wa Yahweh, ku kabilan mutane, * ku yi wa Yahweh ]aukaka da yabo, * ku yi wa Yahweh ]aukakar da ta cancanci sunansa.

             Ku kawo baiko, ku shiga farfajiyarsa, * ku sunkuya wa Yahweh loton da Tsattsarkan nan ya bayyana, * ku yi rawar jiki a gabansa, ku dukan duniya!

    A tsakkiyar al’ummai ku ce, “Yahweh yana mulki. * duniya ta kafu, ba za ta jijjigu ba. * Zai shari’anta mutane da gaskiya.

    Bari sammai su yi murna, duniya ta yi farinciki, * bari teku da duk abin da ke cikinsa su yi }ugi, * tuddai da duk abin da ke a kansu su ji da]i!

Sannan dukan itatuwan kurmi za su yi sowar murna * a gaban Yahweh in ya zo, * in ya zo domin hukunta duniya.

Zai hukunta duniya da gaskiya, * al’ummai da amincinsa.

Zabura ta 97

Yahweh yana mulki, * bari duniya ta yi murna, * tsibirai masu yawa kuma su cika da fara’a.

    Gajimarai da hadari suna kewaye shi, * adalci da gaskiya ne tushen kursiyinsa.

Wuta tana tashi a gabansa, * tana kuma bin bayansa.

    Wal}iyoyinsa suna haskaka duniya, * }asa ta gani tana rawar jiki.

    Duwatsu suna narkewa kamar kyandir * da ganin Yahweh, * da ganin Ubangijin duniya duka.

        Sammai suna fa]in hakkinsa na gaskiya, * dukan mutane kuma suna ganin ]aukakarsa.

        Bari dukan masu bautar gumaka su kunyata, * masu rubar tsummokinsu. * Ku sunkuya masa, ku alloli duka.

    Bari Sihiyona ta ji, ta yi farinciki, * ’ya’yan Yahuda mata su yi murna, * saboda tabbacin }aunarka, Yahweh.

    Domin kai ne Yahweh Ma]aukaki, * Mafi Girma bisa dukan duniya, * kai ne bisa dukan alloli.

Yahweh na son masu }in mugunta, * yana kiyaye rayukan masu bautarsa, * zai cece su daga hannun miyagu.

An }addara lambun aljanna domin masu adalci, * farinciki kuwa don zukatai masu gaskiya.

Ku yi farinciki da Yahweh, ku masu gaskiya, * ku yi wa tsattsarkan sunansa godiya.

Zabura ta 98

Ku yi wa Yahweh sabuwar wa}a, * domin ya yi al’ajibai.

Hannunsa na dama ya kawo masa nasara, * dantsensa kuma ya ke~e shi.

Yahweh ya sanar da nasararsa * a idanun al’ummai * ya nuna ramuwarsa.

    Ku tuna da }aunarsa da amincinsa, * ya gidan Isra’ila!

    Dukan iyakokin duniya, * ku ga nasarar Allahnmu!

        Ku yi sowa ga Yahweh, dukan duniya, * ku yi hayaniyar murna da wa}o}in farinciki.

        Ku raira wa}a ga Yahweh da molo, * da molo da murya mai da]i.

        Da algaitu da muryar }ahoni, * ku yi wa}a a gaban Yahweh Sarki!

    Bari teku da abin da ke ciki su yi }ugi, * duniya da dukan mazaunanta.

    Bari igiyoyin teku su ta~a hannu, * duwatsu su yi sowa tare don murna

a gaban Yahweh, * in ya zo, * don ya hukunta duniya.

Zai hukunta duniya da gaskiya, * al’ummai kuma da adalci.

Zabura ta 99

Yahweh ne yake mulki, * bari mutane su yi rawar jiki.

Mai Zama a kan Kerubobi, * bari }asa ta girgiza.

Yahweh ya fi Sihiyona girma, * yana birbishin dukan }arfafan iskoki.

    Bari su yabi suanka, * ya Mai Duka, Mai Bantsoro. * Tsattsarka ne shi!

    Sarki mafi }arfi, * mai son gaskiya, * kai ne ka kafa adalci.

    Kai ne ka aikata adalci * da gaskiya a gidan Yakubu.

    Ku ]aukaka Yahweh Allahnmu, * ku yi sujada a matashin }afafunsa. * Tsattsarka ne shi!

    Musa da Haruna ne tsakanin firistocinsa, * Sama’ila ma na cikin masu kiran sunansa.

    Ya amsa masu * daga ginshi}in gajimare * ya yi magana da su.

Sun kiyaye dokokinsa, * shari’ar da ya ba su. * Yahweh Allahnmu, kai ne ka amsa masu.

A gunsu, kai Allah Mai Gafartawa, * wanda ka tsarkake su daga zunubansu.

Ku ]aukaka Yahweh Allahnmu, * ku yi sujada a tsattsarkan dutsensa. * Gama Yahweh Allahnmu tsattsarka ne.

Zabura ta 100

Ku yi sowa ga Yahweh, dukan duniya, * ku bauta wa Yahweh da farinciki, * ku zo gabansa da wa}a ta murna.

    Ku san dai Yahweh Allah ne. * Mai Iko Duka ne, ya yi mu. * Mu mutanensa ne, garken da yake kiwo.

    Ku shiga }ofofinsa da yin godiya, * farfariyarsa da wa}ar yabo. * Ku gode masa, ku yabi sunansa.

Gama Yahweh mai alheri ne, * }aunarsa na nan tun fil’azal, * amincinsa kuma har dukan zamanai.

Zabura ta 101

Zan yi wa}ar }aunarka da adalcinka, * Yahweh, a gare ka zan raira yabo.

Zan bayyana kammalalliyar sarautarka. * Yaushe ne za ka zo gare ni?

    Na zama da zuciya mara aibu * a cikin fâdata.

    Ban ta~a sa abu mara moriya * a gaban idanuna ba.

    Na }i sana’ar yin gumaka, * ba ta manne mani ba.

        Mai karkatacciyar zuciya ya yi nesa da ni, * ban ma yi abuta da mugu ba.

        Duk wanda ya yi tsegumin ma}wabcinsa a asirce, * na kwa~e shi.

        Mai girman kai da zuciyar alfarma, * na gama da shi.

    Idanuna a kan amintattun ’yan }asata ne, * don su zauna da ni.

    Sai mutun mai kammalallen hali ne * zai yi mani hidima.

    Mai aikata yaudara bai ta~a zama a fâdata ba, * wulli manajan }arya bai ta~a wali gaban idanuna ba.

Ina yanka dukan miyagun }asa * sai ka ce hurtuman shanu.

Masu aikata mugunta ]aya da sauran, * ina hallakawa daga birnin Yahweh.

Zabura ta 102

Yahweh, ka ji addu’ata, * bari kukana ya kai gare ka!

Kada ka juya fuskarka daga gare ni * a cikin ranar wahalata.

Ka kasa kunne gare ni, ran da na yi kira, * ka gaggauta ka amsa mani.

    Gama kwanakina suna wucewa da sauri fiye da haya}i, * }asusuwana ma suna }onewa kamar kaskon wuta.

    Zuciyata ta }one kamar ciyawa, ta yankwane, * na rame saboda Mai Cinyewa.

    Mu}amu}aina suna ciwo da nishina, * }asusuwana suna manne wa namana.

        Kamar ungulu nike a cikin daji, * na zama mujiya ta cikin kangaye.

        Bana barci, na zama kamar gwara * mai kuka a kan ]aki wuni zubut.

    Magabcina yana zagina, * Mai tonona yana yin biki da ni.

    Toka ce abincina, * daga kwallana nike samun ruwan sha.

Saboda haushinka da hushinka, * kâ ]aga ni, ka kuma jefad da ni.

Kwanakina kamar inuwar da ke }ara tsawo suke, * ina kuma yankwanewa kamar ciyawa.

    Amma kai, Yahweh, * kana sarauta tun fil’azal, * kursiyinka ma ya tabbata har abada.

    Za ka tashi, ka nuna tausayi ga Sihiyona, * gama lokacin a ji tausayinta ya yi, * i, }ayyadadden lokacin ya zo.

        Bayinka suna jin da]in duwatsunta, * suna kuma yin juyayin tur~ayarta.

        Al’ummai za su ji tsoron sunanka, * Yahweh, * dukan sarakunan duniya ma za su ji tsoron ]aukakarka,

            Loton da Yahweh ya sake gina Sihiyona, * ya bayyana gare ta da ]aukakarsa,

                 loton da ya ji addu’ar matalauta, * bai ma }yale ro}onsu ba.

            Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, * don mutanen da za a halitta su yabi Yahweh.

        “Yahweh ya zuba ido daga can tsattsarkan wurinsa, * daga sammai ya dubo }assai,

        don ya ji nishin bursunoni, * ya ’yanto wa]anda aka yanke wa hukuncin kisa,

    domin a ji shelar sunan Yahweh a Sihiyona * da yabonsa a {udus,

    sa’ad da mutane ke taruwa, * tare da sarakuna don su bauta masa.”

Yahweh ya raunana }ar}ona da ikonsa, * Allahna ya gajarta kwanakin moriyata.

“Kada ka sure ni kamin rabin kwanakina, * da yake shekarunka ba su da iyaka.”

    Tuntuni kâ sa harsashin duniya, * sammai kuma aikin hannuwanka ne.

    Su za su hallaka, amma kai za ka wanzu, * dukansu za su }o}e kamar tufafi.

    Kana sauya su kamar riguna, * su ma suna shu]ewa.

Amma kai kana zama yadda kake, * shekarunka ma ba za su }are ba.

’Ya’yan bayinka za su zauna a tabbace, * jikokinsu kuma za su kafu a gabanka.

Zabura ta 103

Yabi Yahweh, ya raina! * duk jikina, yabi sunansa mai tsarki!

Yabi Yahweh, ya raina! * kada ka manta da dukan alherinsa,

    shi wanda ke gafarta dukan muguntarka, * wanda ke warkad da dukan cututtukanka,

    wanda zai ku~utad da ranka daga Rami, * wanda zai yi maka rawani da }auna da rahama.

    Shi ne wanda zai wadata dauwamarka da kyau, * lokacin da za a sabunta }uruciyarka kamar maiki.

        Yahweh ne ke tabbatad da sakamako * da adalci ga dukan wa]anda ke cikin }unci.

        Ya gaya wa Musa hanyoyinsa, * ayyukansa kuma ga ’ya’yan Isra’ila.

            Yahweh mai tausayi ne da jin}ai—Arahamani Arahimi, * sarkin ha}uri ne da yalwar }auna.

            Ba zai yi tankiya ko surutu kullun ba, * ba kuwa zai ri}e hushinsa har abada ba.

                 Ba bisa ga zunubanmu yake yin ma’amilla da mu ba, * bai ma saka mana gwalgwadon miyagun ayyukanmu ba.

                      Amma kamar yadda sama ke birbishin duniya, * haka ne girman tausayinsa yake ga masu tsoronsa.

                 Kamar yadda gabas ke nesa da yamma, * haka ne yake nesanta kansa daga ayyukan tawayenmu.

            Kamar yadda uba ke tausayin ’ya’yansa, * haka ne Yahweh ke jin tausayin masu tsoronsa.

            Domin ya san abin da aka yi mu da shi, * ya tuna mu yam~u ne kawai.

        Jikan Adamu, kwanakinsa kamar ciyawa ne, kamar furan jeji, haka yake yin zamaninsa.

        Da iska ta ka]a shi, sai ya shu]e, * gidansa baya }ara tunawa da shi.

    Amma }aunar Yahweh tun fil’azal take, * har abada za ta zauna kuma ga masu tsoronsa.

    Alherinsa zai bi jikokin jikoki, * ga wa]anda ke kiyaye yarjejeniyarsa, * suke kuma tunawa da cika ka’idondinsa.

    Ko da yake Yahweh ya kafa kursiyinsa a sama, * da sarautarsa yake mulkin komai.

Ku yabi Yahweh, ku mala’ikunsa, * jarumawa }arfafa, ku cika umurninsa, * kuna sauraren muryar maganarsa.

Ku yabi Yahweh, dukan sojojinsa, * da wakilai masu hidima wa]anda ke aikata nufinsa.

Ku yabi Yahweh, dukan ayyukansa, * a dukan wurare, ku talakawansa. * Halelu-Yahweh, ya raina!

Zabura ta 104

Halelu-Yahweh, ya raina!

Yahweh Allahna, kai mai girma ne }warai, * kana yafe da kwarjini da ]aukaka!

    Kâ lullu~e jikinka da hasken rana kamar riga, * kâ warware sammai kamar tanti.

    Shi ne wanda ya tara ruwa a rumbunansa na sama, * yâ sa karusansa a kan gajimarai,

yana tafiya da fukafukai mi}a}}u, * iska tana kai sa}onsa, * halshen wuta mai ci ne mai hidimarsa,

    wanda ya kafa }asa a kan harsashinta, * don ta tsaya daram ba tare da jijjiguwa ba.

    Kâ rufe ta da teku kamar riga, * har ruwaye sun tsaya bisa duwatsu.

        Amma da jin tsawarka sun gudu, * da jin }arar aradunka sun ranta a noman kare.

    Wasu sun gudu zuwa samar duwatsun, * amma wasu sun gangara zuwa }al}ashin }asa, * wurin da ka tanada masu.

    Kâ sa iyaka da ba za su }etare ba, * don kada su sake rufe }asa.

        Yâ saki idanun ruwa da }oramu, * don su ri}a malala a tsakanin duwatsu,

        suna shayar da kowace dabbar jeji, * don jakan daji su jika makwogaronsu.

        Kusa da su tsuntsayen sama ke zama, * daga tsakkiyarsu hankaki suke surutu.

            Yana ba duwatsu ruwa daga rumbunan tara ruwansa na sama, * daga matararsa }asa ke wadata da ruwa.

                 Yana sa ganyaye su tsiro don dabbobi, * da ciyawa don shanu masu hu]ar gona.

                      I, yana ba da hatsi daga }asa, * da abinshan inabi ya faranta zuciyar mutun.

                           I, yana sa fuska mai }iba haske, * da abinci yake }arfafa zuciyar mutun.

                      An ba itatuwan Yahweh ruwa sosai, * su al’ul na Labanan wa]anda ya dasa,

                 inda tsuntsaye ke yin she}arsu, * shamuwa ita kam, icen fir ne gidanta.

                      Dogayen duwatsu na bareyin daji ne, * kogunan duwatsu kuma na remaye.

                 Wata na canzyawa a kan kari, * rana ta san lokacin da za ta fa]i.

                      Da almuru ya iso, sai dare ya yi, * sannan ne dukan namun jeji ke zagawa.

                           Kuyakuyan zakoki suna ruri don ganimarsu, * suna neman abin sa wa baka daga wurin Allah.

                      Da rana ta fito, sai su janye jiki, * su kwanta a ma~oyunsu.

                 Sai mutun ya fita wurin leburancinsa, * ya dinga hu]a har maraice.

            Yaya yawan aikinka yake, Yahweh! * Da Hikima a gefenka kâ yi dukansu, * duniya cike take da halittarka.

        Uban Gidan Teku, * mai tsawo, mai fa]i,

        kai ne ka halicci masu iyo ba iyaka, * rayayyun dabbobi, manya da }anana,

        kâ yi jirage don tafiya, * da Lawiyatan, wanda ka yi don ka yi wasa da shi:

    Dukansu suna dubanka, * don ka ba su abincinsu a kan kari.

        In ka ba su, sukan tara, * in ka bu]e hannunka, ya Mai Nagarta, sukan wadatu.

        Amma da ka kau da fuskarka, sai su suma, * in ka ]auke ruhunka, sai su mutu, * su koma yam~unsu.

    Ka aiko da ruhunka, a sake halittarsu, * ka sabunta fuskar }asa.

Bari ]aukakar Yahweh ta tabbata har abada, * da ma Yahweh ya gamsu da aikinsa!

    Da ya kalli duniya sai ta gigice, * in ya ta~a duwatsu ma suna yin haya}i.

    Bari in yi wa Yahweh wa}a duk tsawon rayuwata, * in yabi Allahna matu}ar ina numfashi.

Da wa}ata ta shiga kunnensa, * zan yi farinciki da Yahweh.

Bari masu zunubi su ~ace daga duniya, * miyagu ma kada su sake wanzuwa.

Halelu-Yahweh, ya raina!



Zabura ta 105

Ku yi wa Yahweh godiya, ku kira sunansa, * ku sanar da ayyukansa a cikin al’ummai!

Ku yabe shi, ku raira masa wa}a, * ku wallafa labarun al’ajibansa.

Ku yi alfahariya da sunansa tsattsarka, * masu neman Yahweh, ku faranta zukatanku.

Ku nemi Yahweh da ikonsa, * kasancewarsa ta dindindin za ku bi]a.

Ku tuna da al’ajiban da ya yi, * da alamomi da hukuntan da bakinsa ya furta,

ku jikokin baransa Ibrahimu, * da ’ya’yan Yakubu za~a~~ensa!

    Gama shi ne Yahweh Allahnmu, * ikonsa yana bisa dukan duniya.

    Yana sane da yarjejeniyarsa har abada, * ka’idar da ya }ulla don tsara biye da tsara har dubu.

    Ya yi ta da Ibrahimu, * ya ma sabunta ta da Isiyaku.

        Domin ya tabbatad da ita ga Yakubu kamar a matsayin shari’a, * ga Isra’ila kuwa kamar yarjejeniya ce ta har abada.

        Cewa: “Kai zan ba }asar, * tuddan Kan’ana za su zama abin gadonku.”

    Sa’ad da ba su da yawa, * ba}i kima ne a cikinta,

    suna yawo daga wannan al’umma zuwa wata, * daga wannan sarauta da mutane zuwa wata,

bai bar wani ya zalunce su ba, * saboda su ma har sai ya tsawata wa sarakuna,

ya ce: “Kada ku ta~a shafaffen sarkina, * kada kuma ku yi wa annabawana lahani!”

    Daga nan sai ya sa aka yi yunwa a }asar, * ya karya kowane karan hatsi.

        Ya aike masu da wani mutun, * Yusufu da aka sayar bawa.

        Sun ]aure }afafunsa da marî, * wuyansa kuma ya sha sar}a,

            sai lokacin da maganarsa ta kai gaban Fira’auna, * wanda maganar Yahweh ta tabbata ta wurinsa.

            Ya aika sarki ya sake shi, * shugaban mutane ya ba shi ’yanci.

                 Ya na]a shi shugaban fâdarsa, * mai sarrafa duk abin da ya mallaka,

                 don ya koya wa fadawansa, * ya koya wa dattawansa hikima.

                      Sannan Isra’ila ya zo Masar, * Yakubu kuma ya ba}unci }asar Hamu.

                      Mai Duka ya ri~an~aya mutanensa, * sun yalwata fiye da abokan hamayyarsu.

                      Ya juye zukatansu su }i mutanensa, * su yaudari bayinsa.

                           Sai ya aiko Musa bawansa, * da Haruna wanda ya za~a.

                           Sun aikata alamominsa a jeji, * da alamunsa a }asar Hamu.

                      Ya aiko duhun da ya duhunta, * ba su iya ganin aikinsa.

                      Ya mai da ruwan shansu jini, * ya karkashe kifayensu.

                 Ya cika }asarsu da kwa]i, * har ]akunan sarakunansu.

                 Ya yi magana, ya sa ]umbin kudaje, * da }war}wata a ko’ina.

            Ya sauko masu }an}ara maimakon ruwa, * an yi ta rabka tsawa a }asarsu.

            Ya rabke kuringar inabi da itatuwan ~aurensu, * ya kakkarya itatuwan tuddansu.

        Ya yi magana, ya kawo fara, * ga ]ango nan ba iyaka.

        Sun cinye kowane ganye a }asar, * sun kuma cinye amfanin gonakinsu.

    Ya karkashe kowane ]an fari a }asarsu, * kowace yabanyar fari ta haifuwarsu.

Daga nan ya fito da su da azurfa da zinari, * ba wani kumama a cikin kabilunsa.

Masar ta yi murna da tafiyarsu, * domin tsoronsu ya kama su.

    Ya baza gajimare don ya rufe su, * da wuta don ta haskaka daren.

        Sun nema ya kawo masu fakara, * da alkama daga sama ya }osad da su.

            Ya buga dutse, ruwa ya malalo, * ya gudano kamar kogi a busasshiyar }asa.

        Domin ya tuna da tsattsarkar ka’idarsa * da ya yi da Ibrahim baransa.

    Ya zaro mutanensa da murna, * za~a~~unsa suna tafe suna wa}a.

Daga nan ya ba su }asashen al’ummai, * suka }wace har da dukiyar mutane,

muddun suna kiyaye dokokinsa, * da tsare shari’o’insa.

Halelu-Yah!



Zabura ta 106

Halelu-Yah!

                      Ku gode wa Yahweh don mai alheri ne, * gama }aunarsa har abada ce.

                      Wa ke iya fa]in ikon Yahweh? * ko furta dukan yabonsa?

Albarka ga masu lura da adalci, * da ke aikata gaskiya a kowane lokaci.

    Ka tuna da ni, Yahweh, * da sonka mai }arfi, * ka taimake ni da cetonka,

    don in ci arzikin za~a~~unka, * in ji da]in murna ta jama’arka, * in kuma yi alfahari da gâdonka.

Mun yi zunubi kamar kakanninmu, * mun yi }eta da ashararanci.

    Bayan Masar, kakanninmu ba su fahinci al’ajibanka ba, * sun mance da yawan }aunarka.

    Daga Bahar Kyamare ne suka yi wa Ma]aukaki tawaye, * duk da ya cece su saboda sunansa, * don ya sa su kan ikonsa.

        Ya tsawata wa teku, * kyamare ya bushe, * ya sa sun ratsa zurfin sai ka ce tamkar hamada.

        Ya cece su daga hannun ma}iyi, * ya sa sun tsira daga hannun magabci.

        Ruwaye sun rufe abokon gabarsu, * ba ko ]ayansu da ya rage.

        Sannan ne suka gaskanta da maganarsa, * suka yi wa}o}in yabonsa.

    Nandanan kuwa sai suka mance da ayyukansa, * ba su jira shawararsa ba.

    Sun nuna matu}ar ~acin ransu a jeji, * suna gwada Allah a hamada.

    Duk da haka ya biya masu bukatarsu, * ya kori yunwa daga ma}ogwaronsu.

        Sun yi }yashin Musa a sansanin, * da Haruna mai tsabtan nan na Yahweh.

            Sai }asa ta bu]e ta ha]iye Datan, * ta kuma binne bangaren Abiram.

            Wuta ce ta babbake ~angarensu, * harsunan wuta suka lashe mamugunta.

                 Suka mulmula ]an maraki a Horeb, * suka yi wa sura mai narkewa sujada.

                 Suka musaya addininsu * da kamannin sa mai cin ciyawa.

                      Sun mance da Allah Macecinsu, * da ya yi ayyuka masu girma a Masar,

                      al’ajibai a }asar Ham, * da alamomin bantsoro a Bahar Kyamare.

                           Sai ya ce zai hallaka su, * ba don Musa za~a~~ensa ba,

                           wanda ya tsaya tsaka a gabansa, * yana tausar hushinsa don kada ya hallaka su.

                           Sai suka rena }asar da suka nema, * ba su gaskanta da maganarsa ba.

                           Amma suka yi gunaguni a bukkokinsu, * ba su saurari maganar Yahweh ba.

                      Don haka ya ]auke hannunsa a kansu, * ya tunku]a su jeji,

                      ya hargitsa zuriyarsu a cikin al’ummai, * ya warwatsa su a }asashen waje.

                 Suka gama kai da Ba’al na Feyor, * suka yi bikin bautar matattu.

                 Suka fusata shi da ayyukansu, * sai alloba ta afko masu.

            Sai Finihas ya tashi tsaye ya yi ro}o, * har aka tsai da allobar.

            An sanya wannan ga kirkinsa * daga zamani zuwa zamanu har abada.

        Suka fusata shi a ruwayen Mariba, * sai da Musa ya sha wuya saboda su,

        don sun yi wa ruhunsa tawaye, * sai ya fa]i abin da bai kamata ba.

    Ba su hallaka mutanen ba, * yadda Yahweh ya umurce su.

    Amma sun aurayya da al’ummai, * suna koyon al’adunsu.

        Sun kuma bauta wa gumakansu, * da suka zamam masu tarko.

        Suna mi}a ’ya’yansu maza * da mata ga aljanu.

        Suna zub da jinin adalai, * jinin ’ya’yansu maza da mata,

        da suka yanka wa gumakan Kan’ana, * suka }azanta }asar da jini mai yawa.

        Sun }azanta kansu da ayyukansu, * suna yin zina wajen bajirewarsu.

    Sannan hushin Yahweh ya yi }una a kan jama’arsa, * sai ya }i abin gâdonsa.

    Ya bashe su a al’ummai, * don ma}iyansu su mulke su.

    Magabtansu sun matsa masu lamba, * sai da suka }as}antu a hannunsu.

Sau da yawa ya cece su, * amma kuma suna ci gaba da taurin kansu * sai da mugun nufinsu ya komo masu.

    Sai dai ya tausaya wa ~acin ransu, * yana jin kukansu.

    Ya tuna yarjejeniyarsa da su, * yana bi da su da yalwar alherinsa.

Ya ba su rahamomi masu yawa, * a gaban dukan iyayengijinsu.

Ka cece mu, Yahweh Allahnmu, * ka tattaro mu daga al’ummai,

don mu gode wa sunanka mai tsarki, * mu ]aukaka shi ta yabonka.

Yabo ga Yahweh Allah na Isra’ila, * tun fil’azal har abada! * Bari dukan mutane ma su ce, “Amin”.

Halelu-Yah!

Zabura ta 107

Ku gode wa Yahweh domin mai alheri ne, * gama jin}ansa har abada ne.

Bari ku~utattun Yaweh su ce, * shi ne ya ku~utad da su daga hannun mai zalunci.

Ya fid da su daga }asashen waje, * daga gabaci da yammaci, * daga arewaci da kuma tekun kudu.

    Sun yi yawa a jeji, * ta hamada ne suka bi, * amma ba su ga garin zama ba.

    Sun ji yunwa da }ishinruwa, * kamar ransu zai fita.

        Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

        Ya bi da su ta mi}a}}ar hanya, * sai da suka kai birnin da za su zauna ciki.

    Bari su bu]e baki su yabi jin}an Yahweh, * al’ajibansa kuma ga ’yan adan,

    domin ya }osad da ma}oshi mai jin }ishinruwa, * ya ma ci da mayunwacin ma}ogwaro da abubuwa masu kyau.

        A game da mazauna cikin ba}in duhu, * da ke ]aure da marurai masu azaba,

        domin sun tayar wa umurnan Allah ne, * sun shure shawarar Ma]aukaki,

        ya shawo kansu da wahala, * sun yi ta tuntu~e, ba mataimaki.

            Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

            Ya fito da su daga ba}in duhu, * ya karkatsa sar}o}insu.

        Bari su bu]e baki su yabi jin}an Yahweh, * al’ajibansa kuma ga ’yan adan.

        Domin ya tsintsinke }ofofin jan}arfe, * mulmulallun }arafa yana yin gunduwa da su.

            Ba su da kuzari don tawayensu, * sun shiga uku don }etar da suka yi.

            Ma}ogwaronsu ya }i kowane irin abinci, * har sun kai gab da }ofofin Mutuwa.

                 Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

                 Ya aiki maganarsa tana warkad da su, * tana warkad da maruransu.

            Bari su bu]e baki su yabi jin}an Yahweh, * al’ajibansa kuma ga ’yan adan.

            Bari su mi}a hadayun godiya, * suna }idaya alherinsa da wa}ar farinciki.

        Game da masu tafiya bahar da jirage, * suna kasuwanci hayin manyan ruwaye,

            sun ga ayyukan Yahweh, * da al’ajibansa a ruwa mai zurfi.

                  Ya yi umurni, iska ta taso, * da hadari wanda ya ]aga ra}uman ruwansa.

            Sun yi sama, sun kuwa sauka zurfafa, * bakinsu ya yi rawa saboda hatsarin.

        Sun kai sun kawo, suna tanga]i kamar bugaggu, * gwanintarsu duk ta zama ta banza.

            Sai suka yi kuka ga Yahweh cikin wahala, * ya kuwa tsamo su daga matsinsu.

            Ya sa hadiri ya yi shuru, * ya kwantad da motsin ra}uman ruwa.

            Sun yi murna da wurin ya yi tsit, * da ya yi masu jagora zuwa wurin kasuwancinsu.

        Bari su bu]e baki su yabi jin}an Yahweh, * al’ajibansa kuma ga ’yan adan.

        Bari su ]aukaka shi a taron jama’a, * a majalisar dattawa kuma su yabe shi.

    Ya sa koguna sun zama daji, * idanun ruwa sun bushe }ayau,

    }asa mai ni’ima ta koma hamada mai kanwa, * don }etar mazauna wurin.

        Ya sa jeji ya zama tabkunan ruwa, * busasshiyar }asa ta koma kandami.

            Ya zaunad da mayunwata a wurin, * sun ma kafa garin zama.

                 Sun shuka gonaki, * sun dasa garkar inabi, * sun yi girbi mai matu}ar yawa.

            Ya yi masu albarka, sun ma yawaita }warai, * bai rage yawan garkunan shanunsu ba.

        Amma ya sassafta masu, ya kau da * zalunci da hatsari da ~acin rai.

    Mai jibga wa sarakuna wulakanci, * mai sa su su yi yawo a hamada da ba hanya,

    ya kare mabukaci a }asarsa, * ya ninka kabilansu kamar tumaki.

Bari masu gaskiya su gani su ji da]i, * duk mugu kuwa ya yi tsit.

Duk mai hikima zai yi la’akari da abubuwan nan, * zai kuma yi tunani da yawan jin}an Yahweh.

Zabura ta 108

Na shirya zuciyata, ya Allah,* zan yi wa}a in yabe ka.

Ki falka, zuciyata! * Ku falka, molona da garayata! * Zan farkad da safiya!


Zan gode maka a cikin jama’a, Yahweh, * zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Mai Girma.

Domin }aunarka tana birbishin sammai, * amincinka kuma ya kai har sararin sama.

    Tsawonka ya kere sammai, ya Allah, * ]aukakarka kuma ta shafe dukan duniya.

    Don a ku~utad da }aunatattunka, * ka ba ni rinjaye da nasara da hannunka na dama.

        Allah ya fa]a daga tsattsarkan gidansa, * “Zan raba Shakem, * in kuma auna kwarin Sukkot.

        Gileyad nawa ne, har da na Manassa, * Ifraimu ne hular kwanona, * Yahuda kuma sandan sarautata.

        Mowab ne bangajin wankina, * a kan Edom ne zan aza takalmina, * a Filistiya zan yi kirarin nasara.”

    Wa zai kai ni Birnin Mafaka? * Wa zai ba ni gadon Edom?

    Amma kai, ya Allah, za ka husata da mu? * ba za ka sake fita da sojojinmu ba?

Ka ‘yanta mu daga abokin gaba, * tun da yake taimakon mutane banza ne.

Da ikon Allah za mu ci nasara, * shi ne zai tattake magabtanmu.

Zabura ta 109

Ya Allahna, * kada ka bebanta ga wa}ata.

    Domin bakin miyagu * da bakin mayaudara * duk sun wo mani caa.

        Suna yanka mani }arya da halshensu, * da kalmomin }iyayya kuma suna kewaye ni.

        Suna ya}ina ba dalili, * maimakon }auna da nike masu * suna yin tsegumi.

    Suna zargin addu’ar da nike yi masu, * suna rama mani alheri da mugunta, * }iyayya da soyayyata.

        Ka ]ora Mugun a kansa, * bari She]an ya tsaya a hannun damansa.

        In ana yi masa shari’a, a same shi da laifi, * addu’arsa kuma ta zama wani laifin.

        Kwanakinsa su gaza, * wani ya ]auki matsayinsa.

            ’Ya’yansa su zama marayu, * matarsa kuwa gwauruwa.

            ’Ya’yansa su yi yawon bara, * mai aunawa ya }ayyade ku]in gidansa.

        Mai bin bashi ya }wace dukan kayansa, * ba}i kuma su wawashe amfaninsa.

        Kada kowa ya yi masa alheri, * ko ya ji tausayin marayun ’ya’yansa.

            A hana shi madauwamin rai, * a kuwa goge sunansa daga zamani mai zuwa.

                 Bari a rubuta zunubin ubansa * wurin Allah Yahweh, * kada a shafe zunubin uwarsa.

                 Wa]annan zunubai su kasance a gaban Yahweh kullun, * loton da yake shafe tunawa da shi a duniya,

                 tun da baya tunanin nuna }auna, * sai ba}antawa gajiyayye da mabukaci, * har yana kashe mai ~acin zuciya.

                      Tun da yana so la’ana, * ta koma kansa.

                      Tun da yana }in albarka, * ta yi nesa da shi.

                 Ya sa la’ana kamar kaftani, * ta kuwa ratsa jikinsa kamar ruwa, * kamar mai ta game }asusuwansa.

                 Bari ta zama kamar tufar da ta lullu~e shi, * kamar ]amarar da ta ]aure shi kullun.

            Ka }ara kunyar matseguntana * sau ]ari, Yahweh, * da ta masu yi mani ba}ar magana.

        Sai ka zo, Yahweh Ubangijina, * ka aika al’ajibi domina, * saboda sunanka managarci.

        Da alherinka ka cece ni, * domin ni gajiyayye ne mabukaci, * a cikina kuma zuciyata ta soku.

            Na yi kama da inuwa dab da fa]in rana, * ina ta wucewa, * }uruciyata ta kare, na tsufa.

            Gwiwowina sun yi sanyi saboda hana kai abinci, * dâ ni }osasshe ne, amma yanzu na rame.

            Ga masu zuwa wurina * na zama abin zagi, * da sun gan ni sai su ka]a kai.

        Ka taimake ni, Yahweh Allahna, * ka cece ni yadda ya dace da }aunarka,

        don su san wannan aikin hannunka ne, * wanda kai, Yahweh, ka aikata.

    Bari su la’anta, * in dai kana sa albarka.

    In sun yun}uro su }as}anta, * amma bawanka ya yi farinciki.

    Bari matseguntana su sa kaftanin wulakancinsu, * su rufe kansu da kunya kamar mayafi.

Zan yabi Mai Girma da bakina, * a tsakkiyar dattawa zan yabe shi,

domin yana tsaya wa hannun daman mabukaci, * don ya cece shi daga alkalin.

Zabura ta 110

Yahweh ya ce da ubangijina,

“Zauna a kursiyin dama da ni. * Na mai da magabtanka kujera, * matashin }afafunka.”

    Ya }era sandarka mai nasara, * Yahweh na Sihiyona ya ko]a ta.

    Shi Ikonka ne a cikin ya}in magabtanka, * {arfinka kuma a ranar nasararka.

    Tsattsarkan Mai Tallafinka ya bayyana, * Asubahin rayuwarka * Ra~ar }uruciyarka.

        Yahweh ya rantse, * ba ma zai canza nufinsa ba:

            “Kai firist ne na Madauwami, * bisa ga alkawalinsa,

        hakikantaccen sarkinsa, ubangijina, * yadda hannun damanka ya shaida.”

    Ya runtumi sarakuna a ranar hushinsa, * ya karya al’ummai.

    Ya jibge gawarwaki, * ya rafke kawuna * a bisa }asa mai fâ]i.

Mai Za~en Sarakuna ya na]a shi, * Ma]aukakin Zati ya ]aga matsayinsa.

Zabura ta 111

Halelu-Yah!

Zan yi godiya ga Yahweh * da dukan zuciyata * a majalisar masu gaskiya da cikin taron jama’a.

    Ayyukan Yahweh manya ne, * don duk masu jin da]insu su yi binbininsu.

        Ayyukansa suna da girma da ]aukaka, * alherinsa na ]orewa har abada.

        Ya yi al’ajiban da ba za a manta da su ba, * shi ne Yahweh Arahamani Arahimi.

            Yana ba masu tsoronsa abinci, * ya tuna da yarjejeniyarsa ta tuntuni.

            Ta ayyukansa yake nuna wa jama’arsa ikonsa, * yana ba su gallar al’ummai.

        Ayyukan hannuwansa su ne gaskiya da aminci, * dukan dokokinsa amintattu ne.

        Sun kafu tuntuni har abada, * bisa tushen gaskiya da aminci.

    Ya aika fansa ga jama’arsa, * ya kafa yarjejeniyarsa har abada, * sunansa tsattsarka ne da mai bantsoro.

Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima, * duk masu nemanta sun fa’inci Mai Nagarta.

Bari a yabe shi har abada!

Zabura ta 112

Halelu-Yah!

Albarka ga mai tsoron Yahweh, * wanda ke jin da]in umurnansa.

Zuriyarsa za ta yawaita a }asar, * gidan mai gaskiya zai yi albarka.

    Akwai wadata da dukiya suna gidansa, * alherinsa zai ]ore har abada.

    Ga masu gaskiya, a cikin Duhu, Ranar Asuba za ta keto, * ta Mai Jin}ai, Mai Tausayi, Mai Adalcin nan.

        Mutumin kirki baya hana rance, * yana yin al’amuransa da adalci.

        Ba zai ta~a yin tuntu~e ba, * za a ri}a tuna mai gaskiya har abada.

    Baya jin tsoron mugun labari, * zuciyarsa ba ta falgaba, don yana dogara ga Yahweh.

    Ba falgaba a zuciyarsa, baya jin tsoro, * yana murna kullun, yana yi wa magabtansa dariya.

Yana ba mabukata hannu sake, * alherinsa na ]orewa, * za a }ara masa girma da mutunci.

Mugu yana yin kallon kishi da ~acin rai, * yana cizon ha}oransa da kuka, * gidajen miyagu za su warwaje.

Zabura ta 113

Halelu-Yah!

Ku yabi ayyukan Yahweh, * ku yabi sunan Yahweh.

Yabo ga sunan Yahweh, * daga yanzu har abada!

Yabo ga sunan Yahweh, * daga fitowar rana zuwa fa]uwarta!

    Yahweh ne saman dukan al’ummai, * bisa sammai ]aukakarsa take.

        Wa ke kama da Yahweh Allahnmu, * da ke da kursiyi a sama,

    wanda ke karkatowa daga sama * don ya duba }asa.

Yana ]aga matalauci daga tur~aya, * daga juji yake ta da mabukaci,

don ya zaunad da shi tare da sarakuna, * i, da sarakunan jama’arsa.

Yakan ba mara ’ya’ya gida, * ta zama uwar ’ya’ya cike da murna.

Zabura ta 114

Bayan fitowar Isra’ila daga Masar, * Yakubu daga masu }eta,

}asar Yahuda ta zama tsttsarkan wurinsa, * Isra’ila kuma abin mulkinsa.

    Tekun Araba ya gan shi, ya gudu, * Kogin Urdun ya koma da baya.

    Duwatsu sun yi tsalle kamar raguna, * tuddai kuma kamar ’ya’yan bareyi.

    Me ya same ka, ya Teku, har ka gudu? * Urdun, don me ka ja da baya?

    Ku duwatsu, don me kuke yin tsalle kamar raguna? * ku ma tuddai kamar awaki?

Ki yi makyarkyata, }asa, a gaban Ubangiji, * da zuwan Allah na Yakubu,

wanda ke canza dutse zuwa tafkin ruwa, * da ma}yashi zuwa ma~u~~ugan ruwa.

Zabura ta 115

Ba don halinmu ba, Yahweh, * ba don halinmu ba,

    amma don sunanka * ka nuna ]aukakarka,

    saboda }aunarka, * da amincinka,

don kada al’ummai su ce, * “Ina Allahnsu yake?”

    Ko da shi ke Allahnmu a sama yake, * yana yin duk abin da ya ga dama.

    Gumakansu su ne azurfa da zinariya, * aikin hannuwan mutun.

        Suna da baki, amma ba sa magana.

            Suna da idanu, amma ba sa gani.

            Suna da kunnuwa, amma ba sa jin murya.

                 Suna da hanci, amma ba sa jin }amshi.

                 Suna da hannuwa, amma ba sa ta~awa.

            Suna da }afafu, amma ba sa tafiya.

            Ta ma}ogwaronsu, ba sa iya yin amo.

        Masu yinsu za su zama kamarsu, * da kowa da ya dogara da su.

            Ya Isra’ilawa, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

            Ya gidan Haruna, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

            Masu tsoron Yahweh, ku dogara ga Yahweh, * Mataimakinku ne da Shugabanku!

        Yahweh ya yi wa kursiyimmu albarka,

            ya yi wa gidan Isra’ila albarka,

            ya yi wa gidan Haruna albarka.

                 Ya yi wa masu tsoronsa albarka,

                 manya duk da }anana.

            Yahweh ya ri~an~anya ku,

            ku da ’ya’yanku.

        Yahweh ya yi maku albarka, * wanda ya yi sama da }asa.

    Birbishin sama na Yahweh ne, * amma ya ]ora ’yan adan bisa duniya.

    Matattu ba sa yabon Yahweh, * ko dukan masu gangara wa Kurkuku.

Amma mu za mu yabi Yahweh, * daga yanzu har abada.

Halelu-Yah!


Zabura ta 116

Saboda }aunar Yahweh gare ni, * ya ji ro}ona don jin}ai.

I, ya kasa kunne gare ni, * lokacin da nike kira.

    Igiyoyin Mutuwa sun nanna]e ni, * jakadun Shawol sun same ni.

    Da damuwa da ~acin rai sun same ni, * amma na kira sunan Yahweh:

        Ina cewa, “Ina ro}onka, Yahweh, * ka fanshi raina.”

    Arahamani, shi ne Yahweh mai gaskiya, * Allahna Arahimi ne.

    Yahweh ne mai kiyaye mai sau}in kai, * an }as}anta ni, amma ya cece ni.

        Ka koma wurin hutunka, ya raina, * gama Yahweh ya kyauta maka.

        Gama an fanso ka daga Mutuwa, ya raina, * idona daga Hawaye, * }afata kuma daga gudun Hijira.

            Zan yi tafiya a gaban Yahweh * a Lambun Rayayyu.

        Na yi aminci ko da yake an runtume ni, * ko da yake Masifa tana wulakanta ni.

        Saboda tunzurina na zaci, * “Kowane mutun ma}aryaci ne.”

    Ta yaya zan mayas wa Yahweh * da dukan alherin da yake yi mani?

    Zan ]auki }o}on ceto, * in yi kira da sunan Yahweh.

    Zan cika wa’adodina ga Yahweh * a gaban dukan jama’arsa.

        Mutuwar masu bauta wa Yahweh * babbar daraja ce a gare shi.

    Hakika, Yahweh, * ni bawanka ne.

    I, ni bawanka ne, * amintataccen ]anka, * ka kwance mani ]aurina.

    Yahweh, zan mi}a maka hadayar godiya, * ina kiran sunanka.

Zan cika wa’adodina gun Yahweh, * a gaban dukan jama’arsa,

a farfajiyun gidan Yahweh, * a tsakkiyar Birnin {udus.

Halelu-Yah!



Zabura ta 117

Ku yabi Yahweh, dukan al’ummai, * ku ]aukaka shi, ku dukan mala’iku.

Gama }aunarsa gare mu da girma take, * amincin Yahweh har abada ne.

Halelu-Yah!



Zabura ta 118

Ku yabi Yahweh mafi nagari, * }aunarsa har abada ce.

    Bari Isra’ila ya ce, * “{aunarsa har abada ce.”

    Bari gidan Haruna ya ce, * “{aunarsa har abada ce.”

Bari masu tsoron Yahweh su ce, “{aunarsa har abada ce.”

    Daga bakin Kurkuku na kira Yahweh, * ya ji ni daga sararin sama.

Yahweh na tare da ni, bana jin tsoro, * menene mutun ya iya yi da ni?

    Yahweh na tare da ni, Babban Jarumina, * zan ga bayan magabtana.

    Gwamma neman mafaka wurin Yahweh * da dogara ga mutun.

Gwamma neman mafaka wurin Yahweh * da dogara ga sarakuna.

    Dukan al’ummai sun kewaye ni, * amma da sunan Yahweh na mai da lo~arsu abin tarihi.

    Sun matsa mani lamba, * amma da sunan Yahweh na mai da lo~arsu abin tarihi.

    Sun yayya~e ni kamar }udan zuma, * amma da sunan Yahweh na mai da lo~arsu abin tarihi.

        Ka angaje ni don in fa]i, * amma Yahweh ya taimake ni.

        Yahweh mafakata ne da marayata, * yana sa ni cin nasara.

            Daga alfarwar masu nasara * ana ta yin sowar bangirma.

            Hannun dama na Yahweh ya yi nasara, * hannun daman Yahweh ya sami ]aukaka, * hannun dama na Yahweh ya yi nasara.

        Ban mutu ba, amma na rayu, * don in ba da labarin ayyukan Yahweh.

        Yahweh ya yi mani horo mai tsanani, * amma bai sallama ni ga Mutuwa ba.

    Ku bu]e mani }ofofin nasara, * zan shiga in yabi Yahweh.

    {ofar ta Yahweh ce, * sai maciya nasara su shiga.

Na gode maka saboda rinjayena, * kâ ba ni nasara.

    Dutsen da magina suka }i * shi ne ya zama harsahin gini.

    Wannan aikin Yahweh ne, * abin mamaki ne kuma a idanunmu.

Yahweh ne ya yi ranan nan, * mu yi murna, mu yi farinciki da shi.

    Muna ro}onka, Yahweh, ka ba mu nasara, * muna ro}onka, Yahweh, ka ba mu arziki.

Albarka ga wanda ya shiga da sunan Yahweh, * muna yi maka albarka a gidan Yahweh, * Allah Yahweh ya haskaka mu.

    Ku daza rassa a masujada, * ku yi wa }ahonin bagadi ado.

    Kai ne Allahna, na gode maka, * ya Allahna, ina ]aukaka ka.

Ku yabi Yahweh mafi nagarta, * }aunarsa har abada ce.

Zabura ta 119

1-8 a

Masu albarka ne kammalallu a hanyarsu, * suna tafiya bisa ga shari’ar Yahweh.

Masu albarka ne wa]anda ke ri}e shara]unsa, * suna binsa da dukan zuciyarsu.

Basa yin mugunta, * amma suna bin hanyoyinsa.

Kâ yi doka * a kiyaye umurnanka da himma.

Inâ ma a ce an daidaita hanyata * don in kiyaye ka’idondinka.

Sannan ba zan ji kunya ba * zan fuskanci dukan dokokinka.

Ina yabon ka saboda adalcin zuciyarka, * lokacin da nike koyon hukuntanka.

Zan kiyaye ka’idodinka, * ya Madauwamin Mai Girma, * kada ka yashe ni.

9-16 b

Ta yaya saurayi zai zauna da tsarki? * Ta yin tafiya bisa ga maganarka.

Ina nemanka da dukan zuciyata, * kada ka bari in bau]e wa dokokinka.

Ina ri}e alkawalinka a zuciyata, * don kada in yi maka zunubi.

Albarka gare ka, Yahweh! * Ka koya mani ka’idodinka.

Da le~unana nike shelar * dukan kalmomin da bakinka ke fa]i.

Ina jin da]in bin shara]unka, * fiye da dumbin wadata.

Ina ta yin nazarin umurnanka, * ina bimbinin hanyoyinka.

Ina jin da]in ka’idodinka, * ban ta~a manutuwa da kalmominka.

17-24 g

Ka kyauta wa bawanka don in rayu, * in kuma kiyaye maganarka.

Ka bu]e idanuna don in kalli * al’ajiban shari’arka.

Ba}o ne ni a duniya, * kada ka ~oye mani dokokinka.

Raina yana jira da dokin * hukuntanka a kullun.

Ka tsawata wa la’anannun masu izgilanci, * da ke bau]e wa dokokinka.

Ka ]auke mani zargi da wulakanci, * domin ina kiyaye shara]unka.

Duk da yake ’yan iska na zaune suna yi da ni, * bawanka yana tunani a kan ka’idodinka.

Shara]unka suna faranta mani rai, * su ne ma mashawartana.

25-32 d

Wuyana yana manne wa }ura, * ka raya ni bisa ga alkawalinka.

Na ba da labarin tafarkinka, kana saurarena, * ka koya mani ka’idodinka.

Ka sa in gane hanyar umurnanka, * don yin nazarin al’ajibanka.

Ina ru]ewa don ~acin rai, * ka agaje ni bisa maganarka.

Ka raba ni da hanyar }arya, * ta wurin shari’arka ka yi mani jin}ai.

Na za~i hanyar gaskiya, * ina girmama hukuntanka.

Na manne wa shara]unka, * Yahweh, kada ka kunyata ni.

Zan tsere a kan hanyar dokokinka, * in ka fâ]a]a fahintata.

33-40 h

Ka koya mani hanyar ka’idodinka, * Yahweh, * don in kiyaye su kamar dukiya.

Ka ba ni hangen nesa don in kiyaye shari’arka, * in kuwa bi ta da dukan zuciyata.

Ka bi da ni cikin dokokinka, * domin ina jin da]insu.

Ka juya zuciyata ga shara]unka, * ba ga ribar cuta ba.

Ka kau da idanuna daga kallon gumaka, * ka raya ni da ikonka.

Ka cika alkawalinka ga bawanka, * don a gaskiya ina jin tsoronka.

Ka kau da zargina domin ina girmama ka, * gama hukuntanka nagargattu ne.

Dubi yadda nike marmarin umurnanka, * ka raya ni da adalcinka.

41-48 w

Yahweh, bari }aunarka ta zo mani,* cetonka kuma bisa ga alkawalinka.

Zan ba da amsa ga mai zargina, * don na dogara ga maganarka.

Kada ka kauda zancen gaskiya daga bakina, * ya Madauwami Mai Girma! * Ina jiran umurnanka.

Ka sa in bi shari’arka, * ya Madauwami, * har abada.

Bari in yi tafiya da ’yanci, * lokacin da nike bin umurnanka.

Bari in yi shelar shara]unka * a gaban sarakuna, * ba tare da jin kunya ba.

Ina jin da]in dokokinka, * wa]anda na }auna ne.

Zan ]aga hannuwana * bisa ga dokokinka da nike }auna, * ina yin nazari kuma a kan ka’idodinka.

49-56 z

Ka tuna da maganarka ga bawanka, * wadda ka sa in sa zuciya a gare ta.

Wannan ita ce ta’aziya cikin wahalata, * domin maganarka ke raya ni.

Masu izgilanci suna yi mani ba’a, * ya Madauwami Mai Girma, * amma ban kauce daga shari’arka ba.

Da nike tunawa da hukuntanka na tuntuni, * Yahweh, na ta’azantu.

Na hassala * saboda miyagun da ke }yale shari’arka.

Ka’idodinka sun zama matserata * a cikin gidan da nike ba}unci.

Da dare ina tunawa da sunanka, * Yahweh, * shari’arka kuma da goshin asuba.

Na zama abin cin mutunci, * domin ina ri}e da umurnanka.

57-64 x

Yahweh Mahaliccina, na alkawalta * bin dokokinka.

Na nemi alherinka da dukan zuciyata, * ka tausaya mani bisa ga alkawalinka.

Da na yi tunanin hanyoyinka, * sai na maida matakaina ga shara]unka.

Na yi hamzari, ba da jinkiri ba, * don bin dokokinka.

Duk da taron miyagu ya kewaye ni, * ban manta da shari’arka ba.

Da tsakar dare nike tashi don in gode maka, * domin hukuntanka na gaskiya.

Ni ne abokin dukan masu tsoronka, * da dukan masu bin umurnanka.

Duniya cike take da }aunarka, * Yahweh, * ka koya ni ka’idodinka.

65-72 j

Yahweh, ka yi wa bawanka alheri, * bisa ga maganarka.

Ka koya mani ilimi da hikima, * domin na gaskanta da dokokinka.

Kafin in sha wuya, na bau]e, * amma yanzu ina kiyaye kalmarka.

Kai nagari ne, kana kuma nagartawa, * ka koya mani ka’idodinka.

Masu izgilanci suna ~ata sunana da }arairayi, * amma ni, da dukan zuciyta nike kiyaye umurnanka.

Zuciyarsu ta daskare kamar kitse, * ni kuwa ina jin da]in shari’arka.

Ya yi kyau da na sha wahala, * domin in koyi ka’idodinka.

Shari’ar bakinka tana yi mani kyau * fiye da ]umbin azurfa da zinariya.

73-80 y

Hannuwanka ne suka yi ni, suka sifanta ni, * ka ba ni basira don in koyi dokokinka.

Masu tsoronka za su gan ni, su yi farinciki, * domin ina jiran maganarka.

Yahweh, na sani * kai adili ne wajen hukuntanka, * ka tsananta mani kan gaskiya.

Bari }aunarka ta zama ta’aziya a gare ni, * bisa ga alkawalinka ga bawanka.

Bari rahamominka su zo guna don in rayu, * domin shari’arka tana sa in ji da]i.

Bari masu izgilanci su kunyata, * sun so su karkata ni ta yaudara, * amma ni na yi nazarin umurnanka.

Bari masu tsoronka su juyo mani, * don su san shara]unka.

Bari zuciyata ta zama kamila game da ka’idodinka, * don kada in kunyata.

81-88 k

Raina ya ]okanta ga begen cetonka, * ina ta jiratan maganarka.

Idanuna sun gaji suna ta jiran kalmarka, * har ina cewa, “Yaushe za ka sanyaya mani rai?”

Gama na zama kamar mai kuka saboda haya}i, * duk da haka ban mance ka’idodinka ba.

Nawa ne kwanakin bawanka? * Yaushe ne za ka yi wa masu tsananta mani hukunci?

Masu girman kai sun ha}a mani ramu, * ba su kula da shari’arka ba.

Dukan dokokinka gaskiya ne, * amma suna tsananta mani da }arya, ka agaje ni.

Sun kusa hallaka ni a duniya, * amma ni ban yi watsi da umurnanka ba.

Saboda }aunarka ka kare raina, * don ina bin shara]un da ka fa]i.

89-96 l

Yahweh, kalmarka madauwamiya ce, * ta tabbata fiye da sammai.

Gaskiyarka ta tabbata daga tsara zuwa tsara, * ta kafu fiye da }asa.

Ta hukuncinka ta tabbata har kwanan gobe, * domin dukan abubuwa bayinka ne.

Da shari’arka ba ita ce da]ina ba, * da na hallaka saboda wahaluna.

Har abada ba zan mance da umurnanka ba, * domin ta wurinsu kake raya ni.

Naka ne ni, ka cece ni, * domin ina bin umurnanka.

Miyagu sun fake domin su hallaka ni, * amma ni ina nazarin shara]unka.

Fiye da dukan al’ajiban da na ta~a gani, ya {arshe, * dokarka ta rungumi kome, ya Mai Girma.

97-104 m

Dubi yadda nike }aunar shari’arka, * ita ce nike nazari kanta wuni zubut.

Dokokinka sun mai da ni mai hikima fiye da magabtana, * domin suna tare da ni har abada.

Ganewata ta fi ta dukan malamaina, * domin nikan yi nazarin shara]unka.

Na fi tsofaffi hikima, * domin na ri}e umurnanka.

Na hana }afafuna bin kowace irin muguwar hanya, * don in bi maganarka.

Ban goce daga hukuntanka ba, * domin kai ne ka koya mani.

Kalmarka tana da da]in ]an]ano, * kamar zuma take a bakina!

Ta wurin umurnanka nike samun basira, * Ma]aukakin Zati, * ina }in dukan hanya ta }arya.

105-112 n

Maganarka fitila ce ga }afafuna, * da haske a kan hanyata.

Na rantse zan ci gaba * da bin hukuntanka masu gaskiya.

Azabata ta kai Masifa, * Yahweh, ka raya ni bisa ga maganarka.

Yahweh, ka faranta raina da jawabi mai da]i, * ka koya mani hukuntanka.

Raina yana hannunka, ya Madauwami, * don haka bana mance shari’arka.

Miyagu suna ]ana mani tarko, * amma ban goce daga umurnanka ba.

Na yi gadon shara]unka, ya Madauwami, * i, su ne ke faranta mani zuciya.

Na juya zuciyata in aikata ka’idodinka, * ladana zai zama na har abada.

113-120 s

Na tsargi masu zuciya biyu, * amma ina son shari’arka.

Kai ne Makarina da Shugabana, * ina ta jiran maganarka.

Ku rabu da ni, ku miyagu, * don in kiyaye dokokin Allahna.

Ka tallafa mani bisa ga alkawalinka, don in rayu, * kada ka bari in kunyata ga sazuciyata.

Ka rungume ni don in ku~uta, * in girmama ka’idodinka, ya Madauwami.

Ka yi juji na dukan masu bau]e wa ka’idodinka, * domin bautar gumakansu banza ce.

Kâ yas da dukan miyagun duniya kamar sharâ, * saboda haka nike son shara]unka.

Jikina yana rawa saboda tsoronka, * ina tsoron hukuntanka.

121-128 [

Ka kare hakkina na gaskiya, * kada ka bar ni ga masu tsananta mani.

Ka ba bawanka tabbaci, ya Managarci, * don kada masu girman kai su zalunce ni.

Idanuna suna begen cetonka, * da kuma alkawalinka na gaskiya.

Ka aikata wa bawanka alherinka, * ka koya mani ka’idodinka.

Ni bawanka ne, ka ba ni ganewa, * domin in san shara]unka.

Lokacin aikatawa ya yi, Yahweh, * sun banzata shari’arka.

Ma]aukakin Zati, * ina }aunar dokokinka * fiye da zinari komi kyansa.

Ma]aukakin Zati, * ina gaskanta dukan umurnanka, * na tsargi kowane irin rashin gaskiya.

129-136 p

Shara]unka masu banmamaki ne, * ya Ma]aukakin Zati, ina bin su.

Ka bu]e hasken maganarka, * ka ba marasa sani ganewa.

Ina haki da baki bu]e, * domin ina ]okin dokokinka.

Ka juyo gare ni, ka ji tausayina, * yadda kakan yi wa masu son sunanka.

Ka kafa sawayena a kalmarka, * kada ka bari mugunta ta rinjaye ni.

Ka fanshe ni daga zaluncin ’yan adan, * don in bi umurnanka.

Ka sa fuskarka ta haskaka bawanka, * sannan ka koya mani ka’idodinka.

Idanuna suna zub da }oramun hawaye, * ya Ma]aukaki, ba su kiyaye shari’arka ba.

137-144 c

Kai mai gaskiya ne, Yahweh, * mai adalci kuma a cikin hukuntanka.

Ka umurci shara]unka da gaskiya * da aminci, ya Mai Girma.

Abokan hamayyata suna so su hallaka ni, * magabtana ba su kula da dokokinka ba.

An gwada kalmarka, * ya Ma]aukaki, * bawanka kuma yana }aunarta.

Ko da nike matashi renanne, * ban mance da umurnanka ba.

Adalcinka na gaskiya ne, * ya Madauwami, * shari’arka kuma ta hakikanta.

Duk da ina cikin wahala da damuwa, * ina jin da]in dokokinka.

A game da hakikancin shara]unka, * ya Madauwami, * ka ba ni ganewa don in rayu.

145-152 q

Na yi kira da dukan zuciyata, * ka amsa mani, Yahweh, * don in kiyaye ka’idodinka.

Ina kiranka, ka cece ni, * don ina bin shara]unka.

Da sassafe na dube ka da kukan neman taimako, * ana jiran maganarka.

Na raba dare ina zuba idanu gare ka, * da nike nazari akan alkawalinka.

Cikin alherinka ka ji muryata, * Yahweh, * da adalcinka ka kiyaye raina.

Masu bautar gumaka suna matsowa, * sun yi nesa da shari’arka.

Amma kai ne Makusanci, Yahweh, * dukan dokokinka kuma gaskiya ne.

Ya Farko, na yarda da shara]unka, * domin ka kafa su tuntuni.

153-160 r

Ka dubi wahalata, ka cece ni, * domin ban mance da shari’arka ba.

Ka bi hakkina, ka fanshe ni, * bisa ga alkawalkinka ka raya ni.

Ka nisanta miyagu da cetonka, * domin basa bin ka’idodinka.

Rahamominka masu yawa ne, Yahweh, * bisa ga hukuntanka ka raya ni.

Duk da matsanantana da abokan gabata sun yi yawa, * ban bau]e daga shara]unka ba.

Na dubi maciya amana, na ji }yama, * domin ba sa kiyaye maganarka.

Dubi yadda nike son umurnanka, * Yahweh, a cikin alherinka ka raya ni.

Cibiyar maganarka ita ce gaskiya, * ya Madauwami, * hukuncinka kuma adalci ne.

161-168 v

’Yan iska suna tsananta mani ba dalili, * zuciyata kuma ta firgita da masu bina.

Na yi murna da kalmarka, * domin maganarka babbar riba ce gare ni.

Na tsargi }arya, na }i ta, * amma ina }aunar shari’arka.

Ina yabonka sau bakwai kowace rana, * saboda hukuntanka masu gaskiya.

Akwai babbar albarka ga masu }aunar shari’arka, * babu sanadin tuntu~e gare su.

Na sa zuciya ga cetonka, * Yahweh, * na kuwa aikata dokokinka.

Raina ya kiyaye shara]unka, * ina }aunarsu matu}a.

Ina kiyaye umurnanka da shara]unka, * domin dukan al’amurana suna gabanka.

169-176 t

Bari kukana ya kai gare ka, * Yahweh, * bisa ga maganarka ka ba ni ganewa.

Bari addu’ata ta zo gare ka, * bisa ga alkawalinka ka cece ni.

Bari le~unana su dinga yabonka, * domin kana koya mani ka’idodinka.

Bari halshena ya maimaita kalmarka, * domin cikamakin dokokinka adalci ne.

Bari ka shirya hannunka don taimakona, * gama na za~i umurnanka.

Ina begen cetonka, * Yahweh, * shari’arka kuma tana faranta mani rai.

Raina ya da]e don ya yabe ka, * hukuntanka kuma su taimake ni.

Ko da na ratse kamar ~atattar tunkiya, * ka neme ni, bawanka, * domin ban mance da dokokinka ba.

Zabura ta 120

Da aka kai mani hari * na yi kira ga Yahweh, * ya kuwa amsa mani.

    Yahweh, ka cece ni * daga le~una ma}aryata, * daga halshe mai ha’inci.

    Yadda zai saka maka! * zai ninka horonka, * ya halshen ha’inci!

        Zai zama kamar tsinanan kiban jarumi, * da garwashin wuta.

    Kaitona! Ko da na je ba}unci a Mashak, * ko na tafi sansanin Kedar,

    na zauna kurkusa * da ma}iyin salama.

Ni dai, ina maganar salama, * amma su, sai ta ya}i.

Zabura ta 121

Na ]aga idanuna ga Dutsen, * daga ina taimakona zai zo?

    Taimakona zai zo daga wurin Yahweh, * Mahaliccin sama da }asa.

        Ba zai sa }afarka a Tabon ba, * Matsarinka ba zai yi gyangya]i ba.

            I, baya gyangya]i ko barci, * Matsarin Isra’ila.

            Yahweh ne matsarinka, * Yahweh ne inuwarka, * Ma]aukaki shi ne hannun damanka.

        Da rana, rana ba za ta yi maka lahani ba, * ko wata da daddare.

    Yahweh zai kare ka * daga kowace irin mugunta, * zai tsare ranka.

Yahweh zai kare fita da dawowarka * daga yanzu da har abada.

Zabura ta 122

Na yi murna da masu cewa da ni: * “Bari mu je gidan Yahweh.”

{afafuna suna tsaye * a hayin }ofofin Urushalima.

    Urushalima da aka gina tamkar birninsa, * wanda shi ka]ai ne ya kammala ginin.

    A can ne kabilu ke hawa, * kabilun Yahweh.

        Shara]i ne, ya Isra’ila, * ka yi godiya ga sunan Yahweh,

        domin can ne suka zauna * a kursiyun shari’a, * kursiyun gidan Dauda.

    Bari su yi addu’a don salamarki, ya Urushalima, * bari masoyanki su arzuta!

    Bari salama ta wanzu a kewayen ganuwoyinki, * wadata kuma a cikin fâdodinki.

Saboda ’yan’uwana da abokaina ,* ina cewa, “Salama a gare ki.”

Saboda gidan Yahweh Allahnmu, * ina neman alherinki.

Zabura ta 123

Ina zuba idanuna gare ka, * ya Mai mazauni a sama.

    I, kamar idanun bayi * da ke duban hannun iyayangijinsu,

        kamar idanun baiwa * da ke duban hannun uwargijiyarta,

        haka ne idanunmu * ke duban Yahweh Allahnmu, * har sai ya ji tausayinmu.

    Ka ji tausayinmu, Yahweh, * ka ji tausayinmu, ya Rabbi, * mun gaji da wulakanci.

Mun da]e ma}ogwaronmu yana cika * da zagin ’yan iska, * da kuma renin masu izgilanci.

Zabura ta 124

Da ba Yahweh ne tare da mu ba, * bari Isra’ila ya ce,

da ba Yahweh ne tare da mu ba, * sa’ad da mutane suka tasam mana,

    da sun ha]iye mu da rai, * sa’ad da hushinsu ya yi }una a kan mu,

        da ruwaye sun sha kan mu * kamar }orama * ta shanye wuyanmu,

            da ruwaye masu toro}o * sun gudado bisa wuyanmu.

            Yabo ga Yahweh, * da bai ba da mu * kamar ganima su ci ba.

        Wuyanmu ya ku~uce kamar tsuntsu * daga tarkon mafarauci.

    Tarkon ya tsinke, * mu kuma mun tsira.

Taimakonmu yana cikin sunan Yahweh, * wanda ya halicci sama da }asa.

Zabura ta 125

Masu dogara ga Yahweh * kamar dutsen Sihiyona suke.

Mai kursiyin Urushalima * har abada ba zai jijigu ba.

    Kamar duwatsun da ke kewaye da ita, * haka ne Yahweh ke kewaye da jama’arsa * daga yanzu har abada.

        Sandan mugu ba zai tsaya * a kan }asar da aka raba wa masu gaskiya ba,

    in masu gaskiya ba su sa hannu * a cikin aikin cuta ba.

Nuna nagartarka, Yahweh, ga masu nagari, * da zuciyarsu ke daidai.

Amma masu shan kaye saboda baki biyunsu, * Yahweh ya kore su da masu aikata mugunta.

Salama ga Isra’ila!


Zabura ta 126

Sa’ad da Yahweh ya sake arzuta Sihiyona, * mun zama kamar yashin teku.

    Sannan bakinmu ya cika da murmushi, * halshenmu kuma da sowar murna.

        Sannan sai al’ummai suka ce, * “Yahweh ya nuna girmansa * ta yi masu aiki.”

            Yahweh ya nuna girmansa * ta yi mana aiki, * mun zama masu murna.

            Yahweh ya sake arzuta mu, * kamar }oramun Nagab.

        Wa]anda suka yi shuka da hawaye * suna yin girbi da sowa ta murna.

    Ko da yake ya tafi yana kuka, * yana ]auke da }waryar iri,

ya dawo gida da sowa ta murna, * yana zuwa da dammunansa.

Zabura ta 127

Idan ba Yahweh ne ya gina fadar ba, * aikin banza maginanta suke yi.

Idan ba Yahweh ne ya tsare birnin ba, * tsaron banza matsaranshi suke yi.

    A banza ne kuke saurin tashi, * ku da ke kwanciya a makare,

        kuna ta cin abincin gumaka. * Amma Amini yana ba da wadata ga }aunatattunsa.

        I, ’ya’ya kyauta ce daga wurin Yahweh, * albarkar mahaifar mace lada ne daga gare shi.

    Kamar kibau a hannun jarumi, * haka ’ya’yan da aka haifa a }uruciya suke.

Albarka ga mutumin * da ya cika kwarinsa da su.

Ba zai kunyata ba, * amma zai kori magabtansa tun daga bakin }ofa.

Zabura ta 128

Albarka ga kowane mai tsoron Yahweh, * yana bin hanyarsa!

I, za ka ci aikin hannunka, * za ka yi farinciki ka arzuta.

Matarka za ta zama kamar kuringar inabi * mai ’ya’ya a gidanka.

’Ya’yanka kamar rassan zaitun, * suna kewaye da teburinka.

    Ga yadda Amini yakan yi albarka * ga mai tsoron Yahweh.

Yahweh na Sihiyona ya yi maka albarka!

Ka ji da]in wadatar Urushalima * dukan kwanakin ranka!

Ka ji da]in jikokinka, * da kuma salama daga Ma]aukakin Isra’ila.

Zabura ta 129

“Sun tsananta mani sosai tun }uruciyata,” * haka Isra’ila ya ce.

“Sun tsananta mani sosai tun }uruciyata,” * amma ba su rinjaye ni ba.

Mahu]a sun hu]e gadon bayana, * sun yi dogayen kunyai a kansa.

    Bari Yahweh Mai Gaskiya ya tsinke * karkiyar miyagu.

    Bari dukan masu }in Sihiyona * su kunyata, su koma da baya.

Bari su zama kamar ciyawar kan soro, * da ke bushewa a gaban mai tum~ukewa,

don kada mai girbi ya cika hannunsa, * ko mai ]aura dami ya cika }irjinsa da ita,

kada kuma masu wucewa su ce, * “Albarkar Yahweh a kan ku! * Mun yi maku albarka da sunan Yahweh!”

Zabura ta 130

Daga Zurfafa nike yin kuka gare ka, Yahweh, * ya Ubangiji, ka ji muryata.

Bari kunnuwanka su ji * ro}on da nike yi don jin}ai.

    Da kana lissafa mugunta, Yahweh, * Ubangiji, wa zai iya jurewa?

        Amma wurinka akwai gafara, * domin a tsorace ka.

        Ina kiran Yahweh, * raina yana kira, * ina jiran maganarsa.

    Raina yana sauraren Ubangijina, * daga tsaron dare har safe, * da tsaron dare har safe.

Isra’ila, ka dakaci Yahweh, * domin a wurin Yahweh akwai }auna, * a wurinsa da fansa mai yawa.

Shi kansa zai fanshi Isra’ila * daga dukan kurakuransa gare shi.

Zabura ta 131

Yahweh, zuciyata ba mai alfarma ba ce, * idanuna kuma ba masu rena kowa ba ne.

    Ban shiga al’amuran da suka zarce ni ba, * ban kuma shiga zantuttukan da suka fi }arfina ba.

        Amma na kwantad da raina,

    kamar jinjirin da ke kwance a gun uwarsa, * raina ma kamar jinjiri ne a gunsa.

Isra’ila, ka dakaci Yahweh, * daga yanzu har abada.

Zabura ta 132

Dauda, ka tuna da Yahweh,* da dukan nasarorinsa.

    Dauda ya yi wa Yahweh rantsuwa, * ya yi wa’adi ga Mai Girma na Yakubu da ya ce:

        “Ba zan shiga labulen wurin kwanciyata ba, * ba ma zan hau gadon da aka shimfi]a mani ba.

        Ba zan bar idanuna su yi barci ba, * ko ma}iftaina su yi gyangya]i,

    sai na samar wa Yahweh wuri, * mazauni don Mai Girma na Yakubu.

        Duba, mun ji wannan labarin a Efrata, * an gaya mana ma a filin Jayar.

            Bari mu tafi mazauninsa, * mu yi sujada a matashin sawunsa.

            Tashi, Yahweh, ka je wurin hutuwarka, * kai da akwatin da ke mafakarka.

        Bari a tufatar da firistocinka da gaskiya, * masu bautarka kuma su yi sowa ta murna,

            su ce: “Saboda bawanka Dauda, * kada ka ya da shafaffen sarkinka.”

        Dauda, Yahweh ya yi rantsuwa, * hakika ba zai canza ba:

            cewa, “[an jikinka * zan sa a kan kursiyinka,

            in ’ya’yanka sun kiyaye yarjejeniyata, * da shara]un da zan koya masu.

        ’Ya’yansu ma za su zauna * a kan kursiyinka har abada.

    Gama Yahweh ya za~i Sihiyona, * yana marmarinta don ta zama mazauninsa.

        Ga wurin hutuwata har abada, * a nan zan zauna don ina marmarinta.

        Zan yi wa alhazanta albarka mai yawa, * zan }osad da gajiyayyunta da abinci.

    Zan tufatad da firistocinta da ceto, * masu bautata kuma za su ri}a yin sowa ta murna.

Dauda, can zan sa }ahonka ya ri}a haske, * zan kuma kunna fitilarka, ya shafaffena.

Magabtansa zan tufanta su da kunya, * amma kambinsa zai yi }yalli a kansa.

Zabura ta 133

Abu ne mai kyau da faranta rai, * in ’yan’uwa suna zaman salama!

    Kamar kyakkyawan mai ne da aka zuba a ka, * ya yi naso har kan gemu,

        gemun nan na Haruna, * yana naso har wuyan rigarsa,

    kamar ma ra~ar Harmon ce, * in ta sauko a kan duwatsun Sihiyona.

A can ne Yahweh yake ba da albarka, * ta rai na har abada.

Zabura ta 134

Ku zo, ku yabi Yahweh, * ku dukan ayyukan Yahweh!

    Ku da ke tsaye a gidan Yahweh * har tsakar dare,

    ku ]aga hannuwanku ga tsattsarkan wuri, * ku yabi Yahweh.

Yahweh na Sihiyona ya yi maku albarka, * wanda ya yi sama da }asa.

Zabura ta 135

Halelu-Yah!

Ku zo, ku yabi sunan Yahweh, * ku yabi dukan ayyukan Yahweh,

    ku da ke tsaye a gidan Yahweh * a farfajiyar gidan Allahnmu.

    Ku yabi Yahweh, gama shi nagari ne, * ku yi wa}ar sunansa mai da]i.

Don Yahweh ya za~i Yakubu ya zama nasa, * Isra’ila kuma tamkar mallakarsa.

    I, na yarda Yahweh mai girma ne, * Ubangijinmu kuma ya fi dukan alloli girma.

        Duka abin da Yahweh ya ga dama * shi zai yi,

            a sama da }asa, * a tekuna da dukan zurfafa.

        Yana ta da gajimarai * daga bangon duniya,

    yana yin wal}iya don ruwan sama, * yana kawo iska daga taskokinsa.

        Shi ne ya mazge ’ya’yan fari a Masar, * na mutun da na dabba.

        Ya aiki alamomi da al’ajibai, * a tskar Masar, * kan Fira’auna da dukan bayinsa.

            Shi ne ya mazge manyan al’ummai, * ya karkashe manyan sarakuna,

            har da Sihon, sarkin Amoriyawa, * da Og, sarkin Bashan, * i, da dukan sarakunan Kan’ana.

            Ya ba da }asarsu a gada, * gado ga jama’arsa Isra’ila.

        Yahweh, sunanka madauwami ne, * Yahweh, martabarka tana kan dukan tsararraki.

        I, Yahweh yana kare jama’arsa, * yana jin tausayin bayinsa.

    Amma gumakan al’ummai azurfa da zinari ne, * aikin hannuwan mutun.

        Suna da baki, ba sa magana, * suna da idanu, ba sa gani.

        Suna da kunnuwa, ba sa jin murya, * ba su ma lumfashi.

    Masu yinsu za su zama kamar su, * da duk wanda ya dogara gare su.

Ya Isra’ilawa, ku yabi Yahweh, * ya gidan Haruna, ku yabi Yahweh!

    Ya gidan Lawi, ku yabi Yahweh! * Masu tsoron Yahweh, ku yabi Yahweh!

Yabo ga Yahweh na Sihiyona, * Mai Zama a Urushalima!

Halelu-Yah!


Zabura ta 136

Ku gode wa Yahweh don shi nagari ne, * }aunarsa madauwamiya ce.

Ku gode wa Allah mai alloli, * }aunarsa madauwamiya ce.

Ku gode wa Ubangijin iyayengiji, * }aunarsa madauwamiya ce.

    Ga Mai yin manyan mu’ujizai shi ka]ai, * }aunarsa madauwamiya ce.

    Ga Mai yin sammai da hikima, * }aunarsa madauwamiya ce.

        Ga Mai shimfi]a }asa a birbishin ruwaye, * }aunarsa madauwamiya ce.

        Ga Mai yin manyan haskoki, * }aunarsa madauwamiya ce.

            Rana mai mulkin rana, * }aunarsa madauwamiya ce.

            Wata da taurari masu mulkin dare, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya mazge ’ya’yan farin Masarawa, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Ya fito da Isra’ila daga cikinsu, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Da }a}}arfan hannu da mi}a}}en dantse, * }aunarsa madauwamiya ce.

                      Wanda ya raba Bahar Kyamare biyu, * }aunarsa madauwamiya ce.

                           Ya hayar da Isra’ila ta cikinta, * }aunarsa madauwamiya ce.

                      Amma ya birkice Fira’auna da maya}ansa, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya sa jama’arsa haye hamada, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Wanda ya mazge manyan sarakuna, * }aunarsa madauwamiya ce.

                 Ya ma kashe shaharrarrun sarakuna, * }aunarsa madauwamiya ce.

            Har da Sihon, sarkin Amoriyawa, * }aunarsa madauwamiya ce.

            Da Og, sarkin Bashan, * }aunarsa madauwamiya ce.

        Ya ba da }asarsu abin gado, * }aunarsa madauwamiya ce.

        Gado ga Isra’ila bawansa, * }aunarsa madauwamiya ce.

    Wanda ya tuna mu cikin }as}ancinmu, * }aunarsa madauwamiya ce.

    Ya fyauce mu daga abokan gabanmu, * }aunarsa madauwamiya ce.

Wanda yake ba kowace dabba abinci, * }aunarsa madauwamiya ce.

Ku yabi Allah na sama, * }aunarsa madauwamiya ce.

Zabura ta 137

A bakin kogunan Babila, * can muka zauna,

muka yi kuka mai tsanani, * sa’ad da muka tuna da ke, Sihiyona.

    A gefen itatuwan da ke can, * muka rataye garayunmu.

    Domin masu kama mu sun ce * mu yi masu wa}a.

    Masu zaginmu sun bi]i murna, * “Ku raira mana daga cikin wa}o}in Sihiyona.”

        In na mance da ke, * ya Urushalima, * hannuna na dama ya shanye!

        Bari halshena ya li}e wa bakina * in ban tuna da ke ba,

        in ban sa~a ki, ya Urushalima, * a kafa]ata cikin shagali ba!

    Ku tuna da Yahweh, ku Edomawa, * game da ranar Urushalima,

    sa’ad da kuka ce, “Tu~e, tu~e, * har zuwa harsashinta!”

Ya ’Ya Babila, mai hallakawa, * albarka ga wanda ya saka maki * da mugun da kika yi mana!

Albarka ga wanda ya kwashi jariranki, * ya fya]a su a kan dutse!

Zabura ta 138

Ina yi maka godiya da dukan zuciyata, * ina raira maka wa}a a gaban mala’iku.

Ina yin sujada zuwa ga tsattsarkan Haikalinka, * ina yi wa sunanka godiya.

    Ta }aunarka da amincinka * lalle ka ]aukaka * sunanka da alkawalinka a gaban kowa.

    Da na kira, kâ ba ni nasara, * kâ taimake ni da }arfin hali don kai hari.

        Dukan sarakunan duniya za su yabe ka, Yahweh, * in suka ji kalmomin bakinka.

            Za su kuwa yi wa}ar sarautar Yahweh, * cewa, “[aukakar Yahweh da girma take!”

        Ko da yake Yahweh Ma]aukaki ne, * yakan dubi mai }as}anci, * ko da yake Mai Sama, yana ji daga nesa.

    Da nike tafiya a tsakar abokan gabata, * ka raya ni a cikin haushin magabtana.

    Ka mi}o hannunka na hagu, * ka ba ni nasara da hannun damanka. * Yahweh ya rama mani muddin rayuwata.

Yahweh, }aunarka madauwamiya ce, * kada ka }yale ayyukan hannuwanka.

Zabura ta 139

Yahweh, ka bincike ni, * ka gane ni da kanka!

    Kana sanin zamana da tashina, * ka gane tunanina daga nesa.

        Kana safiyon fitowata da dawowata, * ka lura da dukan tafiyata.

            Ba kalmar da ke fita daga bakina, * sai ka san ta duka.

        Kâ yi mani shinge gaba da baya, * kâ rungume ni da tafin hannuwanka.

    Saninka ya fi }arfina, * ya sha kaina, bana iya haddace shi.

        Ina zan je guje wa ruhunka? * Ina zan gudu daga fuskarka?

            In na hau sammai, kana can, * in na kwanta a Shawol, kana can!

            In na ta da fukafukaina daga gabas * don in sauka a }urin yamma,

        can ma za ka ]ora hannun hagunka a kaina, * kana kama ni da hannun damanka.

            Sannan na sansance ko cikin duhu yana kallona, * da dare kuma haske yana kewaye ni.

            Duhun bai duhunta gare ka ba, * Daren yana haskaka maka kamar rana, * daren ma sai ka ce haske.

                 I, ka siffanta }odata, * kâ kare ni tun ina cikin mahaifar uwata.

            Ina yabonka, ya Ma]aukaki, * domin kai mai bantsoro ne.

            Na rusuna don yi maka sujada, * ya mai banrazana ta wurin ayyukanka.

        Kâ san ruhuna tuntuni, * }asusuwana ba a ~oye suke a gare ka ba

            tun da aka za~i yum~un a Asirtaccen Wuri, * aka mulmula ni a zurfafan {al}ashin {asa.

            Idanunka sun ga matakan rayuwata, * don an rubuta dukansu a littafinka.

        An siffanta kwanakina * tun kafin waninsu ya gan ni.

    Amma a gare ni tunaninka suna da nauyi, * ya Allah, tulawarsu tana ta }arfi!

    Da zan iya }irga su, da sun fi yashi yawa! * Bari in tashi in zama tare da kai har abada!

        Ya Allah, ina ma a ce za ka kashe mugun, * masu bautar gumaka, ku yi nesa da ni!

        Suna kallon kowane gunki, * suna zura ido ga abubuwan banza da aka baje kolinsu.

    I, Yahweh, ina }in masu }inka, * ina }yamar masu yi maka tawaye.

    Ina }insu da matu}ar }iyayya, * sun zama abokan gabata.

Ka bincike ni, ya Allah, ka san zuciyata, * ka gwada ni, ka ma gane damuwata.

Ka ga ko wani gunki ya ta~a mallakata, * kâna ka kai ni madauwamin mulkinka.

Zabura ta 140

Yahweh, ka cece ni daga mugun mutun, * ka tsare ni daga mai ]acin rai,

    domin suna shirya }eta a zukatansu, * wuni zubut suna shirin ya}i.

    Suna wasa da halshensu kamar maciji, * ko kububuwa ba ta kai ]afin le~ensu ba.

        Yahweh, ka kiyaye ni daga hannuwan mugu, * ka kare ni daga mafa]aci,

        domin sun yi shirin tadiye }afafuna, * masu izgilanci sun ]ana mani tarko.

        ’Yan ta’adda sun ]ana tarko, * a gefen hanya suka baza mani raga.

            Ina cewa, “Yahweh, kai ne Allahna, * ka kasa kunne, Yahweh, ga ro}ona don jin}ai.

            Yahweh Ubangijina, mafakar cetona, * ka zama garkuwata a fagen fama.

        Yahweh, kada ka biya bukakan miyagu, * ya Ma]aukaki, kada ka inganta ma}ar}ashiyarsu.

        Abokan gaba da suka kewaye ni, * bari su nutse a cikin dafin le~unansu.

        Bari ya zuba masu garwashin wuta, * ya ingiza su cikin Wutar, * kada su iya fita daga kududdufinta!

    Mai kakkausan harshe, * kada ya sami masauki a }asa.

    Azzalumi ma, * bari Mugun nan ya farauce shi zuwa Bayan Duniya.

    Na san Yahweh zai kare zaluntacce * ya bi hakkin matalauta.

Lalle, adalai za su yabi sunanka, * masu gaskiya kuma za su dauwama a gaban fuskarka.

Zabura ta 141

Ina kiranka, Yahweh, * amsa mani mana.

    Ina kiranka, * ka saurare ni!

        Bari addu’ata ta kasance * kamar turaren }anshi a gabanka,

        ]agaggun hannuwana kuma * kamar hadayar maraice.

    Yahweh, ka danne bakina, * ya Ma]aukaki, ka }ulle le~unana.

Ka hana zuciyata kitsa mugunta, * da sha’awar ayyukan miyagu.

        Idan na taya miyagu * cin abincin gara~asarsu,

            bari Mai Gaskiya ya mazge ni, * Mai Alherin nan ya hore ni.

        Haka ma idan mansu mai daraja ya haskaka kaina, * domin ina ci gaba da yin addu’a a kan miyagun ayyukansu.

Bari alkalansu su fâ]a a hannuwan Dutsen, * su kuwa ]an]ana hukuncinsa!

    Kamar wanda aka sassare aka yanyana a Lahira, * haka }asasuwana suka barbaje a bakin Shawol.

        Amma gare ka, * Yahweh Ubangiji, * nike zuba ido.

        Na nemi tsira a gunka, * ya Allah, * ka kare raina.

    Ka kiyaye ni daga tarkon da suka ]ana mani * da kiban azzaluman nan.

Bari miyagun nan duka * su fâ]a tarkunan Yahweh, * ni kuwa in tsira.

Zabura ta 142

Ina kuka ga Yahweh da }arfi, * ina kuka ga Yahweh don neman tausayi!

    A gare shi nike bulbula }arrarakina, * ina gaya mashi wahaluna:

        Ruhuna ya gaza, * amma kai ne ka san inda zani.

    Sun ]ana mani tarko * a kan hanyar da nike bi.

        Ka dubi kewaye da ni, * ba wanda ya san ni.

            Ba ni da damar tsira, * babu mai kula da ni.

        Na yi ruri gare ka, Yahweh, * na ce kai ne mafakata,* da rabona a }asar madauwamin rai.

    Ya Allah, ka saurari kukana, * ya Mai Girma, na gaza!

        Ka cece ni daga mafarautana, * domin sun fi ni }arfi.

    Ka tsamo ni daga kurkuku, * don in yabi sunanka.

Bari masu gaskiya su kewaye ni, * domin ka kyauta mani, ya Ma]aukaki.

Zabura ta 143

Ka ji addu’ata, Yahweh, * ya Allah, ka ji ro}ona don jin}ai.

Ka amsa mani da amincinka, * ka amsa mani da adalcinka.

    Amma kada ka kai bawanka a gaban shari’a, * domin babu wani mai rai da zai barata a gabanka.

        Domin magabci ya faki raina, * ya goga rayuwata zuwa {al}ashin {asa.

        Ya sa ni zama cikin lungun duhu, * kamar mutanen Dauwamammen Gida.

    Ruhuna ya narke mani, * zuciyata ta karai.

Na tuna zamanin dâ, * na lissafci dukan ayyukanka, * kan ayyukan hannuwanka na yi nazari.

Na mi}a hannuwana zuwa wurinka, * daga {al}ashin {asa ma}ogwarona na }ishinruwanka.

Ka yi hanzarin amsa mani, Yahweh, * ruhuna ya gaza, ya Allah!

In ka kau da fuskarka daga guna, * zan yi kama da masu gangarawa Ramin.

    Bari in yi kaci~is da alherinka da asuba, * domin ina dogara gare ka.

    Ka nuna mani hanyar da zan bi, * domin na mai da hankalina gunka.

        Yahweh, ka cece ni daga magabtana,* ya Allahna, a gaskiya ina nutsewa.

    Ka koya mani yin nufinka, * domin kai ne Allahna.

    Da ruhaniyarka ta }warai * ka bi da ni * zuwa {asa madaidaiciya.

Yahweh, saboda sunanka ka ba ni rai, * ta gaskiyarka ka fanso raina daga magabtana.

Ta }aunarka ka shafe abokan gabata, * ka hallaka dukan masu tsorata ni, * domin ni bawanka ne.

Zabura ta 144

Yabo ga Allah, Dutsena, * wanda ya koya wa hannuwana dabarun ya}i, * damatsana logogin fa]a.

    Garuna da mafakata, * katangata da matserata,

    Shugabana, na dogara gare shi, * wanda ya rusunad da mutane a }afafuna.

        Yahweh, menene mutun, har da za ka damu da shi, * ]an adan, har da za ka kula da shi?

        Mutun kamar tururi ne, * kwanakinsa kamar inuwa ce mai wucewa.

            Yahweh, ka na]e sammanka, ka sakko, * ta ta~a duwatsu, ka sa su yi haya}i.

            Ka gilma wal}iyoyinka, ka watsa su, * ka }era kibanka, ka harba su.

        Ka mi}o hannuwanka daga sama, * ka tsamo ni, ka cece ni

        daga Zuzzurfan Ruwa, * daga hannun ba}i,

        wa]anda bakinsu ke wulla }arya, * hanuunsu na dama kuma yana yin shaidar zur.

    Ya Allah, bari in raira maka sabuwar wa}a, * ina ka]a maka garaya mai tsarkiyoyi goma,

    kai da ka ba sarkinka nasara, * ka fanso bawanka Dauda.

Ka fanso ni daga takobin Mugun nan, * ka }wato ni daga hannun ba}i.

wa]anda bakinsu ke wulla }arya, * hannunsu na dama kuma yana yin shaidar zur.

Bari ya yi wa ’ya’yanmu maza albarka kamar icen inabi, * da aka hora tun }uruciyarsu

’ya’ya matanmu kuma kamar ginshi}ai, * da aka gina don adon fâda.

    Bari rumbuanmu su cika, * har su yi banzabo.

    Bari tumakinmu su haifi dubban ’ya’ya, * dubbai bisa dubbai a makiyayinmu, * shanunmu su yi ~ul~ul.

Kada mu ga wani hari ko gudun hijira, * ko mu ji hayaniya a dandalinmu.

Albarka ga jama’ar da ta zama haka, * albarka ga jama’a wadda Yahweh ne Allahnsu.

Zaburta ta 145

Zan ]aukaka ka, ya Allah Sarkina, * zan albarkaci sunanka, ya Ma]aukaki!

    Zan albarkace ka kowace rana, * in yi wa}a da sunanka har abada abadin.

    Yahweh Akbar, * Mai Girma ne da ya dace da yabo, * domin girmansa ba shi da iyaka.

    Kowace tsara za ta bayyana ayyukanka ga tsara ta gaba, * tana ba da labarin bajintarka.

        Ya Mai Martaba, za su yi magana a kan ]aukakarka, * ni kuwa zan wallafa wa}o}in al’ajibanka.

        Ya Mai {arfi, za su furta ayyukanka masu bantsoro, * ni kuwa zan lissafci mu’ujjizanka.

        Za su furta jumlar alheranka, ya Rabbi, * suna raira yabon adalcinka.

            Yahweh Arahamani Arahimi ne, * mai jinkirin hushi, mai yalwar alheri.

            Yahweh mai alherin ne ga kowa, * rahamominsa suna kan dukan ayyukansa.

                 Yahweh, dukan ayyukanka za su yabe ka,* masu bautarka kuma za su yi maka godiya.

                 Za su yi shela ta ]aukakar mulkinka, * suna maganar ikonka.

                 Suna sanar wa ’yan adan jarumtakarka, * da ]aukaka ta girman mulkinka.

                 Mulkinka madauwammin mulki ne, * sarautarka ta dukan zamanai ce.

            Yahweh amintacce ne a cikin maganarsa, * mai alheri ne kuma a cikin dukan ayyukansa.

            Yahweh yana tallafar dukan masu fâ]uwa, * yana ]aga dukan wa]anda suka sunkuya.

        Kowa da kowa ya zura maka ido, * domin kana ba su abincinsu a kan kari.

        Kana bu]e hannunka, * ka }osad da kowane mai rai da alherinka.

        Yahweh mai adalci ne a dukan hanyoyinsa, * mai }auna ne kuma a dukan ayyukansa.

    Yahweh na kusa da dukan masu nemansa, * masu nemansa da gaskiya.

    Yana biyan bukatun masu tsoronsa, * ta jin kukansu yana cetonsu.

    Yahweh na kiyaye dukan masu }aunarsa, * amma zai hallaka dukan miyagu.

Bakina zai furta yabon Yahweh, * duk nama da jini zai yabi sunansa mai tsarki, * har abada abadin.

Zabura ta 146

Halelu-Yah!

Raina, ka yabi Yahweh! * Bari in yabi Yahweh muddin ina raye, * in yi wa Allahna wa}a lokacin da nike rayuwa.

    Kada ku dogara ga mahukunta, * ga ]an adan da baya iya yin ceto.

    Da lumfashinsa ya fita, sai ya koma tur~ayarsa, * a ranan nan shirye-shiryensa sun }are.

            Albarka ga wanda Allahn Yakubu shi ne taimakonsa, * da ke sa zuciya ga Ma]aukakin Yahweh Allahnsa,

                 wanda ya yi sammai da }assai, * teku da duk abin da ke cikinsu,

                 wanda ke yin aminci ga zaluntattu, * da kâre hakkin cutattu, * yana ba da abinci ga mayunwata.

            Yahweh yana ’yantad da ]aurarru, * Yahweh yana bu]e idanun makafi, * Yahweh yana mi}ad da karkatattu.

    Yahweh yana }aunar masu adalci, * Yahweh yana kare ba}i.

    Yana }arfafa marayu da gwauraye, * amma yana }arya ikon miyagu.

Yahweh zai yi mulki har abada, * Allahnki, ya Sihiyona, sarkin dukan zamanu ne.

Halelu-Yah!



Zabura ta 147:1-11

Halelu-Yah!

Wa}ar yabon Allahnmu tana da kyau, * muna jin da]in yabon Ma]aukaki.

Yahweh ne mai sake ginin Birnin {udus, * yana tattara korarrun Isra’ila.

    Yakan warkad da masu karayayyar zuciya, * yana ]aure masu raunukansu.

        Yakan ba kowane tauraro lamba, * yana ra]a wa kowanensu suna.

            Ubangijinmu mai girma ne da mafificin iko, * babu mai iya kwatanta gwanintarsa.

                 Yahweh yakan tallafa wa masu tawali’u, * yana }as}anta miyagu har {al}ashin {asa.

            Ku yi wa}ar godiya ga Yahweh, * ku }ada garaya ga Allahnmu.

        Yana rufe sama da gizagizai, * yana yin ruwan sama don }asa, * yana sa ciyawa ta tsira a kan duwatsu.

    Yana ba shanu abincinsu, * da abin da hankaki za su kwasa.

Baya jin da]in }arfin dawaki, * kaurin cinyar mutun baya burge shi.

Amma Yahweh na jin da]in masu tsoronsa, * da masu dogara ga }arfinsa.

Zabura ta 147:12-20

Ka yabi Yahweh, ya Birnin {udus, * ki yabi Allahnki, ya Sihiyona!

Domin ya }arfafa dogaran }ofofinki, * ya sa wa ’ya’yanki albarka a cikinki.

Yana wanzad da salama har iyakokinki, * yana wadata ki da alkama mafi kyau.

    Yana aiko da kalmarsa duniya, * aradunsa tana tafiya da gaggawa zuwa duwatsu.

    Yana barba]a dusar }an}ara kamar ulu, * yana watsa jaura kamar toka.

    Yana zubo }an}ararsa kamar gari. * Wa zai jure wa tsananin sanyinsa?

    Yana aika maganarsa ta narkad da su, * yana sa iskarsa ta hura sai ruwa ya yi gudu.

Yana bayyana sa}onsa ga Yakubu, * ka’idodinsa da hukuntansa ga Isra’ila.

Bai yi na’am haka da sauran al’ummai ba, * bai ta~a koya masu hukuntansa ba.

Halelu-Yah!


Zabura ta 148

Halelu-Yah!

Ku yabi Yahweh daga sammai, * ku yabe shi daga can bisa!

    Ka yabe shi, dukan mala’ikunsa, * ku yabe shi, dukan maya}ansa!

        Ku yabe shi, rana da wata, * ku yabe shi, dukan taurarin asubar fari!

            Ku yabe shi, sammai mafi tsayi, * da ruwayen da ke bisa sammai!

        Bari su yabi sunan Yahweh, * shi ne ya umurta, aka halicce su.

    Ya kafa su tuntuni har abada, * ya ba da ka’idar da ba za ta shu]e ba.

Ku yabi Yahweh daga {al}ashin {asa, * ku dodannin ruwa da dukan zurfafa!

    Wal}iya da }an}ara, dusar }an}ara da haya}i, * iskar hadarin da ke bin maganarsa,

        duwatsu da dukan tuddai, * itatuwa masu ’ya’ya da na al’ul duka,

            naman daji da dukan bisashe, * masu rarrafe da tsuntsaye masu fukafukai,

        sarakunan duniya da dukan al’ummai, * shugabanni da dukan kabilan duniya,

    samari da ’yan mata, * tsaffi da yara,

bari su yabi sunan Yahweh, * domin sunansa ka]ai ne mai ]aukaka.

Ko da yake ]aukakarsa tana gaban sama da }asa, * ya ]aga }ahon jama’arsa.

Bari dukan masu bautarsa su yabe shi, * musamman ’ya’yan Isra’ila, ’yan gaban goshinsa.



Zabura ta 149

Halelu-Yah!

Ku raira sabuwar wa}a ga Yahweh, * ku yabe shi a taron masu bautarsa.

    Bari Isra’ila ya yi murna da Mahallicinsa, * ’ya’yan Sihiyona su yi farinciki da Sarkinsu.

Su yabi sunansa da rawa, * su yabe shi da ganga da garaya.

    Domin Yahweh yana jin da]in jama’arsa, * yana na]a rawanin nasara ga gajiyayyu.

                 Bari masu bauta masa su yi murna da Ma]aukaki, * su yi farinciki da shi lokacin kwanciyarsu.

    Bari su ]aukaka Allah da ma}ogwaronsu, * suna ri}e takubba masu kaifi a hannwansu,

don su zartad da ramuwa a kan al’ummai, * da sakayya a kan kabilu,

    don su ]aure sarakunansu da sar}o}i, * shugabanninsu da mari,

don su aikata rubutaccen hukunci. * Wannan ce shaidar yabo ga dukan masu bauta masa!

Halelu-Yah!



Zabura ta 150

Halelu-Yah!

Ku yabi Allah a tsattsarkan wurinsa, * ku yabe shi a mafakarsa ta sama!

    Ku yabe shi don ikonsa, * ku yabe shi yadda ya dace da girmansa!

        Ku yabe shi da busar kakaki, * ku yabe shi da garaya da molo!

        Ku yabe shi da tambari game da rawa, * ku yabe shi da tsarkiya da sarewa!

    Ku yabe shi da kuge mai }ara, * ku yabe shi da kuge mai amo!

Bari duk mai lumfashi * ya yabi Yahweh!

Halelu-Yah!